03

18 4 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 03

Copyright©FADILA IBRAHIM

ƘASAR HAUSA

Idan kuka ji ance ƙasar hausa tunanin ku da hankalinku zai baku wata ƙasa ake magana?

Asalin kasashen hausa waɗan da Bayajiddah ya kafa kuma ake kiran su HAUSA BAKWAI sune Kano,Katsina,DAURA, Gobir,Rano, Garun gabas da ZAZZAU a cikin ta bakwai waɗannan sune ƙasashen hausa.

Kamar yadda kuka sani a kowacce bikin sallah ƙasashen hausa suna gabatar da al'adun su bisa yadda addini ya tanadar.

BIKIN SALLAH

Hausawa na cewa "Sallah biki" "Ɗaya rana" ma'ana , Sallah dai wani lokaci ne na biki duk da kasancewar rana ɗaya ake yin ta a kowacce shekara sau biyu Musulmai, yare daban daban suke gudanar da wannan shagulgulan.

Sallah ibada ce da addinin musulunci ya sunnata, wanda a duk shekara ake yi sau biyu babba da karama...To amma Ƙasar hausa ba ibada kaɗai suke yi ba suna haɗawa har da lamurori na biki, Abubuwa da dama hausawa na gudanar dashi lokacin sallah wanda da yawa mutane sukan ɗauka kamar addini ne alahali kuwa AL'ADA ce.

Sallar layyah kowa ya sani Addini ya tanaɗar da sunna babba ta idan mutum yana da hali to yayi layyah da dabba mai kafa huɗu....idan kayi layyah kayi sadakan nama ga waɗanda basu yi layyah ba.....hakan na da nasaba da abin da yazo a koyarwar islama.

Wannan kenan

Kowani gida suna ta haɗa haɗan zuwa sallar idi wanda ake gabatarwa da karfe 9:00am wato tara na safe, a yayin da Gidan daurawa, ko wani gate na gidajen kakanni da iyaye da kuma ƴaƴa an fito da motoci domin zuwa cikin gari don aiwatar da Sallar idi a cikin al'umma.

Dr.SM DAURAWA ne zaune saman kujerar mai zaman banza, cikin motar sa yayin da iyayen sa biyu suna kujerar baya, sai Ado driver yan tuka su,

Sautin kira'a ne ke ta faman tashi a cikin motar na *Suratul Mu'uminoon*
sai kuma kamshin turarukan da ya gauraye dana kowannen su.....ringing ɗin wayar sa ita ta sanya hankalin su ko mawa kan ɗan nasu wanda duk da bai dame su su san wanda ke kira ba amma ya kamata ya sanya wayar sa a silent saboda su ba mutane bane masu son hayaniya.

Sunan ta ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar tasa *My Anam*, kasa ɗaukar wayar yayi saboda yana gaban  iyayen sa....har wayar ta tsinke, kafin a sake bugowa sai ya sanya wayar a flight mood daga nan kuma ya faɗa dogon tunani...tun da yake sallah bai taɓa fashin zuwa turkiyyah ba sai wannan karan, ko wacce sallah a cen yake yi sai dai da anyi sallah da kwana ɗaya yake dawowa Nigeria don yaba ma iyayen sa hakkin su suma....batare da sanin kowa hakan na faruwa ba....amma all of the sudden wannan shekarar abubuwa suna son taɓare masa, duk wani plan da ya ke shiryawa sai yaga baya working, to the extend that abin har yana sasu samun saɓani da iyalin sa Ammi.....ga iyayen sa sun ɗage masa ya fito da mata a cikin dangi ya aura if not zasu masa auran dole.

Abhi fa ba karami bane babban mutum ne amma har yau iyayan sa sun kasa binciko ainahin rayuwar da yakeyi a Turkiyya....sun yar da da halayen ɗan nasu, a tunanin su ko baya da sha'awar aure ne shiyasa har yakai wannan lokacin bai nuna musu matar da yake son aura ba a dangi.....despite knowing that shi fa Abhi baya son wannan auran dangin na AL'ADAR gidan su, infact shi ya zabi yayi aure ma tun bai gama makaranta ba shiyasa ya haihu da wurwuri......yana da buri guda ɗaya a ranshi yana son neman ƴar uwar sa da ƴan gidan su suka kora saboda ta auri bare, wasu *ASMA'U* Yayi alkawarin duk in da take a faɗin duniyar nan zai nemo ta kuma ya dawo da ita cikin zuri'ar su gaban iyayen ta, sannan shima kuma ya gabatar da nasa iyalin.

*Ni dai Diela nace, To amma Abhi kar ya manta cewa abin da mutum yake planning ba lallai ya kasance ya samu abin da yake so ba, komai yana canjawa saboda bawa yana na shi kuma Allah daya halicce mu shima yana nashi*

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now