HIGHSCHOOL III

20 5 2
                                    

SHUKRAH.


Na
Zainab Yakasai(Shukrah).

Enjoying the story? okay take a moment and hit the star at the end of this page on Wattpad.
Zainab Yakasai remain my username.



009.

HIGHSCHOOL III,B.U.K 2005.
(Still a throwback).

Har kusan asuba ina zaune a tsakiyar bed ɗinmu ina ta saƙa da warwara ganin hakan bazai fishsheni ba yasa na miƙe naje na ɗauro alwala nazo na fara nafila, sai abun yamin wani iri don ban saba yin komai ni ƙadai ba,da Sajeeda muke yin Nafila duk dare kasancewar horon da Umma tayi mana kenan. A haka asuba ta riskeni nayi sallah da liman nayi Azkar kafin na tashi na shiga toilet nayi brush da wanka sannan na wuce kitchen don Umma keda girki ranar.
Cikin sauri na feraye sweet potatoes na soya sannan nayi sauce ɗin kayan miyar da nayi grating lokacin da ina soya dankalin, koda na gama tuni ruwan zafin dana jona a ring boiler yayi don haka sai na dama garin kunu na sheƙa ina jin kewar Sajeedar da muka saba girki tare at the same time kuma ina mamakin SAUYIN RAYUWAR da muka samu cikin ƙasa da wuni ɗaya.
Lokacin dana kawo abincin parlourn Daada inda anan ne duka familyn ke haɗu don yin breakfast a kowace rana na tarar da kowa banda Hajiya,Sajeeda sai Hamma Gidaɗo da nasan ya tafi aiki tunda a bank basu yarda da makara ba,Safiyya ce ta taimaka min na zubawa kowa a plates da cups ɗin dana sa Usman ya ɗebo min. Banyi gangancin kaiwa su Hajiya nasu ba nasa Safiyyan takai musu a food and tea flask's ko ya sukayi dasu oho kawai sai naga ta dawo ta ajiye tray ɗin ranta a haɗe sannan ta koma gurinta ta fara cin nata abincin,duk abin nan da ake kuma Hamma Sageer ni yake ta kallo ganin na kasa cin nawa abincin na ƙurawa Hamma Ishaq dake gugar kayansa idanu.
Da hannu Hamman yayi min alama da inzo na kuwa tafi na zauna gefensa inda yake zaune a ƙasa,ba tare da ya daina kallona ba in a whisper yace "Me yake faruwa a gidan nan?", ina Umma?" na juya na kalli ƙofar room ɗin Daada sannan nace "Tana ciki", sai yayi nodding kafin yace "Sajeeda fa, banga ta fito kunyi girki ba ko bazata makarantar ba yau?", na karyar da kai ina shirin yi masa kuka ganin haka kuma ya sashi miƙewa ya riƙe hannuna muka fita, muna zuwa balcony yace "Kar kimin kuka,faɗamin meya faru?", a sanyaye nace "Ko ba Sajeeda ke fushi dani akan laifin da ban aikata ba" ya ɗan zaro ido yana kallona sannan yace "Ita Sajeedar? lallai bata kyauta ba to faɗamin mene laifin da take zargin kinyi mata",na cire hannuna ɗaya daga cikin nasa sannan na goge hawayena na faɗa masa duk yadda mukayi da Uncle ɗin Saj ban ɓoye masa komai ba",na karanci ɓacin rai a idanunsa yana girgiza kai yace "Shikenan yanzu zamu koma kici abinci after school zan nemeku dukan ku sai nasan yadda za'ayi" da "Toh" na answer masa sannan na bishi muka shiga parlour.
Lokacin da muka shiga kusan dukansu sun gama wasu sun shiga shiryawa wasu kuma sun shirya ana jiran Hamma,da sauri nima na shige ɗakinmu don ƙarasa shiryawa a nan naga Sajeeda a jikin drawer kayanmu da alama daga wanka ta fito,tana ganin na nufo gurin kuwa ta ƙara haɗe rai ta bar gurin,bata bani damar yi mata magana ba nima kuma ban wani damu ba saboda Hamma yace zai mata magana ga kuma rashin lokaci.
Kusan a tare muka fito da Hamma duk muka shige motar yaja muka tafi.
Ina zuwa department Ni'ima na nema tunda handbag ɗina na gurinta na kuyi yi sa'a ta ƙaraso har tamin reserving seat,na zauna ina kallon paper dake gabanta tana solving wani problem a statistics,ture paper tayi sannan ta ɗago min handbag ɗin ta ajiye kan seat ɗin tace "Ga ajiyarki nasha nauyi,yawwa ya jikin Saj jiya naso ƙarasowa da muka tashi,Allah be nufa ba",na ɗauki jakar sannan na zauna ina cewa "Thanks Lazy girl,Saj taji sauƙi dama headache ne" "Allah ya sawwaƙe" tace kafin ta ɗora da "Nikam na kasa solving problem ɗin nan ɗan duba min please" na ɗauki paper ina dubawa kafin nace "Kizo dai mu haɗa ƙarfi da ƙarfe muyi solving kinsan fa nima ba wani gane course ɗin nake ba nida kullum bacci nake in anayi", tayi dariya tace "To ai ke naki me sauƙi ne tunda in an koya miki kina ganewa,jiya jiya fa Hamma Sageer ya koya min amma kinga na manta" da mamaki nake kallonta jin sunan data ambata kafin nace "Wait,wani Hamma Sageer ɗin wai?" ta yimin hararar wasa kafin tace "Wanda kika sani" daga haka ta ɗauke kai,sai na juyo da fuskarta with over excitement nace "For real? dama wai Hamma Sageer ɗin nawa ne ake cewa Ɗan gayu ban sani ba?", tace "To saura ki faɗa masa na gaya miki kindai san halinsa" da murnata sosai nace "Kai inawa Hamma Murna ya samu mace ta gari dole ma Saj taji labari", sunan Sajeedar dana kira ya dawo min da yanayin da muke ciki sabo sai na tsinci kaina da jin ba daɗi duk farin cikin da nakewa Hamma na samun Ni'ima sai yayi fading a zuciyata amma ban bari ta gani a fuskana ba.
