28

17 4 2
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 28
©FADILA IBRAHIM
DAURAWA ESTATE

Gaba ɗayan mu muna zaune a dinning muna breakfast,Abhi ya ce,"Anam wai yaushe zan aurar da ke ne, kin girma fa"

Dariya ya bani, wanda nayi ta loman Chips ina korawa da Banana shake, a daidai wannan lokacin sautin muryar sa da sallamar sa ta ziyarci kunne na, na yunkura zan tashi da na tuna hirar mu jiya da daddare yake cewa,"Idan ya zo zan faɗa masa ko ina son shi ko bana sonshi.....shine na tashi zan bar wajan kawai ya sha gaba na idanuwan sa suna kallon idanuwa na, ya hanani wucewa, yana magana da Daddy alokaci ɗaya, ya kuma gaishe da Ammi yana tsugunnawa cike da girmamawa.

Baya na koma taku biyu, na tsaya gefen Ammi, ganin su Umma da Inna sun shigo, sai kunyan su ta kama ni bayan na russuna har kasa na gaishe su, Umma har da shafa min baya ta mikar dani tana cewa "Kayya Anam, "Kwana biyu ban gan ki ba, fatan kina lafiya"

"Lafiya lau Umma, na amsa mata ina gaishe da Inna" Ammi ta mike suka nufi falo Abhi ya kama hannun Ayman suna murmushi suna magana kasa kasa, sai suka birge ni....Riya ta kawo musu abin sha da abin ci.

Sallamar khausar da Inna Mune da Grandpa ita ta sanya suka tsagaita da hirar da mukeyi....Khausar tana murmushi tazo ta tsaya a bayan kujera kusa da ni in da na tsaya, tana ce min,"Guess what?....Na ɗan zare idanu da mamaki ina cewa,"What???

"Am going to be a bride soon"...Har cikin zuciya ta ban ɗaga hankali na ba wannan karan, natsuwa nayi ina sauraran ta, na bata dukkan hankula na, ina cewa,"Really! it's a good news dear am happy for you"

Ta rungume ni tana rawan jiki, har da cewa ,"Thank you Sister".....na juya ina sauraran Grandpa bayan na gaishe shi.....Naji yana cewa,"Dawowan ka yayi matukar kwantar mana da hankali, hakika wasu matsalolin bamuyi tunanin zai lafa ba, kamar zuwa Deen sai bayan dawowan ka jiya ka dakatar dasu kaga yanzu mun samu salama, saboda mahaifiyar sa ta ɗauke shi ma sun bar ƙasar gaba ɗaya, da alama in ba haka akayi bazamu samu sa'ida ba.

Sai alokacin na fahimci ashe dalilin da ya sa jiya Ammi suka haɗu a gidan Grandpa kenan, bana mantawa ina hanyar shigowa ma na ga motocin gidan su Deen suna fita and he can't do anything nonsense shiyasa har yanzu yake bibiya ta ya kasa min komai,....dalili ashe Ayman ya faɗawa Abhi problem ɗin mu tun kwanakin baya daya dawo ashe har gida yaje ya kankara wa Momma warnning"

Sai a yanzu nake jin komai.....Na girgiza kai ina tausayin Deen, he is now a looser, wani murmushi ne ya ziyarci zuciya ta a daidai time ɗin muka haɗa idanu da ruhin zuciya ta sai ya kashe min ido ɗaya, kawar da kai na nayi.

Inna Mune ta karɓa da cewa,"Asma'u naji kuna cewa zaku koma Zaria, Dama ba kun dawo nan gaba ɗaya bane?

Umma ta karɓa da cewa,"Aa Inna Mune, dama mun zo ba da hakuri ne, amma ai zumunci ba zai ƙare ba Inna"
"Haka ne amma da so samu ne ku dawo nan ɗin da zama tun da akwai filayen da yawa gasunan ana ta yanka ma ƴan uwa" Cewar Inna Mune

"Ai yanka fili ba matsala bace, Yanda Inna da Umma suka saba da Zaria zasu yadda su bar Zaria ne su dawo cikin mu?

Charaf Inna ta ce,"Idan zaku bani AYMANA zamu dawo, wollah ai kuna da kirki shosai wallahi" tayi magana da hausan ta na tsofaffi.

Kaf falon kowa yayi dariya,, naji Grandpa na cewa,"Umma da fatan zaki kula da Anam har ta gama hutun zuwa lokacin da zaku dawo nan ɗin"

Umma tayi murmushi tana jinjina kai,Amma fara'ar fuskar Khausar ta sauya hakan ya tabbatar min da bata ji daɗin bin su Zaria da zan yi ba.....ban bi ta kan ta ba, ɗaki na shige don ina da abin yi, duk dama da saura tafiyar tasu sai nan da sati ɗaya hira ce kawai ta kawo hakan amma khausar ta biyo ni ɗaki tana min tambaya.

"Anam kaman farin ciki kike da tafiyar da zakuyi ko?tana tuhuma na.

"Kwarai ina farin ciki mana Khausar, ke kuwa waye zai ki dangi kamar su Umma?...Na mayar mata da amsa kai tsaye.

Wurga min harara tayi ta kafin tayi kwafa ta tashi ta fita, tana cewa, "Ni na tafi wajan Ɗan uwa na ma hira zamuyi yau"

Kafin ta fice daga ɗakin nace,"Allah ya tsare Khausar"....har da amsawa wai, "Amin Anam."na cigaba da aikina.

Khausar na zuwa wajan Ayman, ta same shi zaune saman fancy chair yana shan zobo drink....yayin da yayi relax akan kujerar ya ɗaga kansa sama idanuwan sa na kallon sararin samaniya....sallamar Khausar ita ta dawo da shi daga trance ɗin daya shiga, ya amsa da gyaran murya ba tareda ya ko kalli gefen ta ba.

"Ɗan uwa, Barka da hutawa", Khausar ta faɗa tana mai ajiye kujera kusa da in da ya zauna ta cigaba da cewa,"Ɗan  uwa ina magana ka min shiru"

"Ina bukatar na keɓance ni kaɗai ne Khausar" Ayman ya bata amsa a takaice.

Kai,Ɗan Uwa ni gaskiya bana son irin haka, na zo ne fa mu tattauna kan batun yadda kake aikin ka, ina son salon ka wallahi, ka koya min kaji Ɗan Uwa na"

Kamar yaji takun tafiyar ta da sauri ya juya hanyar shiga sashen Abhi, ya hango ta tsaye ta sauya shiga cikin normal abaya as usual, car keys ne a hannun ta, da alama fita zata yi....da sauri ya tashi ya nufi wajan ta, yama manta da cewa Khausar na wajan, ya sha gaban Anam a dai dai lokacin da take kokarin buɗe mota.

"Yaya Ayman" na faɗa a hankali da sanyin jiki, saboda na sani Khausar na kallon mu, kuma bana son tayi zargin wani abu bayan ƴan uwan takan dake tsakanin mu".......Ko a jikin sa, ya karɓi makullan ya ce,"Anam ki taimaka ki bani wannan daman na yau kawai na zama driver ɗin ki, zan tuka ki nayi yawo dake a faɗin garin Daura, duk in da kike so, na miki alkawarin zanyi tukin da har abada babu kamar sa"....Murmushi nayi, kalaman sa sun saka na manta da kalubalen Khausar hakan yasa na bishi har motar sa kamar rakumi da akala.

©FADILA IBRAHIM

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now