29

17 2 4
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 29
©FADILA IBRAHIM

Kamar yaji takun tafiyar ta da sauri ya juya hanyar shiga sashen Abhi, ya hango ta tsaye ta sauya shiga cikin normal abaya as usual, car keys ne a hannun ta, da alama fita zata yi....da sauri ya tashi ya nufi wajan ta, yama manta da cewa Khausar na wajan, ya sha gaban Anam a dai dai lokacin da take kokarin buɗe mota.

"Yaya Ayman" na faɗa a hankali da sanyin jiki, saboda na sani Khausar na kallon mu, kuma bana son tayi zargin wani abu bayan ƴan uwan takan dake tsakanin mu".......Ko a jikin sa, ya karɓi makullan ya ce,"Anam ki taimaka ki bani wannan daman na yau kawai na zama driver ɗin ki, zan tuka ki nayi yawo dake a faɗin garin Daura, duk in da kike so, na miki alkawarin zanyi tukin da har abada babu kamar sa"....Murmushi nayi, kalaman sa sun saka na manta da kalubalen Khausar hakan yasa na bishi har motar sa kamar rakumi da akala.

Bamu tsaya ko ina ba sai daidai gidan tarihin rijiyar kusugu wato

KUSUGU WELL

Cikakken sunan shi shine Abu Yazid, Ɗa ne ga sarkin Baghdad. *Bayajidda* Jarumi lamba ɗaya daya wanda yayi jarumtar kashe macijiya a wancen lokacin daya shuɗe.
A wancen lokacin da suka shuɗe akwai rijiya mai suna Kusugu, cikin rijiyar wata maciya ce wacce take hana mutanen garin Daura ɗiban ruwa face ranar Juma'a...idan ka kuskure a ranar juma'a ba to kisa ne har lahira zai biyo baya.

Na gyara zama na ina kara kwankwaɗar ruwa mai garɗi wanda ya fito daga rijiyar kusugu, na kalli Yaya Ayman na kalli tsohon dayake bamu labari Na ce," To ya akai Bayajidda yaje rijiyar ɗeban ruwa, bayan macijiyar ta hana"

Tsohon yayi murmushi ya cigaba da cewa,"A wannan zamani da ya shuɗe mace ce take sarautar ƙasar Daura, mai suna Daurama., Bayajidda ya kasance matafiyi ne kuma tafiya ta kawo shi ƙasar Daura, ya sauka a gidan wata tsohuwa mai suna Ayyana, a Daren Alhamis da Bayajida ya shigo Daura ya shigo a gajiye da yunwa da kishin ruwa, sai dai Ayyana ta tarɓe sa da abinci ya ci ya koshi, yayin da ya gama ya nemi ta bashi ruwa sai tace bata da ruwan da zata bashi saboda ta labarta masa yadda suke shan wahala wajan ɗiban ruwa da kuma macijiyar da take kashe mutane idan suka je ɗiban ruwa ba ranar Juma'a ba.

Bayajidda ya kafe akan yana jin kishi, babu irin magiyar da Ayyana batayi ba akan kar ya kuskura yaje saboda ajaline ke kiran sa, amma ya kama hanyar sa ya tafi ya jefa guga cikin rijiyar ta kusugu, yana jefawa ya ji an rike, yayi magana mutun ko aljan amma shiru, ya hau janyo guga da kyar, anan ya lura ashe macijiyar ta kanannaɗe a jikin gugar macijiyar ta fasa kai tana shirin kai masa hari, ya zaro takobin wukar sa mai kaifi ya sare mata kai ya raba jikin ta sannan ya debi ruwa ya sha ma'ishi ya wanke jikinsa ya kuma ɗeba wa tsohuwar nan ruwa a langar ta ya tafin mata da shi....a daidai wannan lokacin Bayajidda ya bar warin takalmin sa kafa guda.....

