HIGHSCHOOL I

26 6 2
                                    

SHUKRAH.


Na
Zainab Yakasai.

007.

Hi guys! hope you're enjoying every chapter,is the story interesting? do you've any suggestion,complain or advice about this novel? okay my DM is alway open for you,feel free to reach me out on WhatsApp through 09028979356 or on Wattpad at ZainabYakasai.

HIGHSCHOOL I.
(B.U.K KANO,2005).



Zaune muke ni da Ni'ima a gaban department ɗinmu ko wacce riƙe da handout muna discussing akan Genetics, Ni'ima tace "Shiyasa nace bazan auri guntu ba kafin nazo ina haifar ƙananan yara haka kawai azo a sakasu a front seat a makaranta su shiga uku da idanun invigilators ranar exam", na kyalkyale da dariyata da ban cika yi ba sai dai in abun ya bani dariyar sosai ko kuma naga mugunta sai na tuna da Saj da kullum take cemin 'Mugu mugu me rowar dariya',na kawar da tunanin ina murmushi nace "Nikam be wani dameni ba kawai dai ina so idan zanyi aure na auri ɗan Maiduguri,kinsan mazansu kamar daga heaven aka ɗaukosu masu kyau abunsu,gashi sun iya soyayya da treating mace with care kinsan Auwal mijin Adda Basma ɗan Maiduguri ne,bakiga yadda muke santin zamansu  ba in mukaje gidan da Saj", Ni'ima tayi dariya tace "Ai kuwa nima naji labari amma dai nafi so nayi aure a kano kinsan fa bana ƙaunar nayi nesa da Mami bakiga ko hutu a gida nakeyi ba?", na taɓe baki nace "I don't mind Cuz i know no matter how far i'll go in the name of marriage Daada will surely come for me when ever the need arises,and to me long distant marriage is the very best at least you'll adopt another culture free of charge,bare ma auren ɗan Maiduguri...Hmm".
Na ƙarasa ina ɗaga kai kamar me hasashe.
Fusge handout ɗin da naji anyi a hannuna ne yasa na juya da sauri,Sajeeda ta na gani a tsaye tana min dariya daga bayanta Uncle ne,ta zauna a gefena tace "Ɗan Maiduguri ko? zan gayawa Daada sai kawai a haɗaki da Musaddam ƙanin Hamma Auwal" na ɓata fuska nace "Allah ya kiyaye me zanyi da wannan Musaddam ɗin? daga ganinsa fa anga ɗan duniya,na tsani irin kallon da yake min kamar maye saboda rashin ɗa'a" na ƙarasa ina watsawa Uncle ɗin Sajeeda harara don tunda sukazo yake ta min irin kallon dana tsana,dama da biyu na faɗi maganar. Yako sha jinin jikinsa sai ya fara kame-kame yace "My Saj,barin koma office ina da Lecture by 4:00pm" ta langaɓar da kanta tana kallonsa kafin tace "Okay love,take care", yana juyawa Ni'ima da tunda Suka zo batace komai ba tace "Inyee love birds" Saj ta kai mata dukan wasa tace "Wai ni ba yayarku bace ba?" nayi caraf nace "Lallai Shekara biyun da kika bani ne kike wani hura hanci akai? dani nayi magana sai ace min gyambo sarkin son girma", tana dariya tace "To ai Hamma Sageer ɗin naki baya nan,shi ya kamata ki gayawa", na taɓe baki kafin nace "Saj,ina tunaninki sai gaki wai ma ke kikazo yi nan?", ta rungumoni tace "Allah Sarki ƴar uwata ashe haka kike sona? daga rabuwa ko good 6 hours ba ayi ba har kin fara missing ɗina?", na cuno baki kafin nace "Missing dai?Allah ya kyauta and baki bani answer na ba,na dai san ba gurina kika zo ba",tana dariyarta me kyau tace "Wai me ya kawoki Department ɗin nan ne? da Journalism kika dace seriously,well Uncle ne yaje har department ya fito dani wai he's bored mu ɗanyi zagaye" taɓe baki nayi ban kuma cewa komai ba.
Daga haka muka cigaba da hira kafin a kira sallar La'asar, Mosque ɗin department ɗinmu wanda tabarma kawai muka samo muka ware wani gefe muka shimfiɗa muka mayar masallacin muka nufa tunda da alwalar mu,muna idarwa kuma muka raka Saj department ɗinta don itama tana da lecture.

