18

7 2 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 18

©Fadila Ibrahim

AL'ADAR ƘASAR HAUSA

A cikin Al'adun ƙasashen hausa wanda aka fi ji dasu sune Biki da Sallah,...yau ake gudanar da bikin ɗaya dag cikin jikar sarki wacce take matsayin ƴa ga Innar Abhi.

Dalilin da yasa mu gayyar soɗi Khausar ta dame ni akan na shirya muje naga yanda suke gudanar da al'adun su idan biki ya tashi.

Ɗinkin atampha na sanya riga da zani, rigar ta sauko iya gwiwa, na ɗaura ɗan kwali irin ɗaurin zara buhari bana mantawa ana yawan cewa wai ina kama da zara buhari, buhari shugaban ƙasar Nigeria ashe tushen sa Daura ne.

Na fito fes Bahaushiya dani, nayi matukar kyau wanda muna sauka daga kofar gidan sarki aka soma kallo na, ana bin mu da idanu, har muka shiga cikin gidan masarautar....mun bada gaisuwa ma kowacce mata, kai tsaye muka shige wani ɗaki daga cikin sashin mahaifiyar Inna.

Khausar na ta min hira akan wani case da tayi last week a kotun magajin gari Kaduna..Ta ce,"Anam, wata karamar yarinya ce ƴar shekara goma sha huɗu, iyayen ta suka ɗaura mata aure da wani mara lafiya, yana da matsalar iska, idan suka motsa bugun ta yake ba kakkautawa.....wai ɗan uwan ta ne shine suka haɗa su auran zumun ci"

Na ce,"Subhanallah, wannan ai zalincu ne, tayaya za'a aura ma yarinya ƴar shekara sha huɗu mahaukaci........cewar Anam tana cikin magana Khausar ta katse ta tana cewa,"Kuma ba garin su ɗaya da iyayen ba, How on earth iyaye zasu rinka wannan sakacin, ai ina mai tabbatar miki an raba auran, saboda yarinyar tana kwance a gadan asibiti fuskar ta ya kumbura tsabar dukan ya ya mata"

Nace, Ahh to raba auran shine maslaha, gaskiya ta bani tausayi, shi kuma wani hukunci kotu ta yanke masa?

"Kotu ta bada shawara ga iyayen sa da su tashi tsaye su nema wa ɗan su lafiya bawai suyi mishi aure ba, saboda abin da yake yi wata rana har ƴaƴan sa ma zai daka kuma ya halaka su"

Sure!!!!......zanyi magana ne muka ji an fara kiɗe kiɗe da raye raye, ai kuwa Khausar ta ja hannu na muka fita, babban filin gidan Masauratar Daura, ganin doki, da maza sunsha kayan sarauta, da rawani, abin ya burgeni, ga matan katsina zaune gefe guda a jere suna buga shantu da kwarya cikin ruwa suna wakar gargajiya abin ya bada citta makura, hankali na ya sake karkata ga filin da aka zagaye shi da kara aka ɗaɗɗaure, ana wasan doki.

Mata da maza sun ci ado da kwalliya, taron yayi taro baka iya ganin wani naka tsabar jama'a, kawai naji an toshe min baki an ɗauke ni cak ina son nayi ihu amma na kasa, ina son na janyo Khausar amma mayafin ta ya kubcewa hannaye na, hankalin ta ma baya wajan tsabar tana kallon raye raye.

Na yi azamar ɗaga waya ta na kirawo lalubo lambar wayar Unknown na ya ɗauka amma bana magana, ina jin shi ya kasa kunne yana hello hello wanda ko waɗanda suka ɗaukk ni balle suji abin da ake faɗa daga cikin wayar ba....Cikin wata jeep baka suka jefa ni suka rufe motar na fara ihu tsananin tsoratar da nayi,....karɓan wayar kawai naji anyi bayan sungano cewa akwai waya a hannu na.

Kai tsaye gidan su Deen suka kai ni, da kafata na shiga gidan tun ina tirjewa har na karasa, sanin cewa babu kowa a gidan saboda mun haɗu da Momma a Masarautar daura suna ta sha'ani da ƴan uwan ta.....Tuna hakan yasa na fara tsoron abin da zasu min a wannan gida.

