NO VACANCY IN MY HEART

36 10 6
                                    

SHUKRAH.




Na
Zainab Yakasai (Shukrah).



Page 32.
No Vacancy In My Heart (Cigaban Asalin Labari).


Na gyara zamana ina kallon Mahdi da tunda na fara bashi labari yayi pausing yana kallona ko blinking bayayi, sai kuma na kalli wall clock naga pass 2:00am.
Bin inda na kalla yayi sai yaga agogo nake kallo, ganin na miƙe na kwanta sai yayi saurin tasowa daga kan kujerar daya koma yazo ya zauna gefena yace "Haƙiƙa nasan ni me lefine a gurinki, i've ruined your life and your dream, i'm selfish i know amma ba lefina bane son da nake miki ne ya janyo hakan, ki yafe min", kamar bazan answer shi ba zuwa can bayan ya ƙara cewa "I'm sorry wife", sai na tashi zaune ina goge hawayen daya zubo min kan cheeks ɗina kafin nace "Ka fahimci a cikin ƙuncin daka jefa rayuwata tsawon shekara goma sha shida? saboda kai na rasa Sajeeda ta, saboda kai Daada ya min nisa muka koma stranger's da mutumin da nafi ƙauna na kuma fi shaƙuwa da", sai nayi pausing saboda yadda kuka yaci ƙarfina.
Without thinking twice Mahdi yayi hugging ɗina, nima kuma banyi ƙoƙarin fita daga riƙon shi ba don lallashi ne abinda nafi buƙata a wannan lokacin amma ba a gurinsa ba, naso ace Daada ne zai lallashe ni a wannan karon sai dai ba yadda na iya.
Yana cigaba da patting shoulder na yace "Ki ƙara bani dama, a karo na biyu zan nuna miki irin ƙaunar da nake miki don itace silar zaman mu a jiya, yau, kuma a cikin ta zamu rayu a gobe har zuwa ƙarshen numfashinmu, ki yafe min saboda ƴaƴanmu", maganganunsa suka sa na ɗago daga jikinsa ina ja da baya, a iya tsawon shekarun da muka shafe idan nace Mahdi be kyautata min ko be nuna min iya kulawar da wanda suka ƙulla auren soyayya suke samu ba nayi ƙarya, amma bazan iya yafe masa ba, zuciyata bazata iya saukowa daga fushin da take dashi ba saboda Sajeeda, Umma, abubuwan da suka dinga faruwa tsakanina da Hajiya, rabuwar kan gidanmu har zuwa yanzu da ni da Daada muka zamewa junan mu baƙi.
A hankali ina girgiza kaina nace "I can't Doctor, i just can't for there's no vacancy in my heart, Sadeeq ya cike ko ina da rauni kuma these wounds are yet to be heal, all this while".
Duk da a iya tsawon zaman mu da Dr. Mahdi ban taɓa kira masa sunan Sadeeq ba amma banga mamaki ko wani alamar tambaya jin na kira sunan a tattare dashi ba sai ma miƙewar da yayi yaje jikin bango yayi switching off bulb sannan ya zagaya ɗaya side ɗin gadon yayi kwanciyarsa.
Kamar yadda ban iya rintsawa ba tsawon dare haka nake da yaƙinin Dr. bai samu bacci ba don kusan duk juyin da zanyi sai naji ya motsa, nasan rashin samun haɗin kai na a karo na biyu ke damunsa ni kuma a nawa ɓangaren tunanin baya da kuma rayuwata a yanzu nake.
Sai da akayi kiran farko na sallar Asuba sannan muka tashi kusan a tare shi ya fita zuwa room ɗinsa yayinda na shiga nawa toilet ɗin na ɗauro alwala nazo na gabatar da nafilfili na neman yafiya da yardar ubangiji da kuma neman mafita a zamana da Mahdi.
Sanda na idar da karatuna bayan sallar Asuba komawa nayi na kwanta don tunda Maama ta shiga S.S3 aka bata head girl ta ɗauke min nauyin komai don bata yadda ta makara, ita ke tashi ta shirya Deedat, tayi breakfast sannan tayi serving kowa in mun tashi, wani lokacin idan ni ko Mahdi da muka saba dropping ɗinsu are in a haste da kanta take kaisu.
Sai da na gama shirina na fito da ɗan sauri don nayi bacci da yawa, na samesu dukansu a parlor tana serving ɗinsu don haka na ƙarasa ina answer gaisuwar twins sanan na ɗora da "Twins kuma a dining yanzu? who wake you guys up this early? ku da ba inda zaku you are suppose to have rest of your satisfaction ai", Maama tayi pouting kafin jealously tace "Kai Mami saboda Twins sunzo shine zaki manta dani?", na dungure mata kai playfully sannan nace "Ni dama ba ruwana dake because you're always backing your father, komai shine yayi dai-dai", kafin ta bada answer Mahdi dake feeding Deedat ya ɗago yana cewa "Seriously? don't tell me your jealous about that, ke kinga lefinta ne ita da Babanta kuma kice ba zatayi backing ɗina ba? ai ni da Maama tip da tire ne", bansan yadda akayi maganarsa ta bani haushi ba ko don na tuno yadda komai ya lalace tsakani na da Daada ne oho? sai na ɓata rai kafin nace "Ashe kasan zafin uba ni ka rabani da nawa", Mahdi ganin yadda yaran sa suka zuba min idanunwa saboda tone ɗin da nayi amfani dashi yasa ya kasa bani answer sai dai na kula jikinsa yayi sanyi don kasa kai spoon ɗin da ya ɗebo abinci bakinsa yayi.
Ganin haka yasa Maama ta kalli Twins tace "Boy's mu bawa su Daddy guri ko?", kamar yadda tace kuwa dukansu sai sukayi packing plates ɗinsu zuwa parlor.
Sai anan Mahdi ba tare da ya kalleni ba yace "Nasan kin daɗe da haddace kalamai na amma zan ƙara maimaita miki, wallahi da inada ikon mayar da hannun agogo baya da nayi, ba zance in an koma baya zan rabu dake ba sai dai zan ta bibiyarki in ta yiwa ƙaunarki biyayya har sai na sameki ta hanyar da kowasu ma'aurata suka samu junansu kinga sai mu gina irin gidan da ni dake muke mafarki tun farkon rayuwarmu, amma ki yafe min ƙaunarki ce silar halin da muka tsinci kanmu a yau", yana kaiwa nan ya ajiye spoon ɗin hannunsa ya miƙe zuwa ƙofa ba tare da ya bani damar bashi answer ba, hakan kuma da yayi yasa naji ba daɗi don nasan ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now