Sai 6:00pm muka gama lecture ɗinmu,gaba ɗaya mun gaji gashi mafi yawancin Student's ɗin are not interested in the lecture don Statistics mukayi, ni daga baya ma bacci nayi sai da Lecturer ya fita Ni'ima ta tasheni.
A department ɗinsu Saj muka zauna muna hira jefi-jefi tare da Ni'ima da mafi yawancin ranaku muke tafiya tare don itama a hotoro gidansu yake,mu Hamma Sageer ke fara saukewa sannan ya tafi ya kait,muna ta zaune sai ga motar gidanmu tazo amma instead muga Hamma Sageer sai mukaga Hamma Bassam,na ɓata rai na shiga baya nida Ni'ima ita kuma Saj ta shiga gaba don sunfi shiri dashi,sai da yayi zooming off sannan yana kallona ta cikin mirror yace "Hamma beji daɗi ba ya matsamin sai nazo ɗaukar ku,Saj don ke nazo ba saboda wannan baƙar yarinyar ba",na watsa masa harara nace "Ɓaƙi ai gado nayi" ina nufin a gurinsa na gada don kaf gidanmu ni dashi ne kaɗai baƙaƙe sai Usman da yawon football a cikin rana ya dafar dashi, ya harzuƙa dama bama jituwa dashi sam yace "In kika min rashin kunya wallahi sai kin sauka a motar nan", na harareshi kafin nace "Ni da motar ubana?", yayi parking sannan yace "Sauka sai Uban naki yazo ya maida ke gida", Sai da na sauka sannan nace "Ba lefinka bane,darajar uban naka ne da baka sani ba". Be ƙara kulani ba yaja motar yayi gaba,naji kamar na ɗora hannu a kaina na fasa ihu jin ana kiran Magrib,nasan da wuya na samu Taxi tunda unguwar mu da nisa daga B.U.K, gani zabuwa uwar tsoro indai ba da Saj ko Hamma Sageer ba sai ko Umma bana taɓa yadda duhu yayi min a waje,kuma hakan ya samo asali ne daga Androphobia dana gamu dashi a shekarun baya.
Ganin tsayuwa ba zata yimin ba sai kawai na fara takawa zuwa gate amma ko nisa banyi ba wata mota tazo ta wuceni,har ta gota sai kuma ta fara yo baya a hankali,na tsaya cak a tsorace ganin me motar yayi parking a dai-dai inda nake.
Saukowa yayi daga motar ya zagayo inda nake yana kallona,niko dake a tsorace nake sai na koma baya ganin ya tsaya daf dani.
Fuskantar na tsorata yasa ya ɗan koma da baya yace "Oh sorry,ina kikayi nayi dropping ɗinki?", nayi masa wani irin kallo nace "Haka akeyi dama? daga ganina sai kace na shiga motar ka?", da mamaki yake kallona kafin yace "Ba saceki zanyi ba baiwar Allah nima student ne" ya ƙarasa yana ciro I.D card ɗinsa daga front pocket ɗin shirt ɗinsa ya miƙo min, ba tare dana karɓa ba nace "Shikenan,kaje nagode",ya jingina da motarsa yace "To muje na saukeki a gate zakifi saurin samun mota", na kalli wani gurin not ready to talk, pleadingly yace "I insist". Sai na tsinci kaina da kasa ce masa A'a ban sani ba ko don naga student ne shi ɗin,sai kuma kamar ana turani na isa gaban motar,yasa hannu ya buɗe min ya zagaya ya shiga muka tafi.
Shiru motar tayi da farko muna sauraron Addu'ar Sheik Ahmad Sulaiman cikin sautinsa me daɗin sauraro,kafin daga baya yayi gyaran murya yace "A wani department kike?", kamar ba zanyi magana ba sai kuma na tuna girman taimakon da yayi min na daure nace "Nursing nake" yace "Wow! Nima ai nima haka amma final level nake,kefa?" nace "200 level",yace "Amma ban taɓa ganinki ba,abun mamaki nafa san kusan kowa a department ɗin", nayi murmushi nace "To ai kusan kowa ba kowa bane,ba kuma dole sai ka sanni ba" ina faɗar haka na mayar da idona kan titi ganin mun kusa isa gate kasancewata bame yawan surutu ba yasa surutun mutane ke saurin damuna,da alama yasha jinin jikinsa sai naji yace "Haka ne".
