LOVE IS A BATTLEFIELD

27 6 2
                                    

SHUKRAH.

Na Zainab Yakasai(Shukrah).

Hi guys! hope you're enjoying every chapter,is the story interesting? do you've any suggestion,complain or advice about this novel? okay my DM is alway open for you,feel free to reach me out on Whatsapp through 09028979356 or on Wattpad at ZainabYakasai.

Page 12.

LOVE IS A BATTLEFIELD.
(Still a throwback).

Har aka gama event ɗin nan hankalina baya gurin dama daga nan Daada yace mu koma gida don haka muka bi motar su Hamma Bassam,ina zama a backseat idanuna suka shiga cikin na driver through mirror and i felt as if my heart jumped down to my abdomen from mediastinum na dai daure nayi ƙasa da kaina wondering what the person is doing in the car sai kuma na tuna lokacin da zamu shiga motar na kula kamar ba ta gidanmu bace,throughout the journey su Bassam ne da abokinsa sai Hamma Ishaq dake baya tare da ni da Saj ke hira mukam jan bakinmu mukayi muka tsuke,sai da akazo round na hotoro Hamma Ishaq yace "Hanif saukeni anan zan karɓi saƙo" nodding kawai wanda aka kira da Hanif yayi kafin yayi parking Hamma ya fita yana mana waving,sai da ya hau titi sannan ya kalleni ta mirror yace "Bassam wai Sister's ɗinka basa magana ne hala?" Bassam da hankalinsa ke jikin window ya juyo yana harararmu yace "Munafirci ne fa kuma waccan ta lokon ce ta koyawa wannan, sun ma gaisheka kuwa?" ya ƙarasa yana pointing ɗina nikam na murguɗa masa baki,daga nan ba wanda ya ƙara cewa komai har yayi parking muka fita muka barsu,na shiga gida ina jin idanunsu a kaina.
  Da daddare muna ɗakin Umma ni da Saj Usman ya shigo yace "Adda Shukrah kizo inji Hamma Bassam" na zaro ido ina miƙewa daga gaban bowl ɗin dambun naman da Umma ta zuba mana na koma kan gado nace "Kace masa bacci nake" Umma ta harareni tace "Meye haka? tashi kije kiji menene?" na cuno baki kafin na tashi ina murmuring "Umma to me zan masa?",daga nan nabi bayan Usman zuwa side ɗinsu ga mamakina shi da wannan guy ɗin na ɗazu ne a zaune a parlor da plates da alama abinci suka gama ci,ganin guy ɗin yasani ja na tsaya daga ƙofa.
Bassam ya harareni yace "Ko nazo na ɗaukoki ne?" na ɗauki kai kafin nace "To me zan maka wai?" sai naga ya juya a harzuƙe abunka da hot tempered person yana kallon abokin nasa sannan yace "Kagani ko? na gaya maka ba shiga harkar yarinyar nan nake ba ka dage gashi nan yanzu ka janyo min raini,to ni na cire hannuna you can go ahead and talk to her" daga haka ya miƙe ya nufo ƙofa yana kuwa zuwa kusa dani na matsa don nasan gaba zeyi dani yadda ransa ya ɓacin nan.
Sai da ya fita sannan friend ɗinsa ya taso zuwa gabana na ɗan matsa jikina na rawa don ban iya keɓewa da wani namijin da ba ɗan gidanmu ba,idan idanuna ba ƙarya suka min ba ma gani nayi parlor ya ƙara girma ai kuwa tsoro ya kamani, may be kula yayi da yanayi na sai naga ya koma inda ya taso ya zauna sannan yace "I've no intension of hurting you,i only saw you earlier nazo kusa dake ina jiran ki gama waya muyi magana and mistakenly kikayi banging ɗina amma naga yadda na tare miki hanya be miki daɗi ba shiyasa da muka ƙara haɗuwa a mota nace zanzo har gida na baki haƙuri tunda ke ƙanwar abokina ce" na ɗan samu relief sai na sauke ajiyar zuciya ina wasa da curtain ɗin da nake jiki har a lokacin sannan nace "Shikenan,Allah ya yafe mana gaba ɗaya" daga haka na juya zan fita sai naji yace "And please ina son wata alfarma" na juyo don bazan iya wulaƙanta shi ba don ba a koya min haka ba beside that ai abokin yayana tamkar yayana ne,sai nace "Allah yasa zan iya" yayi murmushi ya ƙara tasowa yana ƙoƙarin fito da wayarsa daga aljihu yace "Zaki iya,it isn't a big deal ki samin number ki please" ya ƙarasa yana miƙo min wayar,sai na ɗan matsa kafin nasa hannu na ture wayar sannan nace "Kayi haƙuri Hamma akwai wanda muke relationship da kuma mun yiwa juna alƙawarin aure" and in his eye's i saw the feeling of disappointment,lost and anger.
Ganin ya juya ya fita daga parlor sai nima na fita zuwa main parlor inda na tarar da Saj da Safiyya suna karatun Qur'ani nima kuma direct kan shelf na wuce na ɗauko nawa don inada alwala nayi joining ɗinsu.
Tunda na idar da sallar Isha'i na fara kiran Sadeeq beyi picking ba haka na bar masa kusan 30 missed calls,ganin ba picking zeyi ba sai na tura masa text amma shiru haka nayi spending kusan 2 hours a zaune in nayi kiran nayi kiran beyi picking ba sai na masa message but all my effort to talk to him went in vain,bansan yadda akayi ba kawai sai ji nayi na fashe da Kuka Saj dake kwance tana waya da Uncle ta tashi da sauri tana kallona sai kuma tayi hanging wayarta sannan ta min side hug tace "Shukrah! me yake faruwa? har yanzu beyi picking ba?" nayi nodding ina goge hawayena don ba zan iya magana ba,bubbuga bayana ta dinga yi tana bani haƙuri kuma cikin ikon Allah sai naji zuciyata tayi min sauƙi amma da na kwanta sai na nemi bacci na rasa na ƙurawa ceiling fan ido ina lissafin rayuwa,a yadda na shaƙu da Sadeeq da irin ƙaunar da nake masa nasan ko Daada ba zai iya rabani dashi ba,bazan taɓa bari wannan abokin Bassam ɗin ya shiga rayuwata yamin ruining relationship ba and i vow to have my relationship back no matter the difficulties, no matter the ups and down zan jure.

