MY IN-LAWS (Still a throwback)

29 5 5
                                    

SHUKRAH

Na
Zainab Yakasai (Shukrah).




Are you or your friend getting hitched this month? are you thinking of what to share as a souvenir? let me work with your budget for you to put a smile on your love ones faces.
I'll really appreciate you if you make me your first contact.
Call or send me a message on WhatsApp  today @09028979356.
Connect with me on facebook and Instagram @ Sou.venirsbyshukrah


Page 24.

MY IN-LAWS.

Har Asuba ba abinda
nake in banda kuka, Mahdi ya zalunceni ya rabani da pride ɗina bayan yasan bana sonsa.
What if ciki ya shiga? hakan fa yana nufin zan dauwama a gidansa, God forbid! nace da sauri bayan da tunanin yazo min, sai na miƙe da kyar ina kallon Mahdin dake ta sallolinsa ina jin kamar na caka masa wuƙa na huta haka naja ƙafata dakyar zuwa toilet na ƙara yin wanka nazo na saka jallabiyya na tayar da salla ina jin yadda jikina da zuciyata ke min zugi.
Koda na idar Al-qur'ani na ɗauka ina karatu ko zanji sanyi a raina,idanuwan Mahdi da nake ji na yawo a jikina ne yasani rufewa na miƙe haɗe da ɗauke praying mat ɗin ina ninkewa sai shima ya miƙe yana ƙoƙarin karɓa yace "Morning Wife", na watsa masa harara kawai ina ƙoƙarin danne zuciyata don kar inzo inyi abinda zanyi regretting daga baya shima ganin bazan answer shi ba sai naga ya fice daga room ɗin ya sauka downstairs sannan naji ya buɗe entrance door ya fita,na taɓe baki kawai na zauna haɗe da ɗora hannayena biyu akaina na fashe da kukan da ya zame min jiki,a ƙasan raina ina roƙon Allah ya ɗauki raina na huta da abubuwan dake faruwa dani kullum.
Gajiyar da nayi da kukan ne yasa na miƙe ina tafiya a hankali na ƙarasa jikin drawer na na fito da ƙaramin first aid box ɗina na ɓalla pain reliever sannan na sauka ƙasa na kora da ruwa nayi zamana a nan parlor. Bansan tsawon lokacin dana ɗauka a gurin ina tunane tunane ba sai naji tsayawar mota, ko motsi banyi ba bare nayi ƙoƙarin tashi naje na buɗe ƙofa jin ana knocking sanin Mahdi ne, yau sai dai ya kwana a tsaye a gurin shine punishment ɗinsa.
Zuwa can naji ana cewa "Wai masu gidan basa nan ne? Mahdi, Mahdi?", sai na miƙe jin mace ce ke magana na ƙarasa ina jan ƙafata da tayi tsami naje na buɗe amma me ina buɗewa matar da ban sani ba ta watsa min harara tana cewa "Wani irin shashanci ne wannan zaku bar mutum yana ta knocking haka, ina Mahdin?", tana kaiwa nan ta raɓani ta shige parlor tana ƙarewa ko'ina kallo nima na bita cike da mamakin ƙarfin halinta.
Sai da ta zauna ta ƙara maimaita tambayar ta sannan nace "Bansan inda yaje ba", sai ta saki baki tana cewa "Ashe da gaske ne abinda ake faɗa Mahdi wadda bata sonsa ya aura, yanzu ƴar nan sai kice min baki san inda mijinki yaje ba da sassafen nan?" na ɗan yi mata shiru kafin na miƙe ina cewa "Bari na haɗa miki breakfast", ko da ban santa ba kamaninta sun nuna min ita ɗin ƴar uwar Mahdi ce, "A'a da kin barshi ma" naji tace.
