THE TRAGEDY III

27 3 2
                                    

SHUKRAH.

Na
Zainab Yakasai(Shukrah).

Hi guys! hope you're enjoying every chapter,is the story interesting? do you've any suggestion,complain or advice about this novel? okay my DM is alway open for you,feel free to reach me out on WhatsApp through 09028979356 or on Wattpad at ZainabYakasai.

Page 18.


THE TRAGEDY III(Still a throwback).


Gajiya mukayi da tsayuwa Umma ta jani zuwa room ɗinta ta kwantar dani akan bed har lokacin ina riƙe da kaina dake juya min, ganin ta juya zuwa kujerar dake gefen gadon ta zauna sai na daure na tashi zaune kafin nace "Umma me nayi musu suke son kashe ni? kinji me Hajiya tace kuwa? meyasa Daada bazai fahimce ni ya tausaya min ba?", Murmushin takaici Umma tayi tana kallon gefe kafin tace "Ke ai kinfi kowa sanin waye Daada he's a man of his words baya taɓa canja magana amma ina tsoron makomarki don haka na yanke hukuncin gobe zamu wuce Niger na samu Baffa ko zai yi masa magana".
Na ƙura mata idanuna a zuciyata ina lissafin halayen Daada yana da kirki,tausayi da kawaici amma yana da kafiya akan abinda ya tsara no matter the ups and downs,no matter the circumstances Daada baya canja magana sai kawai na hasaso rashin nasara a zuwan mu Niger gurin Baffa don haka na daure nace "Umma kina ganin Daada ba zaiyi fushi ba idan muka haɗa shi da Baffa?", ta kuma murmushin da nasan iyakarsa lips ɗinta sannan tace "Ko yayi ma zai sauko daga baya", nayi nodding kawai kafin na koma na kwanta.
  Shiru ya ɗan ratsa tsakani kafin naji tace "Ki samu kiyi bacci da daddare sai kije ki haɗa kayanki ko set 3 ne don da Asuba nake son mu wuce saboda bana so kowa yayi noticing fitar mu, da "Toh" na answer ta kafin na lumshe idanuna ina addu'ar bacci ya ziyarceni ko zan samu na manta da wasu damuwoyin nawa amma sai baccin ya bawa tunani damar ziyartata a wannan lokacin.

Washe gari Bassam yana fitowa daga masallacin Asuba yazo yayi knocking room ɗin Umma,ta miƙe tana tambayar waye kafin ta buɗe jin shine. Yayi ƙasa da kansa ya gaisheta sannan ya ɗora da "Umma! na fitar da motar can bayan gida sannan na buɗe ƙofar baya kamar yadda kika tsara sai ku tawo mu tafi", tayi murmushi sannan tace "Sannu da ƙoƙari,ga travelling bag ɗin can ka tayani kaiwa motar" ta ƙarashe tana masa pointing jakar kayanmu sannan ta juyo tana kallon yadda nake shan tea data tilasta min sha kafin tace "Ke kuma kiyi sauri bamuda lokaci", sai nayi sauri na ajiye cup ɗin don dama ba daɗi yake min ba kawai gudun faɗanta nake nace "Na ƙoshi Umma muje" ina kaiwa nan dama na ɗauki folded Hijab ɗina na fara warwarewa ina ƙoƙarin sakawa.
Sai da ta ɗauki jakar hannunta sannan ta kalli biscuit ɗin dake kan table da ko buɗewa banyi ba tace "Sai ki ɗauko Biscuit ɗin zai miki amfani a hanya", daga haka kuma ta fita nima na rufa mata ƙofa bayan nayi yadda tace.