Mayar da hankalina nayi kan paper trying to solve the problem haka mukayi ta bugawa muna cancelling amma muka kasa solving,ganin muna ɓatawa kanmu lokaci Ni'ima tace "Kinga tashi zamuyi muje a koya mana ina da wani friend ɗan level 400 ba dai kai ba,Braniac suke ce masa a class ɗinsu", tunda nasan sai 10:00am muke da Class shiyasa ba tare da damuwar komai ba na tashi na bita.
Sai da muka fita sannan Ni'iman ta fito da Visafone ɗinta ta fara neman number Braniac,be wani daɗe yana ringing ba kuma ya ɗauka ta masa bayanin abinda zeyi mana sannan yayi mata describing inda zamu same shi.
Tunda muka doso dandazon mazan dake zaune kan round ɗin da aka cika da shuke-shuke naji gabana na faɗuwa sosai,Allah yasan ina tsoron maza don haka ja nayi na cake,Ni'ima ta juyo tana kallona kafin tace "Kinga matsalar ki ko?ba cinyeki zasuyi ba kowa fa harkar gabansa yake,can't you see Hajiya zabuwa?" ina hararta nace "Nidai kawai ki kirawo shi ko na koma in kin koya kya koya min". Ba ta ƙara cewa komai ba ta kirashi.
Tunda ya fara saukowa daga stair's nake kallonsa he look's familiar, "ƙila friend ɗin Bassam ne" na faɗa a raina don shine ɗan gayun dake friendship da haɗaɗɗun ƴan gayu kaf gidanmu. Bansan ya ƙaraso inda muke ba sai da naji Ni'ima na taɓoni,na juya da sauri na kalleta sai kuma naji kunya na sunkuyar da kaina nabi bayansu zuwa ƙasan stairs muka zauna kan tabarmar dake gurin,gaida shi nayi still not looking at him kafin itama ta gaidashi sannan ta miƙa mishi paper.
A hankali yake koya mana ta yadda dukanmu zamuyi understanding,sai da ya gama sannan ya ɗago yana kallona yace "Kin gane kuwa?" nayi masa nodding,unexpectedly naji yace "To yimin solving a nan na gani" ya ƙarasa yana juyo bayan paper,sai da na karɓi biro naga ashe sam bangane komai ba. Ya karɓi biro a hannuna sannan yace "Your mind wasn't with me when i was solving the problem how can i expect you to understand dama?anyway, ki bani hankalinki yanzu class ne dani ina so in tafi" naji kamar na mare shi don munzo ya koya mana abu shine zai fara min kallon daƙiƙiya, sai na cije na zubawa paper idanu,sau biyu ya ƙara maimaitawa kafin ya bani nayi solving dai-dai.
Yana kallona yace "Zan baki wasu exercise kije gida kiyi me tsoron dare,ranar ko ya kika isa gida?" sai a nan gane ashe ba abokin Bassam bane guy ɗin dana haɗu dashi ranar da Bassam ya saukeni ne ya bani lift zuwa gate,sai nayi murmushi nace "Lafiya ƙalau,nagode sosai sosai". Ni'ima dake ta kallonmu tace "Ashe kunsan junanku?" nace "Shine me kirkin dana baki labari ya bani lift sannan ya jirani na samu mota kafin ya tafi", Ni'ima tayi murmushi tace "Bayan kyau da kirki da kikayita lissafa min shi ɗin ɗan Msiduguri ne,your dream land" ganin ta fara min ɓaranɓarama yasa na buge hannunta dake kusa da nawa ashe ya gani sai yace "Meye na dukanta kuma don tana bani labari?", miƙewa Ni'imar tayi kafin tace "Sadeeq,meet my best friend Shukrah....Shukrah meet my Maiduguri friend Sadeeq ko kice masa Braniac" daga haka ta juya tana cewa "Kar zaman man ya tashi sai da positive result" na bita da kallon mamaki har ta ɓace min kafin na dawo da kallona kansa to my greatest suprise he's smiling,na fara ƙoƙarin miƙewa sai naji yace "Rabu da ita zata mana iyayi abunda ma ba ita ta haɗamu ba,Allah ne ya haɗamu tun last week".
Samun kaina nayi da komawa position ɗina nayi ƙasa da kaina,tambayoyi Sadeeq ya dinga min jefi-jefi ni kuma ina bashi answer wanda ya dace wanda kuma naga basa buƙatar answer sai nayi shiru,a haka alarm ɗina ya buga 9:40am sai na miƙe ina cewa "10:00am nake da class" tashin shima yayi kafin yace "Same with me,but please can i've your digits?", kamar wanda yamin wani abu haka na karɓi wayarsa na saka masa sannan kowa yayi hanyar Class ɗinsu.



Shukrah.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now