20

13 3 2
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 20

©Fadila Ibrahim

DAURA TA ABDU TUSHEN HAUSA

Duk da tsananin rana da ya mamaye sararin samaniya, amma sanyi ne ke ɗawainiya a jikin ko wanni ɗan adam da yake garin daura, baka iya jin zafin ranar saboda masu hasashe sun hasaso mana cewa za'ayi ruwan sama a garin Daura.

Bayan sa'i guda hadari ya mamaye garin alamar ruwa ya bayyana garin yayi duhu tsabar hadarin daya mamaye ko'ina ya kuma ɓoye rana, ya taho da wata walkiya mai zafi, a daidai wannan lokacin su Abhi suka shigo garin Daura, suna shigowa ana tsugewa da ruwan sama mai sauka kamar da bakin ƙwarya...wanda yasa su parker wa don ya tsagaita.

Har wannan lokacin zuciyar Umma bata dena bugu ɗaya biyu ba, suna cikin motar tsahon dakika talatin Abhi yace "Ruwan ya tsaya bari na ɗan siyo ruwa a wancen shagon na kusa da police station ɗinnan, ƙishin ruwa nake ji"

Umma ta gyaɗa kai ita ma ta fito ta tsaya don kare ma cibiyar ta kallo tayi kewar garin kamar ba'ayi ba shekaru Arba'in da ɗori ai ba wasa bane.

********

Tun da muka isa police station suka wurga ni cikin cel, nama kasa yin kuka domin zuciyar tawa ta dishe, kallon Ammi kawai na keyi don a daburce take, tama kasa cewa uffan kallo ɗaya za kayi mata ka hango tsantsar ramar daya bayyana a fuskar ta na sa'i guda,
tsahon awa uku muna abu ɗaya, Ammi ta ce,"Ruwan ya tsagai ta, Anam na son Ruwan sha bari na siyo mata a waje"

Ta isa bakin shagon kafin ta shiga ne, wani yazo ya wuce ta, kamshin turaren Abhi taji ya fito daga jikin mutum yayin da take wucewa, Zuciyar raya mata wani abu, t bayan, yanayin saka kayan keyar sa, kwantaccen suman sa kamar na buzaye, hannun sa, yanayin tafiyar sa....sai kawai ta tsinci kanta da bin sa har in da motar shi yake....amma to her own surprise sai ta ga yana mika ma wata mace ruwa cike da murmushi da nuna kulawa, ta kagu da taga fuskar bawana Allah nan mai kamannin minin ta.

Wallahi kamar ance ya juya, nan ta ganshi ɓaro ɓaro, Dr SM Daurawa, ABHI ɗina dama yana raye ne??? amma me yake yi da wata macce....kenan dama yana cikin garin Daura yana cin amanar mu bamu sani ba......Uhm Uhm Abhi bazai mana haka ba, nayi wauta dana bari shedan yake son yaci galaba akai na ba.......To amma tana tsaye har suka koma cikin mota sun jima kafin aka tada motar suka wuce fau.

Kamar wacce aka zare ma jijiyoyi haka Ammi ta dawo cikin station, kanta na niyar fashewa saboda abubuwa sunyi mata yawa, ta gaza gane me ke shirin faruwa da su ne, Ga Anam ɗin ta yau a police station, ga kuɓa Abhi ɗinta tare da wata mace a cikin garin Daura....ta share wasu hawayen da suka sauka daga idanuwan ta kafin su karasa kumatu...ta mika min ruwan gora tana kakalo murmushi.

*************

Da misalin karfe biyu da wani abu, motocin suka kunno kai zuwa gidan DAURA kai tsaye ainahin gidan su ya ce su wuce, saboda Dama Baban shi ya fisu saukin kai duk a cikin su.

Ganin yadda gidan yanda yake tsit alamar babu kowa, masu gadi suka kawo gaisuwa, suna murnar sake ganin Abhi, tuni masu aikin gidan suka ruga aguje sukayo kiran Inna Mune....Ta fito a saba'in tana cewa,"Ɗa na, da gaske kuke wai" har tana cin tuntuɓe wallahi ta je ta rungume shi tsam tana kukan farin cikin sake ganin Sulaimanun ta.

Sulaiman kai da su waye haka, Abhi ya waiwaya yana cewa,"Ku fito mana"
Suka fito, Yayin da Inna tayi tozali da Asma'u dama Asma'u ƴar ɗakin Inna ce, Inna ta wara hannayen ta tace,"Yaki uktee na"

Asma'u ta ruga a guje ta rungume Inna Mune tana kukan rabuwa....daga bisani suka shiga daga ciki, nan da nan estate ya ɗauka gaba ɗaya cewa ABHI YA DAWO, TARE DA AUNTY ASMA'U.

Duk dama wasu jikokin basu san ta ba, amma haka ake ta tururuwar zuwa ganin ta, yayin da labari ya shiga kunnan HURAIRA DA BABANGIDA sai akalar alkalamin ta canja......kiran Kakana su kayi akan duk abin da yakeyi ya bari yazo gida.

