MY FAMILY.

33 6 2
                                    

SHUKRAH.

Na
Zainab Yakasai (Shukrah).

Hi guys! hope you're enjoying every chapter,is the story interesting? do you've any suggestion,complain or advice about this novel? okay my DM is alway open for you,feel free to reach me out on WhatsApp through 09028979356 or on Wattpad at ZainabYakasai.

Page 15.

MY FAMILY
(Cigaban Asalin labari).

RIJIYAR ZAKI,2021.

Ganin tsayuwa ba zata yiwa Dr. Mahdi ba sai ya samu visitors chair ya zauna haɗe da dafe kansa nasan abubuwa da yawa ne suka haɗe masa na farko rashin kwantar masa da hankali da nake ga attack ɗin dana samu ga kuma yaran mu da muka bari a gida tunda bamu saba barinsu su kaɗai ba,juyi nayi na zuba masa idanu ina feeling pain inside me at the same time ina jin tausayinsa don he didn't deserve what he's going through,like he only showered me with love not hatred at least in ban masa biyayya ba be kamata in dinga saka shi a damuwa ba,na canja masa rayuwarsa komai nashi ya tsaya ko a gurin aikinsa ana yawan masa magana baya tsayawa yayi aiki kamar da,amma bazan iya sakewa dashi ba bazan iya bashi abinda yake so ba wato space a zuciyata ba saboda tawa matsalar da kuma maganar mu ta ƙarshe da Sajeeda . Na goge hawayen da suka zubo min tuno Sajeedar da nayi sannan a hankali nayi murmuring "Daddyn Deedat?" duk da banida tabbacin zai ji ni but to my surprise sai naga ya juyo ko da yake ba abun mamaki bane don ance malamai ji garesu kamar macizai,ya zuba min idanunsa da suke ɗauke da damuwa da gajiya kafin yace "Ammi,kin tashi? ya jikin?" na ɗan yi masa murmushi saboda tausayin da ya bani nace "Naji sauki kawai jikina keɗan ciwo,kayi magana da friend ɗinka suyi discharging ɗina mu wuce saboda yaran" ya ɗan kalli agogo nima na bi agogon da kallo,2:00am na gani nasan ko an sallameni ma bazamu iya fita cikin daren nan ba don haka lumshe idanuna nayi a ƙasan zuciyata ina addu'ar Allah ya karemin yarana da muka baro a gida".

Yadda na kwana ban rintsa ba haka shima Mahdi ya kwana sai dai abun tausayin shine tunda a zaune yayi rabin kwanan sai da 4:00am tayi sannan ya shiga toilet ɗin ɗakin ya ɗauro alwala sannan yaje office ɗin friend ɗinsa ya karɓo praying mat yazo ya fara Nafila,da asuba shi ya taimaka min naje toilet nayo alwala shima yayi sannan mukayi jam'i muka gabatar da sallar mu.
Muna gama addu'a kuma yace na kwanta kafin gari yayi haske yasa ayi discharging ɗina.
Around 7:00am Dr. Idris friend ɗin Dr. Mahdi yazo ya ƙara dubani ya min prescribing wasu drugs ɗin sannan akayi discharging ɗina.
Muna shiga gida na hango Maama da Deedat zaune a dinning area tana feeding ɗinsa sai naji wani sanyi a raina at the same time tausayinta ya kamani don nasan tasha rigima a gurinsa tunda be saba kwana da kowa ba sai da Daddynsa,Hijab ɗin jikina na cire na ajiye akan kujera sannan na wuce dinning area ɗin Dr. ma ya biyoni amma tun kafin mu ƙarasa suka taso da gudu Maama tayi hugging ɗina excitingly while Deedat yaje yayi hugging Dad ɗinsa kuma best friend ɗinsa,na shafa bayanta ina jin ƙaunarta na ƙara samun guri a raina kafin nace "Maama na,ya gida? Deedat ya miki rigima ko?" a shawaɓe ta ɗago daga jikina tace "Dakyar yayi bacci fa sai kuka yake yana kiran Daddy,Ammi next time duk inda zakuje ku tafi damu" ta ƙarashe muryarta na rawa and i sighted tears in her eyes sai naji tausayin rayuwarsu ya ninku fiye da wanda nake musu a baya,na daure don nima kar nayi mata kukan sannan nace "Insha Allah Maama ba zamu ƙara barinku ba kinji?" tayi nodding sannan tace "Ya jikin naki to" sai da na jata muka ƙarasa dinning inda su Dr. suke sannan na ɗauki fork na debo Noodles ɗin dake kan plate na kai bakinta ta karɓa sannan nace "Naji sauƙi sai ciwon jiki kawai" ta ƙarasa haɗiye abincin bakinta sannan tace "Ba damuwa,kiyi wanka zan miki massaging jikin ki, sai anan Daddyn dake feeding Deedat yasa mana baki yace "Don tsabar son kai Ammi kawai zakiwa massage?ita da ma ta kwana a kwance niko a zaune fa nayi spending night ɗin" ta zagaye hannayenta a wuyansa tace "Sorry now,Daddy kai fa namiji ne ai ku dama jarumai ne" ya ɓata fuska kamar zeyi kuka yana ture hannunta da wasa daga jikinsa ita kuma taƙi cirewa sai dariya take masa,yace "Ke kika sani,ni daga yau ma ba ruwana dake" yadda sukayi ba ƙaramin burgeni  yayi ba don it remind me of rayuwar mu ni da Daada sai na kyalkyale da dariya na masa gwalo nace "Deedat mana yaji haushi ya maka" ya dawo da kallonsa gareni sannan ya marairaice yace "Bashi zaiji haushi ba kece zakiji kimin" sai na kawar da zancen ta hanyar cewa "Ni dai zanje nayi wanka bacci nakeji" daga nan nayi gaba shima ya biyoni yana cewa "Abincin fa?kinsan fa ko jiya da kika dawo ba kici komai ba" nace "Kai,abincin nan ba yanzu ba Dr. wallahi sosai nakejin bacci".
 
