16

12 4 10
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 16

©Fadila Ibrahim

Ya tayar da Momma tsaye ya mata murmushi, yace ,"Mom na yar da zan yi converting in koma islam, but with one condition kar ki sanar da kowa, idan munyi aure da Anam zan ɗauke ta gaba daya daga Nigeria, za mu koma *Los Angeles* a cen zamuyi rayuwar mu, kema kuma zaki iya biyo mu daga baya"

"Deen are you all right? Momma ta faɗa tana shafa wuyan sa da forehead ɗin sa, tana daɗa tambayar sa anya lafiyan sa kalau kuwa......yana nufin kenan ba shiga islam ɗin zai yi ba.

Murmushi ya sakar mata saboda gano plan ɗin sa da tayi da sauri haka,...Ya ce,"You heard me right Mom" and it's a plan, no one will know about it except me and you promise"

Momma tsabar mamakin hali da rikon addini irin na Deen da mahaifin sa yasa ta kasa magana ma balle ta motsa daga in da take,tsabar son addinin mijin ta ya janyo mata ta fita daga islam ta koma addinin yahudawa ko ahlulkitabi ko christain........Momma daga baya ta gane abin da tayi ba daidai bane shiyasa ta dawo cikin islam religious.

*Toh wai nace Readers bari nayi wani ɗan tsokaci mai anfani.*

*Rayuwar da Christain suke yi mubar hantarar su da kyarar su, wasu daga cikin su za kuga suna matukar son hausawan mu, sannan wasu daga cikin su ma suna da kyawawan halaye, sannan abu mafi kyau a wajan su shine kyauta da kuma zama da mutum tsakani da Allah batareda sun cutar da mutum ba ko sunyi gulman mutum*

*Christain suna kin Musulman mu ne saboda wata gaba da aka kafa tun lokacin jahiliya period, sannan a zamanin mu na yanzu suna kin musulmai ne ta hanyar nuna musu kyara da muke yi, muna aibantasu, kuma muna tozartasu, Mu sai muce baza muyi tarayyah da christain ba saboda basu da tsarki, ko kuma suna cin dabba wacce ta haramta musulmai su ci, ko kuma abincin su bai da tsarki.*

*Abu na gaba, Suma akwai ɗabi'un da sukeyi wanda ba al'adar mu bace ta Bahaushe, amma kuma suna shiga cikin mu, suna matukar cin abincin hausawa, da sauran yarikan addinin musulunci, Allah kuma ya ɗaura musu son tarayyah da musulmai, daga ciki wasu suna tarayyah damu tsakani da Allah, wasu kuma sunayi ne don samun wani biyan bukata nasu.*

"Bana manta wani lokaci da muna yara, muna da neighbour Christian, Mutumin da Matar were so rest in peace now, a lokacin yaran su sa'annin mu ne suna shigowa gidan mu muna wasa dasu sosai, zasu ci abincin mu, amma idan muka je gidan su bama cin abincin su, kuma har ga Allah daga gida ba'a hanamu ba, zamuyi wasa sosai a gidan su amma bama cin komai nasu hakan na da nasaba da koyarwar da aka mana a islamiyya....sai wata rana yaran suka faɗawa iyayen su cewa bama cin abincin su amma su suna cin namu.....Maman su ta kulle mu a gida wata rana da wasa da dariya tace mu zauna muci abinci, me yasa bama son cin abincin su, to idan baza mu rinka cin abincin su ba, suma idan sun shigo baza suci namu ba.....To a wannan lokacin na fahimci cewa nuna musu kyara da tsarkake kanka daga abincin su hakan zai janyo musu tsanar musulmai ma gaba ɗaya, kuma suji baza su iya tarayyah da musulmai hausawa ba.

Wani abin daga Halayyah ce take zama Al'ada.

*Nasa ni wannan karatun na yakin musulmai da yahidawa ba zan iya ba saboda tarihi ne mai zaman kanshi ko acikin Alqur'ani, ba tun yanzu aka soma hakan ba kuma ba yanzu ake faɗa tsakanin musulmai da Christians ba, amma zan so in ɗan fahimtar daku ta hanya mai sauki wanda ko wani addini bazai ce na aibanta sa ba.   Ni nayi novel ɗina ne ba dan na aibanta ko wani addini ba, nayi shine don nishaɗi*

Al'adar Gidan Daura sun ara sun yafa, kuma bata dace dasu ba, ko kuna ganin ta dace dasu?

Ku amsa min ta Comment section Don Allah.

Na gode masoyana.

**************

Da kyar Momm ta iya buɗa baki tace,"Sharafaddeen why all this, ni ina son kayi aure ne hankalin ka ya kwanta nawa ma ya kwanta, bana so kayi aure ka gudu da matar daka aura, nafi son kayi aure ka zauna da ita anan tare da ni gaba ɗaya,x har ku haifa min jika Deen"

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now