ZARIA

Farfajiyar tsakar gidan Umma, yayin da kowa ni abu yana zaune a muhallin sa babu wani kazanta sai ma tsafta zalla wanda dole ne tsakar gidan ya baka sha'awa kasancewar ƙasar tsakar gidan ja ce gefe ɗaya kan baranda kuma anyi siminti.

"Salamu alaikum, a bani daddawa na hamsin kuka na hamsin" wani yaro yayi sallama yana mai shigowa kamar an hakaɗo shi... yayin da shigowar tashi tayi daidai da sallamar Abhi.

"Assalamu alaikum warahmatullah"

Umma ta waiwayo tana amsawa, fuskarta ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa yayin da take dama fura dakar Inna..tsame hannun ta tayi, ta wanke a cen gefe sannan ta taho tana musu maraba.

Inna ta ce,"Barka da zuwa dai Sulaimanu takwaran Aimanu na, Ba tare kuke ba ne ina yake ne"

Abhi yayi murmushi yana ce ma Riya ta shigo, bayan Umma ta shimfiɗa musu katuwar tabarmar kaba suka baje abin su, nan da nan aka cika musu wajan da kwanonin abinci kashi kashi, sannan sai kwaryar fura wanda tasha kindirmo kamar anyi ɓarin nono,....Umma ta zauna suka gaisa cike da murnar dawowan sa tana, Riya ta gaishe ta cikin harshen yaren su na cen don ba kasafai take turanci ba.

Inna ta samu abinyi tun da taji Riya tayi wani yare, tayi sauri ta bawa yarin daddawa ta dawo wajan su tana cewa,"Ina kuma ka samu mana wannan mai yaren inyamurai kuma Sulaimanu"

Abhi ya ce,"Tana gaishe kune da yaren Turkiyyah, tana zama ne tare da su Ammi da Anam, tana taya su aikace aikace, to sun taho sun bar ta shine na taho da ita"

"Ayhoooooo ni dai ince, amma kuma tana kama da inyamuran ƴan cen gadin ne ko? Inna ta sake tambaya.

Umma dai taga abin Inna ya fara yawa, fama ita idan akayi bako daga ta faɗi wancen sai ta faɗi wannan haka take.....Umma ta ce,"Inna a ƙasar turkiyya basu da inyamurai, yaren su daban yake dana najeriya"

Inna ta galla wa Umma Asma'u harara ta yamutsa fuska ta ce,"Sannu zakakura, yo ai naga bake na tambaya ba zaki wani zake kina min baya ni, sai ki bari ƴan ƙasar suyi magana, ke da ko Nijar wannan ma baki taɓa zuwa ba, naii dallah".....Inna ta gama zazzaga wa Umma Asma'u ta tashi tayi tafiyar ta ta zauna gaban buhun daddawar ta ta cigaba da murzawa....tana yi tana waigen Riya da sun haɗa ido sai ta sakar mata murmushi.

Abhi dai ya kasa cewa komai, tun bayan Inna ta gama masifa sai suka koma daga uhm sai uhm uhm....sun ci sun sha, duk da Riya batayi tsammanin abincin ƴan najeriya zai yi daɗin ci haka ba tas suka cinye...sannan suka tashi su kayi sallah daga nan kuma Abhi da Umma suka taɓa hira, ita kuma Riya tayi ƙawa tana wajan Inna tana taya ta matsa daddawa...Inna na tambayar ta wai tasan miye wannan.

Riya ta gyaɗa mata kai, duk da bata gane me tace ba amma ta fahimci inda tambayar nata ya dosa, ta ce "Abhi yana kawo musu, Anam na yawan amfani da shi a girkin ta"

Inna kam gyaɗa kai tayi batareda ta gane abin da Riya tace ba, ta cigaba da surutun ta.

Abhi ya ce,"Ina fatan kun shirya gobe zamu je Daura, In Sha Allah, Aiman na cen, zamu same shi a cen"

Kamar bugun ganga yadda ake bugawa da sauri sauri, haka zuciyar Umma ta soma bugawa jin an ambacin DAURA.

©FADILA IBRAHIM





AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now