Tsohon ya tsagaita dalilin kwarewar da nayi, sosai na kware Ayman yana bubbuga min baya na a hankali, ina ta kwalkwalal ruwa, yana cigaba da cewa "Sannu Anam" Ki bar shan ruwan hakanan, kin samu ruwa sai kwalkwalar ruwan kike ba dole ki ƙware ba"

Na ɗan harare sa kamar da wasa, na ce "Eh ɗin na sha kuma ma na kara sha ɗin" na sha sannan na ajiye ƙaramar langar ruwan, yayin da tsohon yake ta mana dariya ya ce,"Ku ɗin ma'aurata ne ko, na hango tsantsar qauna a idanuwan junan ku"

Muka haɗa idanu muna murmushi, na ɗan kwanta a gefen hannun sa na dama, ina cewa,"Kakaka cigaban mana da labarin mana"

Tsohon ya ce,"Da haka Daurama da Bayajidda suka fara...kamar ku ɗinnan.....Wayewar garin kowa ya san labarin abin da ya wakana, yayin da ake ta tururuwar zuwa rijiyar kusugu don bawa idanu abinci.....labari ya isa ga masarautar Daura zuwa Daurama ta kasa yadda har sai da tazo da kanta taga abin da ya faru, ta bada umarnin a nemo mata wanda yayi jarumtar domin ta bashi tukwici mai tsoka, Ganin Jarumin bai zo ba, sai Daurama ta sanya aka kawo mata warin takalmin daya bari....Samari, Matasa da dama sun gurfana a faɗar Daurama don gwada wannan takalmi sai dai babu wanda yamai.....Cikin ikon Allah kuwa tsohuwar nan ta ji abin da ke faruwa, hakan ya kara tabbatar mata da cewa bakon tane jarumin daya kashe wannan macijiya...sai ta nufi gida ta sanar da shi abin da ke faruwa hakan ya sa ya isa har faɗar Sarauniya Daurama ya faɗa cewa Shi ya kashe macijiya.....Sarauniya Daurama ta nemi da ya nuna sheda, nan take ya fito da kan macijiyar ya nuna, kuma aka miko masa takalmi ya gwada cikin ikon Allah ya masa....Sarauniya ta cika alkawarin bashi kyautuka da kyautar rabin garin Daura, daga baya kuma ta amince ta aure sa...Shine aa aka samu albarkar aure aka samu Hausa bakwai da Banza bakwai daka ɓangaren ƴaƴan su.......Har yau dai bayajidda ana bada tarihin sane a matsayin jarumin daya zo daga wata ƙasa ya nuna jarumta...amma ba shi da alaka da Hausawa saboda asalin sunan sa ABU ZAID, rashin jin hausan yasanya aka sanya masa Ba-ya-ji-da.

"To kunji takaitaccen tarihi akan wannan rijiya ta kusugu.wanda ta zama gidan tarihin da har gobe ana zuwa gari i gari ana ganin rjiyar"

Tuni nayi bacci a hannun damar Yaya Ayman, tsohon ya ce,"Bata da wiyar bacci Allah sarki, to zaku iya tafiya"... Ayman ya gyaɗa kai yana sake duba agogo karfe huɗu ne daidai ya samo gashin kaza dogo ya tsokala mata cikin hanci... a firgice Anam ta farka tana waige waige kawai sai Ayman ya kama dariya yana rufe baki, Anam ta ce,"Haba Yaya Ayman, tsokana fa"

"Ya ce,"Sorry Anam, yadda ya faɗi kalmar sai ya bata dariya ta shi tayi tana cewa, "Ya kamata mu koma gida kada Ammi tayi ta nema na"...."As you said my queen" ya faɗa yana rissinawa, ya sake ɗagowa ya ce,"Da fatan dai gobe Gimbiyar zata amince mu sake fita gobe kamar dai irin na yau?

Suna hanyar tafiya Anam kam murmushi take yi tsabar murna ta kasa cewa komai, farin cikin kasancewa tare da Ayman, ina ma ace shine zai mijin ta....Ta ce,"Yaya Ayman wai kai baka da budurwa ne?

Ayman yana tuki ya ce,"Ina da ita mana", "Khausar???? na wurgo masa tamabayar a lokacin da bayyi tsammani ba kuma daidai lokacin da muka kawo kofar gidan namu, sai ga Khausar ɗin ta fito ina ga da alama zasu koma gida kenan sun gama yinin na su.....Khausar ta tsaya cak tana kare mana kallo ba tare da ta ce komai ba ta bi bayan Inna Mune suka tafi...kamar an cire wata jijiya a jiki na haka na fito daga cikin motar ina jin sa yana min magana amma na kasa amsa masa, saboda ban fahimci mood ɗin Khausar ba, kallon da ta min ya sanya ni cikin wani yanayi....Anam dai bata da tsoro amma na rasa dalilin daya sa nake ɓoye wa khausar alaqa ta da Ayman....ko dan ita ma shine zabin ta?

©FADILA IBRAHIM

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now