BYE-BYE

16 1 2
                                    

AL'ADARMU
Page 42
Mallakin Diela

Happy Diwali
Festival/ Biki
October-November

Diwali bikin addinin Hindu ne da a keyi da hasken wuta,cikin watan october zuwa november,Biki ne da ya kasance Al'ada ga kabilar Hindu wanda suke yin shi a kowacce shekara. Kowa ya sani Kabilar Hindu sune masu bautawa gumaka da kuma shanu...akwai wasu daga cikin india masu bautawa rana, da sauran su, akwai Kabilar Christain, Akwai kuma Musulmai da sauran su, amma Christain da Musulmai bai zama dole suyi bikin Diwali ba.

Na jima a tsaye saman benen ɗakin da muke ni da yaya Ayman ina kare ma Hindu kallo, suna murna suna biki sosai, kasancewar yau ɗin ranar farin ciki ce agare su....na daɗe a cikin rayuwata ina son indiya amma ban taɓa tunanin taka kafa ta nazo kasar ba, sai yanzu da jinya ya kawo ni.

Ranar ne kuma naji mummunan labari daga Nigeria wanda ya sani zazzabi sosai, ina kwance saman gadon ɗakin hotel ɗin, lulluɓe da wani lallausan bargo, Yaya Ayman na matsa min yatsun hannaye na, na runtse idanuwa na, guntayen hawaye suka fito, ina tuna yadda na ɗau cikin ina kokarin ganin na kula da ita yadda Allah ya bani iko........Ayman ya rufe min baki da hannayen sa yana cewa,"Shisshhhhh Anam, kar ki butulce ma Allah da ya bamu kyauta kuma ya karɓi a bin sa, zan so mu zama masu godiya a gare sa, shi ya bamu kuma ya karɓa, haka zalika zai bamu wani In Sha Allah"

Murmushi nayi na kwanta a faffaɗan kirjin sa ina sheshshekar kuka har bacci ya ɗauke ni.

Abhi ya gama wasu ayyukan da yake yi, ana neman sa a ƙasar Turkey, sai ya tafi da Mummy Khausar, dream ɗin ta saboda tana son ta saro kayan turkey, mu kuma aka bar mu a Mumbai don hankali na ya kwanta.

Watan mu biyu naje Turkish Armed Force saboda suna bukaatar ganin mu, a wannan babban taro aka karamin matsayin da har yau nake alfahari da kai na, na koma tsohon aiki na wato Culinary Art.

ANKARA

Birnin ƙasar turkiyyah, nan aka dawo dani daga wajan aiki na.

Duba da yanda nake kokarin yin aiki tukuru kafin na san cewa nayi aure sai ya kasance dana yi aure kuma sai na zama weak, because matan soja basu cika aure a yankin syria, turkey, russia, iraq, lebanon dama wasu sauran kasashen ba.

Sai aka canja min location i was posted to Ankara-Turkey, and my husband open a big restaurant for me to start a business, main while colleagues ɗina suna kawo ma resto ɗina ziyara sosai....Ammi ta turo min Riya kasancewar zata auri wani ɗan ƙasar turkiyyah saboda mu sai suka dawo Ankara itama, amma sai ta zaɓi da ta rinka zuwa tana taimakamun a restaurants ɗina gidan ta baya da nisa da namu haka resto ɗin ma.

Fannin aiki na ma bani da matsala saboda ina ɓangaren masu yima sojoji girki idan za a je mission although ba kowani mission nake zuwa ba.

All this while am pregnant, 7month to 8month, Ayman ya san da ina da ciki, amma wajan aikin sa sunki barin sa yazo turkiyya ya ganni, duk da dama ni kaɗai ce Ammi da Umma sun karɓe min Boys ɗina, ni kuma nace da yardar Allah sai na sake haifan wasu Boys ɗin tun da sun kwace min waɗan cen.

Ayman baya da magana sai waya, Anam idan kin shiga watan haihuwa ki sanar dani fa na dawo, kafin ki haihu....ina dariya na ce to.

Ina shiga watan haihuwa na Commander ya bani maternity leave,

*Turkey Stylish Foods* shine sunan resto ɗina, Kasancewar muna samun costumers sosai sai riya take kula mun dashi, na ɗauki sabbin ma'aikata waɗanda suke abincin garuruwa huɗu, Turkey, China, Italy+ Nigeria don ba zamu yarda Al'adun mu ba, kuma akwai ƴan Nigeria dasuke zuwa business kasacewar ina abincin da suke so, sai nake samun costumers sosai.

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now