19

7 2 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 19

©Fadila Ibrahim

**********

Tun karfe shida na safe motoci kirar vibe guda biyu suka tsaya a kofar gidan Umma.

Umma ta fito da karamin kit ɗin akwatin ta, don ita bata san yaya zai kasance ba da zuriar gidan Daura, ta sani ba lalle su amshe ta hannu biyu ba...shiyasa fa ɗibi kaya ƴan kaɗan...Tana jin Abhi yana magana da direbobin sa don motocin sa ne daga Abuja suka zo, Umma ta koma ɗakin Inna tana cigaba da magiya, "Inna wallahi da gaske tafiya zamuyi, ke kaɗai zamu ɓari a gidan wai"

Inna da take kwance ta dukunkune da  tsummokaran kayan ta, ta kura wa Umma ido tana nazarin abin da zata ce mata,"Asma'u yanzu tafiya zakiyi ki bar ni, Asma'u tsahon rayuwar ta na saba dake shine ɗan uwan ki yazo ya hure miki kunne zaki tafi ki barni Asma'u".....Kawai sai ta fashe ta kuka babu kakkautawa.

"Ya ilahi" Umma ta sauke ajiyar zuciya yayin da ta kasa cewa uffan, tuna badakalar da suke sha ne ita da Inna tun daren jiya data sanar da ita zasu je Daura.....ta tsugunna har ƙasa kusa da Inna ta ce,"Inna ina matukar son zama dake, bazan guje miki ba saboda ƴan uwa na, Inna na gama da miji na lafiya,  ina so iyaye na su yafe min laifin da na musu na bijire wa dokokin su, Inna ba wai nace zan tafi na bar ki bane, tare fa zamu je kuma mu dawo tare"..  Ki kwantar da hankalin ki In Sha Allah muna nan tare Inna" Umma ta faɗa tana mai riko hannayen Inna haɗe da washe baki tana magana amma kun san halin Inna ba ayi mata gwanin ta sai ta ture ta tana cewa,"Ni matsa dallah, sai wani shafa ni kike yi sai kace kin samu mijin ki Yusuf a kusa dake......Ni nuna min motar dama na shirya kayana zani ganin Aimanu na"

Haka Umma ta sake baki tana mamakin ƴar tsohuwar nan da gwale mutum, girgiza kai tayi tabi bayan Inna wacce tuni ta jima da fita tayi hanyar waje kai tsaye...ko data leka ta ta hango Inna tana faman kiciniyar buɗe kofa zata shiga mota....Abin ya bata dariya wanda da kyar suna ta shan drama da direba kafin ya buɗe mata ta shiga da tsalle tana cewa "Yeee hu huuuuuuu ai mun saba hawa lokacin marigayi yusuf ɗa ɗaya tilo yana ca mota ai shima, ga kyau ga AC"...HAHHHH ta kwashe da dariya abin da, direban yana ta taya ta da alama ya saba da irin su Inna shiyasa tazu tazo ɗaya.

8:30am

Karfe Takwas da rabi sun kama hanya, Abhi sun hau mota ɗaya da Umma Asma'u, Riya kuma suna mota ɗaya da Inna, suna ta shan drama....Duk abin da ta gani sai ta yi magana akai, na tsoro ta chakumo Riya, na dariya a kwakumeta ana nuna mata ana dariya...tun Riya na fahimta har ta sanya earpiece, ta sanya facemask ta fara baccin karya to shine ta samu salama.

DAURA TA ABDU TUSHEN HAUSA
Ƙasar BAYA-JI-DA

Zaune nake saman kujera na dukunkune jiki na, Sashin Deen in da na fara aiki a baya,Ɗakin babu abin da yake yi face warin giya da warin tabar sigari, Deen dai baya sha, da alama barasa ce abin kwalɓewar sa.

Karo na ba adadi na sake kallon su, ina takaicin ɓoyayyen hallaiyar sa wanda bakowa yake iya ganin hakan ba,  Suke ta sheke ayar su, kiɗa ne yake ta faman tashi a babban speakers ɗin dake falon yayin da karamin teburin dake gaban kujerun shakatawan falon cike yake da kwalabe da kofunan glass, yana sha suna sha.

