STILL MY FAMILY.

25 6 0
                                    

SHUKRAH.


Na
Zainab Yakasai (Shukrah).


Page 34.
STILL MY FAMILY.

CIGABAN LABARI.

1st,December 2022.

Ranar ɗaya ga watan December rana ce da tayi dai-dai da cikar Daada Shekara Tamanin, a ranar kuma Hamma Sageer ya haɗa gagarumin taron taya Daada murna da kuma sadar da zumunci a tsakanin ƴaƴa da jikokin Daada.
Tunda nayi sallar asuba ban koma ba saboda zumuɗin wannan ranar da muka daɗe muna shirya mata, kasancewar tunda Maama ta girma ta ɗauke min nauyi girki da sauran aikace-aikacen gidan ina idar da karatun Al-qur'ani wanka na shiga, ina fito na shirya sannan na wuce room ɗin yara na tashe su suyi wanka na fito na tarar Maamah tana jera abinci a dining, mayar min da murmushin da nayi mata tayi kafin ta tawo tamin side hug sannan tace "Good Morning Mami na! ya kika tashi?", na shafa kanta ina ƙara jin sonta da yake nunkuwa a raina with every passing second nace "Morning My Baby! ya ƙoƙari?", tace "Alhamdulillahi! Mami naga har kin shirya, gaskiya kinyi kyau Mami! i love you and i want to become like you when i grow up", na kalli kaina cikin Coffee lafaya me adon flower milk da aka ƙara ƙawata shi da stones ƙanana da manya, ni kaina nasan nayi kyau ba kaɗan ba har yanzu murmushin dake kan fuskata be ɓace ba nace "Maamah kullum sai kin faɗi haka and i know right you didn't forget how badly i've treating your father right before your eyes", ta ɗago tana kallon cikin idanuwa na har yanzu bata bar murmushin da take ba kafin ta kama hannuwana duka biyu ta damƙe sannan tace "Mami! i and Daddy know you're not that bad, kawai kina taking revenge of what he did to you ne, saboda Mummy Sajeeda da kan gidanku daya tarwatsa, kullum yana faɗar haka kuma nima nasan ke mace ce ta gari kuma uwa ta gari and everyone have his good and bad sides bare ma what you did wasn't that bad, ɓacin rai ne".
A hankali na dinga yin ƙasa har na durƙusa a gabanta ita ma ta biyoni, ina jin ba daɗi a raina nace "Maamah! upon all that i did ashe zaki iya yabo na? gaskiya idan ban godewa Allah da baiwa da ni'imar da yayi min na samun yarinya kamar ke me hankali da nutsuwa ba sai ya tambaye ni", sai ta rungumeni sosai kafin tace "I so much love you, Mami! ina kuma so kimin wani favour please", na ɗagota ina wiping mata hawayen daya fara gangaro mata don Maamah sak ni ce ba wuya abu ya fara sata kuka, kafin nace "Say it, faɗi abinda kike so ni kuma na miki alƙawari in dai baifi ƙarfina ba zan miki shi", ta miƙo min ƙaramin ɗan yatsan ta sannan tace "Promise?", na karɓa nima nace "I promise, Baby", sai ta kalli gefe ta ƙara tattaro nutsuwarta kafin tace "Ki min alƙawari ba zaki ƙara tafiya ki barmu ba, sannan inda hali ina so ki yafewa Daddy na", ta ƙarasa tana pointing Mahdi da bansan sanda yazo gurin ba, gabana yayi mummunar faɗuwa don ban shirya yafe masa ba, tunda kusan alƙawari na yiwa kaina ne, amma ba zan iya karya alƙawarin da na yiwa Maamah ba don ina so ta dinga koyi da kyawawan aiyukana ne ba akasin haka ba, sai na sunkuyar da kaina don alfarmar data nema ta biyun tayi min nauyi amma duk yadda nakai ga neman maganar da zan gaya mata rasawa nayi lokaci ɗaya kuma naji zuciyata ta sakko akan Mahdi kamar wadda asiri ya saki, bakina har rawa yake sanda na buɗe ba tare da na kalli ɗaya daga cikinsu ba, nace "Ba zan iya ƙara tafiya na barku ba Maamah komai wahala, i promise you this", sai nayi shiru don for the very first time naji nauyin idanuwan Mahdi a kaina, Maamah da na tabbatar ta fahimci yanayin da nake ciki ta ƙara riƙe hanayena with concern tace "Shame the devil Mami!, ki yafewa Daddy kema Allah zai yafe miki", na ɗago muka haɗa idanuwa dashi and in his eyes i see love, care, concern and sacrifice.
Sai da na miƙe na juya musu baya kafin nace "Na yafe masa, ina fatan nima zai yafe min mistakes ɗina", unexpectedly, naji Mahdi yayi hugging ɗina tightly ta baya, ina iya jin yadda bugun zuciyarsa ya ƙaru sosai (Tachycardia), muryarsa na rawa kamar yadda hannayensa dake kan cikina suke yace "Da gaske? ya Allah nagode maka, wife! wallahi ban taɓa kwana da wani abu da kika yimin a raina ba, na yafe miki tun ba yau ba", sai kuma ya kawo bakinsa dai-dai right ear ɗina yayi da murya yadda   Maamah ba za taji abinda yake cewa ba ya ɗora da "Hope you'll find a place for my love in your heart, ko kaɗanne, Dan Allah!", idan nace tone ɗin da yayi amfani dashi beyi nasarar kassara tunanina ba nayi ƙarya don haka kasa bashi answer nayi, shi kuma ganin Twins sun fito tare da Deedat yasa yayi breaking hug ɗin.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now