Sai kusan Asuba na samu nayi bacci aiko ina idar da salla na cigaba da kiransa amma wannan karon ma ko shiga wayar batayi,hankalina yayi matuƙar tashi dandanan kuma sai zazzaɓi ya rufeni nace Saj ta lulluɓeni.
Da aka gama breakfast ma ɗaki aka kawo min amma na kasa ci sai da Umma ta tsaya akaina nasha kunun amma ƙosan ma kasa ci nayi,ganin ba ci zanyi ba sai kuka yasa ta haƙura ta bani paracetamol ta fita. Tana fita kuma bata daɗe ba Hamma Sageer ya shigo ya ƙaraso jikin bed ɗin yasa hannu a forehead ɗina yana feeling temperature na,sai ya kalli Saj yace "Kuna bari sauro yana shigowa ko?jiya fa ƙalau take amma yanzu ga malaria ya rufeta", Saj ta fara dariya sannan tace Hamma Love sickness fa take ba wani abu ba" zaro idon Hamman yayi kafin yace "Really? bani labari? waye wannan amma bata bani labarinsa ba?" sai anan nayi magana nace "Hamma na bashi number ka fa be kiraka ba?" yace "Yes,ba wanda ya kirani" sai ya mayar da hankalinsa kan Sajeeda yana jiran jin labari,ai kuwa ta kwashe komai ta gaya masa.
  Ya juyo yana kallona sannan yace "Bani number shi na kirashi da wayata" da sauri kuwa na miƙa masa wayar bayan nayi searching number,karɓa yayi yayi dialing digits ɗin a wayarsa sannan ya kira. Bugu biyu kuwa yayi picking da sallamarsa, Hamma ya answer suka gaisa kafin yace "Hamma Sageer ne brother ɗin Shukrah,i learnt that you guy's misunderstood each other and you're not picking her calls gashi hakan ya kwantar da ita" dan jim yayi kafin yace "Eyya,zanzo gidan to in anjima" Hamma yace "Alright,i'll send you the address right away" daga haka sukayi hanging.




Shukrah.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now