Duk yanda Kakana yaso akan su bashi beli na zuwa gobe mu dawo amma sun ki yadda, da alama biyansu akayi akan case ɗin, Kakana ya zo daf in da nake ya kama hannaye na yace ,"Anam ba son mu ba, kuma In Sha Allah zan dawo anjima don baza mu barki ke kaɗai anan ba....Ana kirana urgently zan tafi gida.

Babu bakin magana, iyaka ta gyaɗa kai kawai na keyi ina yi musu bye bye, ni nasan halin tsaka mai wuyar dana shiga,ina ganin yadda suka fece suka barni a cel.
Ammi na zaune ita ɗaya don ya ce ita ta zauna kafin yaje ya dawo, ganin tayi shiru sai ta bani tausayi, Ammi bata son tashin hankali yanzu zata rame....shiyasa na jima ina faɗa mata mubar garin nan, zasuyi ta amfani damu ne babu gaira babu dalili...magana nake a zuciya ta amma hankali na yana hanyar waje, tun kafin ya karaso zuciyata ta hango min shi yana shigowa.

Magana yayi da kananan polisawan wajan, kai tsaye suka nuna masa offishin DPO din su.

Ko kallon in da nake ma bai yi ba, tafiyar sa tamkar zaki......Aiman kenan.

*************

Kasancewar duk wani meeting ɗin da za'ayi a falon Babangida ake haɗuwa ayi, kamar ko da yaushe yau ma hakan ne ta kasance.

Abhi na zaune gefe guda shi da su Riya da Umma Asma'u da Inna....da kuma sauran dangi har dasu Mummy khausar, gida fa tuni ya cika dama ga matsalar da Anam ta faɗa suna bukatar meeting.

Abhi ya ga shigowar Baban Sulaiman, wato Kakana...Baban Sulaiman yaji shauki saboda idanuwan sa sun hango masa ɗan sa ɗaya tilo, amma halin nan na sarauta yana nan a jinin jikin sa , hakan ya taimaka masa ya dawo da miskilancin da babu wanda ya ɗauko wannan halin sai Anam duk cikin zuri'ar gidan Ɗaura. Bai hana Abhi tashi ya rungume mahaifin nasa ba cike da shauki da begen juna Kakana ya bubbuga masa baya sannan ya sake shi ya nemi gu ya zauna.

Fuskar Baban Sulaiman babu dariya balle nuna halin ko in kula kai tsaye kujerar daya saba zama ita ta nufa ya hau ya zauna sannan yayi gyaran murya haɗe da buɗe taro da addu'a cikin harshen larabci da karatun Alkur'ani.

Daga bisani Baban cikin gida Baban kowa mai zafin rai wato Kawu bishir ya chaɓe...."Kafin nace wani abu, mun gode wa Allah da ka dawo gare mu da ranka da kuma lafiyar ka"

Hakika a baya munyi tawassali, mun kuma hakura da kai alokacin da aka shaida mana cewa har da kai a cikin waɗan da aka kashe sai dai kuma kai ba a ga gawar ka ba, dalilin rashin ganin gawar taka sai Baban Sulaiman yace ba zai yi jana'izan ka ba har sai ya tabbatar da cewa baka raye....ƙwatsam muna cikin wannan yanayi kuma sai ga matar ka da ƴar ka sun riske mu.

Daga haka sai Babangida ya dakata, yana jiran ko Baban Sulaiman zai ce wani abu...sai Baban Sulaiman ya lumshe idanu alamar ya cigaba da magana kawai.

"Hakika abin ya zame mana almara, bamu san da zaman suba, amma kuma su sun san da zaman mu,Tabbas munji zafin abin da ka aikata, baka bamu hakkin mu a matsayinmu na iyayen ka ba, kaje kayi kan gaban ka" ya tsagai ta ya sha ruwa sannan ya cigaba da cewa,"Ko Asma'u da muka kore ta a gidan gaba ɗaya, ai sai da muka sauke mata hakkin mu daya rataya a kan mu sannan muka sallame ta"

"A wannan lokacin bamu isa mu yanke musu hukuncin yin nesa da mu ba, illah muka yanke hukuncin yin rayuwa da su na har abada, amma mun kayyade musu sharuɗɗan gidan Daura, Yayinda *Sa'adatul Anam* ta so bijire wa dokar mu in da Ammi ke kokarin hanata".....Gaskiya ba zan ɓoye maka ba girman nasara ƴar ka tayi, ɗabi'un ta da Al'adun ta sun banbanta da namu na arewan najeriya, hakan saɓa doka ce a gidan Daura, laifin ka da yawa Sulaiman.

Abhi yayi gyaran murya ya ce,"To da farko dai zan fara da baku hakuri tukunna, Babangida, Baba Huraira, Baba na, Zan so ku yafe min bijirewa dokar ku da nayi abaya, kuma na tsallake matan arewa, matan najeriya na tafi na auro ƴar ƙasar turkiyyah. yayi shiru na ƴan mintuna abin ya dawo masa sabo....Ya fara da bada labarin wacece Ammi asalin ta, sunan ta, kabilar ta da sauran su.

©FADILA IBRAHIM

AL'ADARMU ✔Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt