13

4 3 6
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 13

©Fadila Ibrahim

Na kama kai na, na bar wajan ina mai addu'an kar Allah ya amsa addu'a ta, na faɗi hakan ne saboda wallahi ina so mu bar Daura mubar komai, kawai mu koma ƙasar mu turkey....amma kuma ta kasa fahimtar in da na dosa, Ina wannan tunanin har na samu abin hawa na hau batareda nace mishi ga in da zani ba tsabagen tunani yamin yawa a kwakwalwa ta.

Munyi akalla tafiyar minti goma kafin mai napep ɗin ya waiwayo yace ,"Ranki shi daɗe ina zaki je ina ta tambaya?

Sai a lokacin na dawo daga zurfin tunanin dana faɗa, na ce,"Ohhh ya hakuri" , Cikin gurbatattiyar hausa ta wacce ban gama iya furta kalmomin ba na sake na ce," Tudun waa daa" mai napep ya yi ƴar karamar dariya dai dai lokacin da wani yake kokarin tsayar da shi a bakin hanya, muka tsaya.

Fuska ta tana kallon gefen hanya, yayin da tunanin zuciya ta ma ya banban ta da abin da ke kunshe a cikin fuskar tawa.....da sallama ya shigo ya zauna gefen dana zauna yana cewa,"Aboki na, ka kaini wani restaurants da ka san abincin su akwai daɗi please ni ba ɗan gari bane"

Mai a daidai ta ya ce,"An gama, ya kaɗa Napep ɗin muka yi gaba.... bamu tsaya ko ina ba sai daidai Eatery ɗina, na sauka na biya na shige yayin da gate man ɗin suke aikinsu  yadda ya kamata.......na shiga ba da jimawa ba ina ta duba abubuwan da ya wakana resto ɗin, sai naji ana min magana ta baya na.

Zazzakar muryar sai tayi min kama da muryar Abhi na hakan ya sa na juya da sauri ina kare wa mai muryar kallo......Kasancewar akwai wata kujera a kusa da shi hakan ya taimaka masa wajan dafa kujerar yana cewa,"Allahumma barik" ya faɗa a daidai lokacin da ya dafa kujerar zuciyar shi na cigaba da bugu sosai saboda tabbas idanuwan sa da gangar jikin sa sun tabbatar masa da cewa Anam ce.

Duk da kuwa ya sani bai taɓa ganin ta a zahiri ba sai a hoto, amma kuma yana da tabbacin ita ɗin ce ya gani a gaban sa yau saboda gangar jikin sa ta aminta da hakan, ya faɗa a cikin ran shi ya ce,"Lord so soon" ma'ana Allah da wuri haka, yau fa ya iso Daura, sai gashi Allah ya haɗa sa da ita......."Mallaam am talking to you" Yaji salon nata muryar tana yi masa magana jin shirun ya yi yawa.

Da kyar Aiman ya iya tattaro duk kan natsuwar sa, ya dawo da hankalin sa zuwa gangar jikin sa, ya kuma kara buɗe idanuwan nasa, yayin da ya ɗaure fuska babu yabo babu fallasaa, kadaran kadahan in ji hausawan Katsinawan mu.....Aiman ya ce,"Don Allah ki taimake ni da abinci ko da ba yawa, yunwa nake ji"

Ɗa ga kai nayi ina kallon sa, Nayi mamakin wani abu da naji ya tokare min zuciya ta kallon idanuwan sa da nayi shiya janyo min hakan, sai nayi blaming kai na, sannan na kama gaba na bayan na bada order cewa "a ba shi take away na fried rice da meat guda ɗaya" Sannan na wuce bench ɗina na zauna.... Na kwantar da kai na saman teburin da yake gaba na, rasa ya akayi na fara sa kai na cikin damuwa da tunani.....hakan na da nasaba da rashin Abhi a kusa da mune ko ko dai girma ne ya fara kama ni, Toh amma obstacles ɗin da muke shiga ya fara yawa........Knocking bench ɗin a kayi, Shin waye kuma zai takura min sai da nayi a kallah sakan uku kafin na ɗaga kai na,  na duba naga ko waye amma wayam babu kowa....sai wata paper da aka ajiye a saman bench ɗin an manne ta da kuɗin Turkey bandir biyu......mamaki ya sa na fita reception babu kowa, na fita waje shima dai wayam babu kowa.....ai ban ga ta zama ba na hau a daidaita na koma gida da sauri saboda na sanar wa Ammi amma sai na tarar da wata dramar da tafi ta kullun wai anzo neman aure na.

Tabbas ina kokarin shigowa gida naga motoci sun kai biyar manyan jeep, da wasu maza a balcony/ barandar shiga sashin Grandpa....da kuma manya manyan tsadaddun akwati na masu kyau....sai dai sanin cewa ba hurumina bane sai nayi sashin mu.

Ammi na zaune ita da Mummy Khausar, da Khausar ɗin suka ganni na shigo, Khausar ta rungume ni tana cewa "Nayi missing ɗin ki sister"

"Sister Khausar saukar yaushe kuma, shine baki kira ni kin faɗa mun ba da ban fita ba" Na tamabaya ina murmushin ganin ta.

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now