Sanda muka isa park munyi sa'ar samun motar data kusa gama load don muna shiga bamu wani daɗe ba ta cika kuma sai a sannan Bassam ya tafi, throught out the journey dama ba wanda yacewa ɗan uwansa wani abu tsakanin ni da Umma don ni lissafin ƙaddarorina nake yayinda ita Umma take ta jan ƙaramin carbin dake hannunta.
  Sai ana kiraye kirayen sallat isha muka isa gidan, Neneh dake zaune kan sallaya a tsakar gidan da alama tunda ta sallaci Magrib take zaune ta dafe haɓa da mamaki tana kallonmu, sai kuma ta taso da sauri tana tafe hannu tana cewa "Lale marhabun da manyan baƙi, Shukrah kinga yadda kika ƙara girma kuwa?" ta ƙarashe tana rungumoni ni kuwa murmushin jin daɗi nayi na rungumeta nima ina jin yadda farin cikin ganinta ya goge kusan 40% na damuwar da nake tattare da ita.
Dama ita Umma muna shigowa ta isa toilet ta ɗauro alwala sai muka rankaya ɗakin Nenen na ajiye mana jakar kayan yayinda Umma ta tada iƙama nima sai na fita ɗauro alwalar.
Lokacin da muka idar Nene ta cika mana gabanmu da fura da cikwui har da mazarƙwaila sai a sannan ta zauna tana cewa "Irin wannan zuwan bazata haka?bakwa kiran Ja'afar (Cousin ɗin Umma dake kusa da gidan) kuce ya sanar kuna hanya?", Umma ta gyara zama ta ɗauki cikwui ta gutsira kafin tace "Ayi haƙuri Nene tafiyar ce ta taso gadan gadan ba shiri muka kamo hanya", Nene tayi shiru tana examining fuskar Umman da baka iya gane yanayinta indai ba sabawa kayi da ita ba saboda juriyarta, sai Nenen tace  "Wani abune ya faru a gidan naku?", Umma ta kalleni taga nima ita nake kallo sai ta ɗauki kofin da Nene ta kawo tayi amfani da ludayi ta ɗebo fura ta zuba sai da ta sha sannan ta ajiye cup ɗin tana sauke ajiyar zuciya, ta ƙara gyara zamanta wannan karon miƙe ƙafafuwanta tayi saboda gajiyar da tayi sannan kamar ana mata dole tace "Nene ina Baffa?".
Nene tayi murmushi ta ɗauki hand fan irin na kabar nan tana mana firfita kasancewar garin ya ɗanyi zafi kafin tace "Zuwan na Baffa ne kenan?", Umma ta sunkuyar da kai not ready to talk, sai Nene ta ɗora da "To Baffa dai sunje can Zinder anyi rasuwa amma muna sa ran ganinsa gobe ko jibi tunda yau me rasuwar yayi kwana uku", Umma ta jingina da gadon ƙarfen dake ɗakin kafin tace "Allah ya jiƙan musulmi ya dawo da Baffan lafiya", da "Ameen" Nene ta answer sannan bayan ta dawo da kallonta kaina tace "Ke kuma gajiyar hanyarce ta ramar dake haka ko kuma dai bakya cin abinci?", na ɗora kaina a kafaɗarta nace "Gajiyarce dai Nene".
Ta ɗanyi jim kafin ta tureni tana cewa "Ɗaga ni sarkin son jiki karki karyani bari na samu naje na kawo muku abinci, burabusko mukayi kin iya ci dai ko?", na ɗan ɓata rai bayan na tashi a jikinta don ban iya cin abun ba sai nace "Nidai ban iya ci ba Nene furar ta isheni" komawa tayi ta zauna tana kallon Umma tace "Hala dai yarinyar nan zaɓe zaɓen abinci kike bari tanayi don sangarta, gashi nan ai kullum sai ƙarewa take kamar kuɗin guzuri,haba yanzu ace burabuskon ne bazata ci ba?" Umma ta kalleni ta taɓe baki sannan tace "Nene ki kawo zataci", sai  Nenen ta tashi ta fita tana cigaba da mitar ta tana ta yarfe hannaye.
  Umma ganin Nenen ta fita sai ta dawo da idanunta kaina tace "Ki nutsu kina jina ko? ki barni naji da damuwa ta, nan ba kamar can gidanku bane ba kome aka baki ki karɓa kici", na kalleta kawai amma ganin yanayinta sai bance komai ba na cigaba da shan fura ta a hankali don har yanzu ba wai ina jin daɗin bakina bane.
Sanda Nene ta shigo sai
ta ajiye min faranti da kilishi sannan ta ƙarasa kusa da Umma ta ajiye mata farantin burabuskon.