Turo ƙofar da akayi ne ya hanani bata answer ina kuma ɗaga idanuwana na saukesu cikin na Mahdin dake ta min murmushi, sai na kawar da kai ganin irin kallon da matar take mana anan kuma Mahdi ya kula da ita don haka da sauri ya ƙaraso ya ajiye ledar dake hannunsa kan center table ya durƙusa yana cewa "Adda Manga kece haka da sassafe? kin tashi lafiya?", taja tsaki tana harararsa kafin tace "Dole ka tambayeni nice da sassafe mana, dubeka Dan Allah duk kabi ka lalace ka zama bawan mace, shiyasa baka zuwa gurin mu don kar mu gaya maka gaskiya ko?", jin yayi shiru kansa a ƙasa sai ta ɗago tana min wani irin kallo kafin ta nuna ledar daya ajiye tace "Saboda ka auri ƴar gold shine ba zata dinga maka girki ba sai ka siyo mata abinci tana zaune tana izza ko?", muryarsa a matuƙar sanyaye cike da ladabi yace "Ba haka bane Adda am, bata ji daɗi bane".
Sai ta kalleni dai-dai lokacin da nake zama a ƙasan carpet don ƙaƙafuwa na sun gaji tace "Amma ke ba ƴar arziƙi bace, ki dinga wahalar da yaro ji yadda ya koma fa", wani murmushin takaici ne ya suɓuce min kafin na kalleta ina jin bazan iya cigaba da danne zuciyata ba nace "Dan Allah kisa ya sakeni kowa ya huta", ba ita ba hatta shi sai da yaji shock don a tare suka ɗago suna kallona, sai kuma ta mayar da idanuwanta kansa tace "Kaji ko? indai na isa dakai a matsayina ta babbar yayarka ka saki yarinyar nan kafin ta kashe ka, ko baka ga ƙiyayyar ka a idanuwanta ba?", ya mayar da idanuwansa kanta da sauri muryarsa har rawa take yace "Adda, ba abinda kike tunani bane mun ɗan samu saɓani ne shiyasa tace haka", a tsawace tace "Ni zaka rainawa hankali? a tunaninka bansan komai bane? nifa tun asali dama ba ƙaunar auren nan naka nake ba shiyasa banyi attending ba, yarinyar ta tsaneka sai cusa mata kai kake bafa a dole".
Miƙewa Mahdin yayi yace "Adda, Don Allah kiyi haƙuri kije gida zanzo", ta kuwa miƙe tana cewa "Mahdi! gata nake maka me zaka cigaba da zama da yarinyar nan kayi? yarinyar da bata ganin danginka da daraja yau kusan wata tara da aurenku amma ko mahaifiyarka bata taɓa zuwa ta gaida ba", tana kaiwa nan ta nufi entrance shima ya miƙe ya bita yana cewa "Zata zo", nikam tsaki kawai naja na koma kan 3 sitter na kwanta ina jin ɓacin raina yana ninkuwa, lallai matar nan bata san saboda umarnin mahaifina nake zaune da ɗan uwanta ba take magana kamar yana min wani favor ne, meye ma haɗina da danginsa da zanje inda suke?.
Koda Adda Manga ta fita gidan Hajiyarsu ta koma tana ta huci kamar wadda ta dawo daga yaƙi ta samu Siyama sister ɗin Mahdi zaune a parlor tana kallo tace "Ke, Kinsan gidansu Matar Mahdi?", Siyama tayi murmushi tace "Munje ɗaurin auren can ai, me ya faru?", Addar ta kawar da tambayar ta hanyar cewa "Hajiya fa?" Siyama ta kalli bedroom ɗinta kafin tace "Tana ciki", sai Adda tayi ƙasa da murya tace "Kije ki ɗauko veil ɗinki silently ki sameni a mota daga haka ta fice tana jiranta, bayan kamar 2 minutes kuwa sai ga Siyamar ta shiga suka fice daga compound ɗin tana ma Addar kwatance har suka ƙarasa gidan Daada.
Dukan ƴan gidan suna zaune a parlor banda Hajiya da tunda Daada da Baba Ali sukayo bikonta ta mayar da zaman ɗaki kamar ibada in bata kama ba ba fitowa take ba tunda tana da toilet a room ɗinta, ko abinci ma room ɗin ake kai mata.
Can ciki sukayi sallama Daada ya ɗago daga karatun jaridar da yake ya answer sannan Aunty da Umma suka fara musu barka.