Wa'iyya zu billah, a haka ake son aura min wanda AL'ADUN MU ba ɗaya ba, An samu banbancin ɗabi'u tare da banbancin AL'ADU....duk da cewa nayi tashin ƙasar waje amma tarbiyata da tashi ko kusa bata haɗu ba....Ina nan zaune muka ji karar knocking kofa, kamar yadda banyi tsammani ba, haka suma basuyi tsammanin ganin sa a daidai wannan lokacin ba duk da cewa dama zaman jiran sa suke yi idan yaki zuwa kuma zasu aika a ɗauko shi a duk in da yake.

Tafa hannuwa Deen ya keyi, yana kai kwalbar giyar sa, yana cewa,"Great! Great!!!!!!!!!I knew it, ashe dai ka cika sunan ka Aiman, abokai ku dube sa, wai ya zo ceton masoyiyar sa" Suka kwashe da dariya suna cewa,"come in side, zo ka ɗauke ta mana"

Idanuwa na sukayi tozali da nashi, take yanke zuciya ta da gangar jiki na suka amsa sunan Aiman, yayin da ruhi na ya haɗu da nashi ruhin, mikewa nayi ina cewa *Yaya Aiman*

Kiran sunan yayi daidai da harbawan harsashi wanda tuni Aiman ya janyo ni muka koma gefe a daidai wannan lokacin kuma Momma ta bankaɗo kofa kuma harsashin ya bi ta tafin hannun ta ya fasa mata tsoka da kashin hannun yana zubda jini....Momma tayi kara ta rike hannun tana zubar da hawaye masu zafi.

Deen yayi kukan kura, ya bige hannun abokin nasa, yana cewa "uban wa yasa ka kayi harbi, you see what you've course" shittt ya buga bayan teburin da kafar sa ya nufi wajan mahaifiyar tasa.

Aiman na ganin haka ya kamo hannu na, muka arce a guje, basu iya biyo mu ba saboda hankalin su a tashe yake sam, jiki na rawa yake yi har na kasa gane gabas da yamma, tunanin abin da zai biyo baya ne shine yake tamin yawo a cikin ƙwaƙwalwa ta.

Har kofar gida ya sauke ni ya wuce babu wanda yayi magana tsakanin mu, haka ma dana shiga gida ban iya cewa komai ba...Ammi da Khausar suna ta tambaya ta ina naje amma na kasa faɗa musu abin da ya faru....Hakanan nayi bacci dai rabi da rabi, ina firgita daga karshe na tashi na ɗauro alwala na kama sallar nafifili har gabanin asubahi.

Inda na idar da sallah nan na kishingida bacci mai nauyi yayi a wan gaba da ni, wanda ban tashi ba sai karfe goma na safe shima naji hayaniya yayi yawa ne, hakan ya sa na fita tsakar gida don jin abin da yayi kawo cecekuce har ake hayaniya.....Kakana na gani a main compound ɗin gidan, yana sa'insa da pan sanda suna cewa sai an tafi da ita, sunyi attempting kisa ne ita da saurayin ta saboda bata son Deen.

Kai na ne naji yayi min nauyi, gangar jiki na na rawa, yayin da idanuwa na suka sauka kan Ammi wacce take hawaye.....faɗi nake ina cewa,"Ammi kingani ko, Kinga abin da Najeriya ta janyo min ko"

"Ammi na sha faɗa miki ki taho mu koma ƙasar mu amma kin ki saurare na, naga abin da na hango shiyasa tun da fari ban so hakan ya kasance ba"..........."Ya isa haka shige mu tafi" Wata daga cikin police ɗin ta faɗa...ankwa suka sanya min kakana ya biyo bayan mu da motar sa tare da Ammi da khausar.

Tsananin damuwan dana shiga yasa bana ma iya kallon hanya, balle na ga mutanen dake gefe na, hakika na shiga halin tsaka mai wuya, shin wa ye zai iya ceto ni daga ifti'la'in daya sauka a gare ni.......Ɗaga kan da zanyi ne idanuwana suka sauka a kan Aiman, ya yi tsaye yana kallo na cike da mamakin abin da idanuwan sa suke hango masa.....na matse wasu zafafan hawaye ina tuna Abhi na da kuma irin rayuwar da mu kayi a Turkiyyah, babu tashin hankali ko kaɗan, sai ma soyayya da kulawa da kwanciyar hankali.

©Fadila Ibdahim






AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now