NEW BABY ALERT.

35 9 8
                                    

SHUKRAH.




Na
Zainab Yakasai (Shukrah).



Is your sister, cousin or friend getting hitched? Okay! you don't have to waste your time thinking of what to give as your contribution.
@sou.venirsbyshukrah is always ready to work with your budget for you to make your love ones feel special on their memorable day.
  Connect with us on Facebook and Instagram @sou.venirsbyshukrah.
Or send a message on WhatsApp to 09028979356 now.



Page 27.

NEW BABY ALERT.



Har aka kwana uku Mahdi bezo gidan ba ballantana musan me result ɗin test ɗin da aka min yace duk da ma nafi tunanin malaria ne tunda ranar da Umma ta rasu sauro ya cijeni sosai,  tunanin malaria ne kuma yasa na kwantar da hankalina da tunanin da naji ya gifta min a rai sai kuma nayi saurin cewa "God forbid" a fili sannan na miƙe daga zaman da nake tun safe a ɗakin Daada na wuce side ɗin Aunty inda aka sauke Neneh.
Ina fita parlor naga Daada, Baba Ali, Baba Umaru (mijin Yakumbo Mero) da Baffa a zaune suna ɗan tattaunawa aiko na ƙaraso a hankali cike da rashin ƙwarin jiki na durƙusa na gaidasu duka suka answer min cike da kulawa da kuma tausayawa suka kuma dinga jero min sannu har sai da sukaga wucewa ta.
Ko da na shiga Neneh na zaune kan carpet tana ninke kayanta tana zuba cikin jaka, na isa na zauna kusa da ita haɗe da ɗora kaina a shoulder ɗinta cike da shagwaɓa nace "Neneh! shine ko kizo ki ganni yau ko?", ta ajiye hijabin da take ninkewa sannan tana patting shoulder na tace "Na shiga kai miki magani ai kina bacci da yake shirin komawa nake sai ban samu dawowa ba, ya jikin naki?", na ɗago da sauri don banyi tunanin tafiyarsu a kusa ba sai na marairaice kuma idanuwana har sun fara tara kwalla nace "Neneh meyasa zaku tafi yanzu? karki tafi please ki bar Baffa ya wuce, ke fa nake gani nake jin daɗi in kin tafi ya zanyi?", ta ƙara hugging ɗina tightly kafin tace "Allah zai kawo miki mafita tafiya kuma ta zama dole tunda ba zamu dawwama a haka ba kema yau zaki wuce gidan mijinki", sai na sakar mata kukan da yake cimin rai nace ina yarfe hannayena "Neneh Dan Allah kisa baki Daada ya barni na zauna anan, nasan in kinyi magana zai yarda yanzu saboda yana tausayina tunda Ummana ta rasu", Neneh ta ɗan ɓata fuska sannan cike da faɗa tace "Bana son shashanci kinji ko? gidan mijin naki ne bazaki koma ba? aure abun wasa ne wai? to ki buɗe kunnuwanki dakyau ki jini ko shi mahaifin naki bashida hurumi ko iko dake a halin yanzu gwara ma ki maida hankali" tana kaiwa nan ta cigaba da ninkin da take ni kuma na kwanta a gefenta ina cigaba da kukana a raina ina tunanin shikenan ni ba wanda yake sona tunda sun kasa fahimta ta.
Har ta gama abinda take ina yadda nake ban kuma fasa kukan da nake ba, sai kuma taji tausayina aranta tabbas tasan ba a kyauta min ba da aka tilasta min na auri Mahdi amma ba yadda zatayi tasa Daada ya raba auren musamman ma a wannan gaɓar, to ai wadda ma ta haɗa ta riga ta raba ni kaɗaice a tsakaninsu kuma tunda be fasa lokacin Umma tana raye ba yanzu ma ba abinda zai ya fasa.
Sai ta ɗagoni ta rungume sannan cike da kulawa tace "Kina jina Shukrah? ki iya maraicinki kar naji kinyi musu da mijinki ko mahaifinki in ance ki koma, bakida kowa a kusa sai su mu idan muka koma ba zaki ganmu nan kusa ba wataƙila ma rai yayi halinsa kafin mu ƙara haɗuwa, tunda kikaga anja mahaifinki yaƙi saki akan auren nan to wataƙila akwai wani alkhairi a tattare da auren, kiyi haƙuri kici jarrabawarki", tunda ta fara nake jinta ina digesting maganganunta trying hard not to believe her though i know right she's telling me nothing but the truth amma bazan iya haƙurin da kowa yake so nayi ba, da ace Sajeeda bata ratsa lamarin nan ba, da auren Mahdi beyi silar rasuwar ƴar uwata da nafi ƙauna ba, da Ummana bata mutu da baƙin cikin auren da aka min da Mahdi ba, da kan gidanmu be tarwatse saboda Mahdi ba, da tabbas zan haƙura na rungumi auren nan amma waɗancan dalilan da suka yiwa aurenmu zobe ne sukasa bazan taɓa iya accepting Mahdi ba, never! zan dai cigaba da zaman biyayyar mahaifina a gidansa.
   Jin nayi shiru alamar bazance komai ba sai ta shiga goge min hawaye tana cigaba da min nasiha har Aunty ta shigo da sallama amma ganin yanayin da muke sai tayi murmushi ta juya tana cewa "Kuyi haƙuri bansan kuna magana bane", sai Neneh tayi murmushin itama tana cewa "Haba Haba ki shigo mana, ba wata magana muke ba nasiha nake mata", Aunty ta shigo tana kallona kafin tace "Dama Mijinta ne yazo Daada yace ayi mata magana su wuce", Neneh ta kalleni ni kuma na kasa haɗa idanuwa da ita don har a lokacin kukan da ta hanani nake, sai tace "Gata nan", daga haka ta umarceni dana saka hijab ɗina su Safiyya zasu kai min kayana daga baya, haka kuwa ba don raina yaso ba nayi yadda tace sannan nabi bayan Aunty muka fita zuwa parlor inda Daada, Baffa da Mahdi suke.
Sai da Baffa yayi mana nasihohi masu ratsa jiki sannan muka shiga muka yiwa Neneh sallama itama tayi mana addu'o'i sannan muka fito muka wuce.


SHUKRAHDove le storie prendono vita. Scoprilo ora