Dakyar suka zauna Addar tana hura hanci ta kalli Daada tace "Allah seini! gurinka nazo", ya fuskanceta yana cewa "Allah yasa lafiya", ta ƙara ɗaure fuska tace "Ƙalau,vdama zuwa nayi nasa kayiwa ƴarka magana tana wahalar mana da ɗan uwa bafa dole a auren nan", Gaban Umma ya faɗi don taga kamannin matar da Mahdi sai ta daure tace "Wace ƴar a ciki? kinsan ba ɗaya ya aurar ba", ta watsawa Umma wani kallo kafin tace "Matar Mahdi nake magana akai", Aunty ta mayar mata da irin kallon da take musu kafin tace "Me tayi to? go straight to the point and stop romancing words, my friend", Addar tace "Idan ɗanki yayi aure ya zakiji in surukar ta kwashe good nine months bata ta gaisheki ba?", Aunty ta taɓe baki kafin tace "Bansa aka ba", Addar tace "Ni nasa".
Aunty tayi dariya kafin tace "Hala ke kike haifeshi", sai Addar ta miƙe tana cewa "Kar ki gaya min magana", Daada ganin Aunty ma ta miƙe sai ya miƙe shima yana kallonta yace "Kefa ba haƙuri gareki ba yarinya tayi lefi an kawo ƙara sai ki nemi ki tada hayaniya?", Aunty was shocked don haka ta saki baki tana kallon Daada tace "Au hayaniyace ma wannan? naga ne Mahdin ba ɗanta bane meye nata na yin ƙorafi kuma?", Daada yace "What if she was sent by her mum?", "She should've say so sai mu fahimceta" Aunty tace tana harararta, Sai Umma ta ƙaraso gaban Addar tace "Baiwar Allah kuyi haƙuri za'ayi mata faɗa, insha Allah zata gyara", Addar dake ta harare harare tace "Kar ma ta gyara" tana faɗar haka ta riƙe hannun sister ta zasu fita.
From no where sai ga guɗa kowa ya mayar da idanuwansa side ɗin Hajiya don daga nan take fitowa, sai kuwa Hajiyar ta ƙaraso excitingly tana tafe hannayenta tace "Ai nasan za a rina, yarinyar da aka riga aka sangarta tun farko dama ai ba zatayi abun arziƙi baNrashin arziƙi ma yanzu kuka fara gani Hajiya", Umma ta kalleta da mamaki kafin tace "Falyaqul khairan auwhli yasmut", Hajiyar ta harareta tana cewa "Ke bana son iyayi da munafurci, ƙarya akayi bake kika sangarta ta ba kullum bakya nuna mata komai sai rashin kunya".
Ran Umma yayi matuƙar ɓaci don haka tace "Ashe kinsan rashin tarbiyya nake koyawa kika ɗauki Sajeeda kika bani na haɗa? kenan kema da rashin tarbiyyar tawa kike taƙama tunda kullum sai kinyi alfahari da ƴarki", sai Hajiya ta kawowa Umma damƙa tana cewa "Karki ƙara ambatar min sun ƴa mayya kawai", sai anan Daada da shock yasa yayi pausing ya motsa ya buge hannun Hajiya daga jikin Umma yana cewa "Wani irin shashanci ne wannan?" a tsawace, jin haka sai duka yaran dake wajen sum sum suka wuce ciki Daada kuma ya juya yana kallon Addar yace "Walk out" pointing at the door, da alama ita ma tsorata tayi da yanayinsa shiyasa taja sister ta suka fice da sauri.
Daada ya dawo da kallonsa kan matansa yana cewa "I'm sick and tired of everything going in this house, ku bazaku huta ba ne even for once?", Hajiya ta buɗe baki zatayi magana ya katseta ta hanyar cewa "Bana buƙatar jin komai daga bakinku, ku ɓace min daga gabana".
Tunda Umma ta shiga ɗaki take ta safa da marwa abubuwa sun taru sun yi mata yawa daga wannan sai wancan,bbatada plan ɗin zuwa gidan Shukrah a rayuwarta gaba ɗaya amma tana ganin zataje wannan karon tayi mata faɗa sosai don ta tsani abun magana, a da batayi faɗa da mutane ba bare yanzu don haka ba zata yarda akan Shukrah ta dinga faɗa da mutane ba.
Daada kuwa suna shiga dukansu ya ɗauki car key ɗinsa ya fito yau da kansa zeyi driving ɗin daya daɗe beyi ba.







Shukrah.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now