Washe gari da Sassafe sai ga Baffa ya dawo, yayi matuƙar farin ciki kuwa da ganinmu don kusan shekarar mu biyu rabon mu da zuwa Niger su kuma tunda tsufa yazo musu dama suka haƙura da zuwa Nigeria, dan danan yace a yanka mana Zabin da yazo dasu a soya.
Sai bayan sallar la'asar muka samu zama gaba ɗaya da Baffa muna shan mazaiƙwaila da aka zuba a faranti, Nene ta kalli Baffa cike da girmamawa tace "Baffa, Faɗimatu fa gurinka tazo", sai Baffan ya dawo da dubansa kan Umma yace "Faɗimatu, ince dai lafiya ko?" Umma kamar zatayi kuka ta girgiza masa kai, sai ya ƙara fuskantar ta da alamar ya shiga tashin hankali yace "Subhanallahi, baki taɓa kawo ƙara ba duk tsawo shekarun nan ina tsoron kar kice min da me gidan kuka samu matsala".
Gyara zama Umma tayi ta kwashe labarin duk abinda ke faruwa ta gayawa Baffa, tunda ta fara dama yake girgiza kai alamar alhini.
Tana idarwa kuma yace "Ashsha,Shi Modun ne yayi wannan ɗanyen hukuncin?", Umma ta karyar da kai sannan tace "Wallahi Baffa munyi iya kacin ƙoƙarinmu mu shawo kansa amma yaƙi,abokiyar zamana bakaga fushin da tayi ba tunda ƴarta tana can kwance kamar ba zatayi ba amma shi ya kafe yace gidansa ne yadda ya tsara haka za'ayi".
Jinjina kai kawai Baffa yayi don ya yiwa Daada farin sanin,to surukutar shekaru Ashirin da ɗoriya ai ba wasa bace,kamar ba zai sake cewa komai ba can kuma sai yace "Handset ɗinki tana kusa ki kira min shi naji dalilin shi na yanke ɗanyen hukuncin da yayi?" Umma ta gyaɗa kai tana ƙoƙarin nemo number cikin wayarta dake hannunta.

Kira kusan uku Umma tayi masa kafin ya ɗaga da faɗan shi yace "Ina kika ɗauke min yarinya kika kai?", ta kalli Baffa da yake gyaɗa mata kai alamar tace tana tare dasu sannan tace "Dama Niger muka tafi, ga Baffa ma yana son maka magana", tana kaiwa nan ta miƙawa Baffa wayar ya karɓa tare da yin sallama, sai Daada ya sassauta muryarsa yana cewa "Allah seini,Ina wunin mu,yasu Nene da aiyuka?", Baffa ya kallemu sannan yace "Dukansu suna nan ƙalau,naji abinda kake shirin aikatawa haba Muhammadu shekaru fa sun jaa amma ace har yanzu ba zaka daina kafewa kan magana ɗaya ba?", yayi shiru yana jiran answer Daada amma jin shirun yayi yawa kuma yasan Daadan yana jinsa maganar ce ba zaiyi ba sai ya ɗora da "Me zai hana idan ma ba zaka aura masa ƴar uwarta ta ba ka haƙura da aura masa Shukrahn tunda ba sonsa take ba?", sai anan Daada yayi gyaran murya kamar ana tilasta masa magana yace "Allah seini, a gafarce ni amma shirye -shirye sunyi nisa bazan iya canja magana wa magabatan yaron ba,kuma naga abinda nake ƙoƙarin yi ma ai addini bai haramta min ba hasalima mu aka bawa damar zaɓar wa ƴaƴayenmu mazajen fari, ayi haƙuri dai ayi daga baya za'a ga alfanun abun", Baffa yayi murmushin takaici kafin yace "Me hali dai baya sake halinsa, Muhammadu nima fa bance ba dai-dai kake ba ina dai gudun abinda zai je yazo ne kasan fa damu da yaran nan ba ɗaya ba tunda zamanin ma ba ɗaya bane", Daada yace "Baffa! ba abinda zai je yazo nafa isa da gidana", Baffa ya jingina da kujerar da yake yana shafa kansa kamar bazai ƙara cewa komai ba har sai da Daadan yace "Allah seini, a sanya musu albarka nan da sati me zuwa na tsayar za a ɗaura auren tunda abubuwa sunzo a haka".
Bansan na miƙe tsaye ba sai da naji ni timmm na faɗi ƙasa,ba suma nayi ba tunda ina jin Umma da Nene sunyo kaina da sauri suna salati sai da suka ɗagoni sannan na saki wani irin kuka me cin rai na ƙanƙame Nene cike da tashin hankali nace "Nene! Mutuwa zanyi ku yafe min", sai ta rufe min baki harda ƴar kwallarta tana cewa "Ba zaki mutu ba,kiyi haƙuri kiyi masa biyayya zakiga alfanun abun" nayi shiru na mayar da hankalina kan Baffa da har yanzu yake waya da Daada amma bana iya jin me yake cewa,a hankali kuma sai naji jikina yayi sanyi idanuwa kuma sai suka rufe gaba ɗaya.






Shukrah!.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now