30

10 3 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 30
©FADILA IBRAHIM
DAURAWA ESTATE

Ayman yana tuki ya ce,"Ina da ita mana", "Khausar???? na wurgo masa tamabayar a lokacin da bai yi tsammani ba kuma daidai lokacin da muka kawo kofar gidan namu, sai ga Khausar ɗin ta fito ina ga da alama zasu koma gida kenan sun gama yinin na su.....Khausar ta tsaya cak tana kare mana kallo ba tare da ta ce komai ba ta bi bayan Inna Mune suka tafi...kamar an cire wata jijiya a jiki na haka na fito daga cikin motar ina jin sa yana min magana amma na kasa amsa masa, saboda ban fahimci mood ɗin Khausar ba, kallon da ta min ya sanya ni cikin wani yanayi....Anam dai bata da tsoro amma na rasa dalilin daya sa nake ɓoye wa khausar alaqa ta da Ayman....ko dan ita ma shine zabin ta?

Ina fita naji yana cewa,"Anam kiyi sallah, yanzu zan dawo zamuyi magana da ke"

Duk da na ji abin da yace, amma ban iya amsa masa ba nayi wuce wata ciki. Ayman na ajiye ni ya bar kofar gidan namu, kai tsaye gida ya koma ya gabatar da sallah, alokacin su Umma har sun koma gida...na shiga gida ban samu kowa ba har Abhi baya nan sun fita da Grandpa, Ammi kaɗai na samu da Riya suna hutawa a falon shakatawan Ammi.

Bayan nayi sallah nayi wanka na sauya kaya na fito falo na zo na zauna kusa da Ammi ina mata magiyar yunwa nake ji.

Ammi ta ce,"Akwai abinci a dinning" na tashi naje na duba, coololi ne guda uku, na zuba fried rice, da chips sai na ɗebi farfesun naman kaza, na dawo na zo na zauna, abincin dana ɗiba bazan iya cinyewa ba, hakan yasa Ammi ta zuba min idanu kallo na  kawai takeyi, jim kaɗan sallamar sa ita ta sanya duk muka waiwaya Ammi na amsawa, Ya tsugunna har kasa ya gaida Ammi ya sannan cike da kunya ya juya yabar falon ya fita.

Ammi duk tana kallo na, gashi kuma na kasa cin komai, tashi nayi na kirawo Riya na mata magana kus kus a kunne sannan na fita waje.....na same shi a balcony barandar shiga sashen Abhi zaune saman kujera na sunkuyar da kai na ƙasa har na karasa na samu kujera na zauna, shiru ya biyo baya.

"Anam ina so ki amince min, a tsaida maganar auran mu kafin su Umma su koma Zaria"

Na san cewa Ayman na da natsuwa fiye da duk wani saurayin dana sani a duniya amma natsuwar tashi ta yanzu ya fita daban da sauran ranakun da yake mu'amular sa....Hakika zuba masa idanuwa na nayi na kasa furta masa ko da kalma ɗaya tak.

"Anam ki yarje min saboda kece zabi na, ke nake so na aura ki zama uwar ƴaƴa na", ya ɗan sunkuyo saitin fuskata ya ce cikin siririyar murya,"Anam kice min wani abu mana"

"Kaci abinci Yaya" adaidai lokacin Riya take ajiye kwanonin kashi masu murfi ta jera su tsab akan karamin teburin dake tsakiyar mu, na kasa kallon fuskar shi bare kwayar idanun nasa, hakika ina jin nauyin Ayman kuma girman soyayyar shi ce tayi min yawa har nake kasa yin magana idan ina gefen sa...."Kice min wani abu Anam, ko ba kya so na ne?

Karar Horn ɗin motar Abhi ita ta dawo da ni daga trance ɗin dana shiga na zurfafa sosai cikin tunani, a hankali na nufi motar Abhi na buɗe masa murfin motar ina yi masa barka da shigowa, yayin da Ayman dake gefe na a tsaye ya sakarwa Abhi da wani murmushi mai kashe zuciya, na fahimci akwai wata shakuwa tsakanin Ayman da Abhi wanda Allah kaɗai ya haɗa ba mutum ba.

Hannayen Ayman na cikin na Abhi suna tafe a jere duk da cewa Abhi bai furta kalma ɗaya ba, gaisuwa ma gyaɗa mana kai yayi kai tsaye sai da muka raka shi falon shi sannan muka dawo wajan zaman mu......duk da mun koma amma hakan bai sa na furta masa sirrin zuciya ta, Yaya Ayman bai jima ba ya min sallama tare da yikinin washe gari zai dawo, in shirya faɗa masa koma miye ne.

******
7:00am

Kamar Almara cikin bacci naji muryar ta cike da kissa da tana kuka tana ambaton sunan Yaya Ayman....Ina kwance a dinning ɓangaren falon Abhi saboda anan ne muke ajiye littafai na islam na idar da karatun Alkur'ani shine bacci ya kwashe ni.

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now