Sai around 1:00pm na tashi shima kiran Zuhr ne ya tasheni,na miƙe ina salati idanuna suka faɗa kan Dr. dake baccinsa peacefully a gefena sai na samu kaina da ƙare masa kallo,ba yau na saba yi masa haka ba duk a ƙoƙarina na samo dalilin da zaisa na ƙara tsanarsa amma kullum kyau,nutsuwa,kamala da haƙuri nake gani a tattare dashi. Ban san ya tashi ba sai da naji hannunsa a fuskana yana dariya yace "Allah ya kamaki kinga kyakykyawa kin wani ƙura min idanu" na murguɗa masa baki ina ture hannunsa sannan na sauka daga kan gadon nace "Ai dai kasan na fika kyau ko?" yace "Oho dai ana so ana kaiwa kasuwa", ban ƙara cewa komai ba na wuce toilet nayi brush na ɗauro alwala, ina fitowa shima ya shiga kuma ko kafin ya fito har na idar don haka daya fito na bashi guri ya shirya naje na samu yarana a parlor suna kallo.
Zama nayi na ɗora Deedat akan jikina ina shafa kansa nace "Wannan gashin yayi yawa ya kamata aje a rage shi" Maama ta kallo mu sannan tace "Ammi Dan Allah abar masa sumar tayi masa kyau" taɓe baki kawai nayi na mayar da idanuna kan Tv sai naji Maama tace "Ammi abinci fa?" nace "Me kika dafa?" ta miƙe tayi hanyar dinning tana cewa "Steamed cous-cous ne da egg sauce". Ita tayi serving ɗina ina kuma cikin ci Mahdi yazo yayi joining ɗina muka cinye, Ta kuma ƙara mana tana cewa "Ammi yanga kikewa Daddy ko? gashi nan ai ya cinye" na harareta shi kuma yayi dariya yace "To lefinta kika gani? taga zuƙeƙe ba dole ta dinga yauƙi ba don ta burgeni" na ɓata fuska ina kallonsa sannan nace "Ai na gama burgeka shiyasa ma ka dinga yiwa Daada zarya sai da ka rabani dashi" yace "To cigaba da maganar in cinye abincin".
Shiru ne ya biyo baya har muka gama muka cigaba da kallo Maama kuma suna hira da Daddynta jefi jefi,sai da 2:00pm tayi sannan Maama ta tashi ta ɗaga Deedat suka wuce ciki don shirin islamiyya.
Suna fita Mahdi ya kalleni yace "I nearly forget twins will be coming for mid-term break" na faɗaɗa murmushina don nayi missing yarana,ina ƙaunarsu sosai a raina don daƙyar ma na yarda aka kaisu boarding school,nace "Kasan nima na manta,jibi ne ko?" yace "Uhm ai da wuri zanje na kawo miki su nasan damuwarki zata ragu ko?" nayi murmushi sannan nace "Ban yarda ba tare zamuje",ɗaga kafaɗa kawai yayi sannan yace "To,Allah ya nuna mana jibin" na answer da "Ameen" sannan muka cigaba da kallon mu.

