40

10 2 0
                                    

AL'ADARMU
Page 40
Mallakin Diela

AFTER HONEYMOON, BAYAN CIN AMARCI.

2years later
Turkish Armed Force

Filin wajan ana kiran sa da reception, iyaye kama daga kan yara da mata da kowa sun zo tarban ƴan uwan su sojoji waɗanda suka dawo daga yaki.

"Abbu look, it's Momma" Kallon wajan Ayman yayi first look ɗin daya samu daga fuskar ta shiyasa farin ciki ya ziyarci zuciyar shi lokaci ɗaya ya sake wani kayataccen murmushi, kafin yayi wani yunkuri tuni Mustapha  (sunan Grandpa) ya fita ta karamin hanyar wajan yaje ya rungume Momma ta ɗaga shi sama tana saɓa shi a kafaɗar ta, sannan ta karasa in da Mijin nata yake.

"Welcome back Momma" Ayman ya faɗa yana manna mata peg a forehead ɗin ta da kumatun ta, ta kalli Mustapha Sulaiman Yusuf ta barbaza mishi gashin kanshi ta ce,"How are you Papi?

"Am good Mom" yaron ya faɗa duk da maganar ba sosai take fita ba.

Suka tafi gida, sun canja apartment don tuni Abhi ya sake wancen gidan nasu saboda ba kasafai yake zuwa Turkey yanzu ba, girma ya kama shi sai dai mune muke zuwa Nigeria.

Tsahon wata uku kenan aka tura mu ƙasar America, kuma Alhamdulillah mun gama aikin lafiya har mun dawo, wannan karan na ɗauki dogon hutu ne a base.

Muna ta shirin zuwa Nigeria.....Papi kam murna yake zaije yaga Grandpa da Grand grandpa ɗin sa.....muna private jet kasancewar mu yanzu bamu da matsalar tafiya saboda Abhi matsayin Abhi ya wuce in da ake tunani.

Da yamma misalin karfe huɗu daidai muka isa muna tsakar gidan namu, Ammi ne suke ta guje guje da Junior yana hango mu yayi ta wajan mu a guje yana kwala kiran sunayen mu....murnar ganin sa yasa na ajiye kayan hannu na na chaɓe sa sama haka zalika Ayman ma yayi masa yana masa wasa don Junior kam ya girma sosai shekara bakwai yanzu.

Sashin mu muka shiga, wanda tuni Umma ta sa an gyara mana shi tsab,Mun ci kuma mun sha sosai muna ta raha, Abhi yana Daura saboda Jikin Grandpa ya tashi....

Da daddare muna falon Ammi ana ta hira, sai ga Umma ta fito daga kitchen ɗin Ammi tana cewa, ƴa ta Anam zo daga ciki mana.

Dana ɗaga ido na hangi wasu manya manyan kofuna masu murfi, na ce ,"To Umma ina zuwa bari na je sashi na zan zagaya ne"

Umma ta yi dariya ta sani babu wani dawowan da zanyi, illai kuwa ai ina guduwa ban dawo ba....nayi wanka nayi shirin bacci, dama na sani Ammi baza ta bar Papi ya dawo ba, karfe goma Ayman ya shigo da wani kofi biyu a hannun sa, yana mika min ya ce,"Umma tace kishanye, kar ya kai gobe"

Yamutsa fuska nayi, na karɓa na ajiye a gefe, ina juyawa naga malamin ka ya tsira min idanu yana kallo na, ya ce,"Ba ance ki shanye bane"

"Gaskiya ni Yaya uhm uhm, haka wancen karan ma ina sha, sai da na sha wahala, kuma kuma ance idan ana sha wai ciki akeyi Allah kuwa"

Ayman ya kyalkyale da dariya, ya ce,"Ko kisha ko na miki ɗure, ni da nake so kafin ki koma hutun nan an sama Papi kanwa,"

Na zare idanu, na ce saboda bakai kake haihuwan ba ko, ina buɗe kofin kamshin su na'a na'a da kanunfari ya daki hanci na tuni na ji amai ya taso da gudu nayi ban ɗaki na kwararo amai sosai na galabai ta, har sai da Yaya Ayman yazo ya wanke min baki ya ɗauko ni ya kwantar dani saman gado yana min sannu.

To fah yau dai duk abin da nake ɓoyewa kowa zai sani......"Anam tunanin me kike yi ne haka, ina ta tambayan ki kin min shiru"

Yaya Ayman ke magana, na zurfafa cikin tunani nace,"Me kace Yaya nah"

"Cewa nayi, meke damun ki ne, nifa tun muna Turkey na lura kaman baki da lafiya sosai, ko zamu je hospital ne?

"Uhm Uhm am fine bana son warin abin nan ne" na faɗa ina tura baki.....Yaya Ayman ya ɗauki car keys, ya ɗauko zumbulelan hijabi ya yafa min, ya ɗauke ni cak har cikin mota sannan ya rufe, kai tsaye private hospital muka je.

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now