Koda ya saukeni a gate ƙin tafiya yayi wai sai yaga tafiya ta,haka muka daɗe a tsaye har aka kusa kiran isha kafin na samu taxi nayi masa godiya muka wuce.
Ina zuwa gida kamar yadda nayi expecting Daada na tsaye a balcony ya goya hannunsa a baya da alamar ni yake jira don haka ya sabayi duk in matarsa ko wani a cikin ƴaƴansa yayi dare a waje,ina ƙarasowa yace "Daga ina kike?", gabana ya faɗi kar dai ƙarya Bassam ya shirya min,a tsawace Daada ya kuma cewa "Ba magana nake miki ba?",zan iya cewa a tsawon shekaruna ban taɓa ganin Daada yamin ihu ba sai dai ɗan faɗan da ba a rasa ba.
Muryata na rawa nace "Daga makaranta Daada", yayi murmushin takaici yace "Ashe kin canja makaranta ban sani ba? naga dai an ɗauko Sajida tun ɗazu,ko ba tare kuke dawowa ba dama?", idanuna suka kawo kwalla don ba wahala suke min ba nace "Daada shine yace na sauka wai kaje ka ɗauko ni" Daada yace "Ai rashin kunya kika masa", ina goge hawayena nace "Ba haka akayi ba Daada ka tambayi Sajeeda ai tana motar akayi komai".
Kafin Daada ya ƙara yin magana Hamma Sageer da dawowarsa kenan daga Mosque ya ƙaraso gurin mu yana kallona yace "Sai yanzu?", ban kalle shi ba bare yasa ran answer na sai naga shi da Daadan sun juya zuwa Parlour, a hankali nima naja ƙafata na bi bayansu ina karanto kowace addu'a ce tazo bakina.
Ina shigowa kuwa Umma dake jirana tazo da sauri ta fisgoni tace "Me ya hanaki biyo Bassam", na fara kuka don nasan halin Umma duk da mun shiga University dukanmu ba wahala yake mata ba a ciki ciki nace "Ubana ya zaga kuma yamin gori wai ni baƙa ce", Daada,Hamma Sageer,Hamma Ishaq da duk sauran ƴan parlour sai da sukayi dariya banda Sajeeda dana kula hankalinta a tashe yake sai Umma da ɓacin rai yayi mata yawa,banga Bassam ba kuma nasan ƙila yana gurin Aunty tunda dama shi Mummy's boy ne ko da yaushe yana tare da ita.
Allah ne ya taimakeni Hajiya na parlour ita ta kafa ta tsare ta hana Daada yimin faɗan da ya tanadar mun ta kuma janyeni daga gurin Umma kuma tana cewa "Dan Allah saketa kun takurawa yarinya daga dawowarta sai a hau ta da masifa,inace nake murna zamuyi Allah ya dawo da ita lafiya muje kici abinci" daga haka ta jani muka wuce side ɗinta.
Sai da nayi salla na zauna cin abinci sai ga Saj nan ta shigo,na haɗe rai don haushinta nakeji a gabanta akayi komai amma ta kasa kareni tun kan na dawo ga takaicin bin Bassam ɗin da tayi ta barni da Magrib a titi bansan inda na kama ba,duk yadda Sajeeda taso na kulata ƙi nayi haka ta haƙura ta fita. Ranar a ɗakin Hajiya na kwana,washe gari ma a Bus ba wanda na kula ina ta cika ina batsewa,Hamma Bassam dake mazaunin driver tunda Hamma Sageer be warware ba ya kalleni yana dariyar rainin hankali yace "Good morning Blacky" na watsa masa harara kawai bance komai ba saboda haushinsa nake ji don ya haɗani da iyayena tunda danaje gaida Umma da Asuba ƙin answer wa tayi,Daadan ma daya answer daga "Lafiya" be ƙara cemin komai bare bare yace muyi azkar kamar yadda muka saba haka naje nayi abuna ni ƙadai.




Shukrah.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now