Ranar Friday da sassafe muka tashi muka shirya saboda ɗauko Twins daga makaranta,sai da mukayi dropping Maama da Deedat a school ɗinsu sannan muka wuce Kibiya inda anan ne sukeyin Tahfiz. Muna isa muka tarar da iyayen yara da yawa don haka muka ɗan jiran har aka sallami wanda suke gabanmu,wani Malami da Dr. ya koyar a jami'a ne ya taso ganinmu ya risina yana gaida mu a ladabce sannan bayan mun gaisa ya tafi kira mana twins.
Da wani irin gudu Boy's ɗin nawa da suka ƙara zanƙalewa suka tawo suka rungumeni suna cewa "Ammi we missed you,yasu Maama?" nayi kissing cheeks ɗinsu sannan nace "We missed you to Boy's" na ƙarasa ina kallon Dr. da yayi folding hannayensa yana kallonmu,sai Siyaam ya tafi yayi hugging ɗinsa shi kuma Shaheed ya shagwaɓe yana kallona sannan yace "Kai Ammi,we've grown up fa ko kin manta nan da two months zamu cika 15years" nayi rufe bakina da hannuna irin na manta ɗin nan sannan nace "Oh na manta Manya,Allah ya nuna mana" daga haka naja hannunsa zuwa gurin mota suma suka biyo mu bayan Daddyn yayi signing.
  Ko kafin mu dawo cikin Kano dama closing time ɗinsu Deedat yayi don haka school ɗinsu muka wuce direct mukayi picking ɗinsu.
Suna shigowa motar kuwa suka cikamu da ihun murnar ganin Yayyen nasu,daga nan sai hira da labarin makaranta. Daga ƙarshe Maama tace da Shaheed wanda shine Hussain kuma shine me surutu ba kamar Siyaam miskili irina ba, "Wai kai ba Tahfeez kuke ba?" yayi nodding sannan tace "To kamin waƙa kayi praising ɗina da larabci ni kuma zan baka chocolate" yayi murmushi sannan yace "You're not serious nima ina da chocolate ɗin,bari na baki a kyauta amma bazan miki waƙa ba don ban iya ba" daga nan yayi unzipping backpack ɗinsa ya fito da Chocolates ya fara sharing,yana miƙo min dama nace "A'a nagode don tunda girma yazo min na watsar da kayan zaƙi aiko Dr. yace "Bani na wife ɗina inci mata", nidai shiru nayi a ƙasan raina ina tunanin irin halin Mahdi a rayuwa baya taɓa ɓoyewa kowa son da yake min ƴan uwansa ma sunyi masa masifar tunda sunga ba sonsa nake ba amma yaƙi daina sona,haka ba da son ransu ba suka gaji suka kyalenmu to yanzu gashi har a gaban yara nuna min soyayya yake. Sai da yayi parking sannan na dawo daga duniyar dana tafi,muka sauka a tare muka wuce cikn gidan, muna shiga kuma nace kowa yayi wanka yayo alwala yazo muyi rama sallar da mukayi missing sai mu ci abinci kafin la'asar.
Haka kuwa akayi Dr. ya mana limanci daga nan Na dafa mana spaghetti tunda ina da miya mukaci a tray ɗaya,moment ɗin daya dinga dawo min da rayuwata ta baya. ban bari mun gama ba na tashi Dr. da yafi kowa sanin yanayi na ya biyoni ɗakin,zan kwanta na fara aikin tunanin ya riƙeni yace "No please,not today yaranki na buƙatar farin cikin ki kinsani ko?" sai na fasa kwanciyar nace "Shikenan" ya ɗagoni tsaye sannan yace "Muje su bamu labarin makaranta" daga haka mukaje mukayi joining nasu a parlor muka yita hira har aka kira Asr.





Shukrah.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now