THE HEARTBREAK.

26 5 1
                                    

SHUKRAH.


Na
Zainab Yakasai(Shukrah).


Hi guys! hope you're enjoying every chapter,is the story interesting? do you've any suggestion,complain or advice about this novel? okay my DM is alway open for you,feel free to reach me out on WhatsApp through 09028979356 or on Wattpad at ZainabYakasai.

Page 14.

HEARTBREAK.
(Still a throwback).

After like two minute naji message tone ɗina aiko gabana yayi mummunar faɗuwa sai na dafe saitin zuciyata ina kiran sunan Allah, Sai da nayi sallar magrib nayi addu'ar Allah yasa duk abinda zan gani a message ɗin ya zame min alkhairi sannan jikina a sanyaye na ɗauko wayar na buɗe message ɗin daya min sending kamar haka
   "I don't know where to start but i know i felt pain after i read your message, I’m Sorry I don’t want to deceive you Zainab,Things are going deeper and I know my family won’t allow me to go to Kano and get a wife, If we continue it will get worse Idan mukazo rabuwa shiyasa na fara nesanta kaina dake,i wish you nothing but the very best life in future,Ma'assalam".
  Bansan yadda akayi wayar hannuna ta faɗi ba,bansan meya faru dani ba amma nasan bugun zuciyata sai da ya tafi hutun wani lokaci kuma banda karkarwa ba abinda duka jikina keyi gumi ya jiƙani jagaf daga inda nake a zaune kamar statue,Allah kaɗai yasan tsawan lokacin da na ɗauka a zaune cikin yanayin da na fi tunanin mutuwar zaune ne ko ince  suma ne.
Jin ihun Sajeeda ne ya sani buɗe idanuwana da bansan sanda suka rufe kuma na kwanta ba,Hajiya da Safiyya da suke parlor suka shigo da gudu suna cewa "Lafiya Sajeeda?" Sajeeda tana kuka kamar an aikota tace "Suma tayi" sai Hajiya ta ƙaraso da sauri ta ɗagoni sai kuma ta sakeni tana cewa "Innalillahi jikinta fa ya saki" na ƙara buɗe idanuna na motsa lips ɗina da suka min nauyi underneath my breath nace "Hajiya ki kira min Daada" sai naga ta rungumeni tana hamdala kafin ta aika Safiyya ta kira shi,sai a time ɗin Ummata da Aunty dasu Hamma suka shigo cikin tashin Hankali duk suka kewaye bed ɗin suna kallona,sanda Daada yazo bashi guri sukayi ya riƙeni yana cewa "Me ya faru?" na girgiza kai sai a lokacin kuka yazo min na kuwa fashe musu dashi a hankali na damƙe hannunsa dake cikin nawa nace "Daada mutuwa zanyi" ya rungumoni yace "Cuta ai bata kisa Mamana,yanzu zan kira Doctor yazo ya dubaki kinji" na girgiza kai ina jin tausayin zuciyata tunda dukansu tausayina suke a matsayin mara lafiya ba wadda akayi breaking heart nata ba,Aunty ce ta tafi kiran Doctor Usman wani maƙocin mu dake aiki a can AKTH.
kwantar dani Daada yayi kafin ya kallesu yace "Shikenan muje ta ɗan samu bacci kafin Dr. ya ƙaraso" daga haka suka fice suka sauke min curtain,na lumshe idanuna kawai don nasan ba yadda za'ayi bacci ya matso kusa dani a yanayin da nake.  

Lokacin da Dr. yazo yamin TPR&BP test hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba,ya kalleni sosai sannan yace "Bp ɗinki yayi is high meke damunki ne" maimakon na bashi answer sai kawai na fashe da kukan dake cina tunda ya shigo,calmly yace "Is okay,don't tell me now but please try to overcome what's hurting you inside,calm yourself down komai yayi zafi maganinsa Allah" nayi nodding kafin nace "Insha Allah,Thanks". Fita yayi parlor gurin Daada ya barni da Aunty da Hajiya,suna nan a zaune har Hamma Sageer yaje chemist ya siyomin drugs ya kawo aka bani bayan Aunty tayi forcing ɗina nasha tea.
Washe gari na samu sauƙin jikina amma banda na zuciyata don ji nake kamar pain ɗin yana multiplying with every breath i take,da yake semester yazo ƙarshe kuma week ɗin zamu fara test tuni na shirya muka wuce makaranta amma ko da na zauna a Class ban iya tsintar komai ba a five hours lecture da mukayi kuma dama nasan deceiving kaina nayi da nayi expecting tunani zai barni na gane,a daddafe na ƙarasa lecture ɗin ranar muka koma gida.
Ina ganin an pasting mana test timetable dama na fara ƙoƙarin cire tunani na mayar da hankalina kan karatu.
Ranar wednesday muka fara test da Genetics,ina karɓar paper na dama na mayar da hankali na fara answering questions ɗin da suka min mugun sauƙi ko don Sadeeq ya koya min sosai ne oho,sai da na tabbatar na gama sannan na ɗago kaina and my eye fall on Sadeeq that's standing by the window and i guess he's among the student's invigilators,gabana ya faɗi nayi saurin ɗauke kai ina jin kuka yana tawo min at the same time kuma ina jin kamar ana sawa ciwukan da ya jimin azuciyata ruwan gishiri,nafi ƙarfin 5mints kaina a ƙasa ban ma san anyi rounding up ba sai da wani invigilator yazo yaja paper na yana cewa "Zaman me kike tun ɗazu bakya rubuta komai har an gama" na ɗauke kai kafin nace "I'm sorry na gama ne" daga haka na miƙe na fice,instead of heading to Sajeeda's department kawai sai na tafi Bus stop na hau bus ɗin da take zuwa court road daga nan na hau taxi na koma gida.
Umma dake parlor ta biyoni ɗakin tana kallon yadda na kwanta ina kuka a tsawace tace "Ke! meye haka? ina Sajeedar?" na tashi da sauri sannan nace "Umma bana jin daɗi ne shiyasa na tawo" tace "To yayi kyau,ya kukayi da yaron" naji wannan faɗuwar gaban data zame min jiki sai kuma zuciyata tace in gaya mata gaskiya don ba amfani ɓoye-ɓoyen tunda at long last dai sai na faɗa matan don haka na gyara zama na faɗa mata duk yadda mukayi a message. I luckily sighted tausayina a idanunta da kwallar data cika mata su sai naji pieces ɗin da Sadeeq ya mayar min da zuciyata suna ƙara dagargajewa,kewar Sadeeq da ƙaunar mahaifiyata suka kanainayeni suna neman yimin illa,da kyar ta buɗe baki tace "Allah yasa haka ne yafi alkhairi keep calm kita addu'a komai zai zama history kinji" and from her words i felt relieved sai na rungumeta ina mata godiya,room ɗin yayi shiru na tsawon lokaci kafin ta janye tace "Sai ki faɗawa Daadan in ya dawo" na answer da "Toh" sannan ta fice ni kuma na koma na kwanta tare da lumshe idanuna kwallar dake cikinsu suka samu nasarar saukowa kan cheeks ɗina.

A daddafe na dinga rubuta test har aka gama sannan ranar friday da daddare Daada ya kirani parlorn sa,nasan akan Sadeeq da yace na kira zai tambayeni don haka jikina ba ƙwari na ƙarasa ina kallonsa,yana zaune da jarida a hannunsa gefensa kuma tea ne kan table ɗinsa. Sai da ya gama da page ɗin da yake sannan ya juyo yana kallona kafin yace "Fatima ta yimin bayanin komai Allah yasa hakan ya zame miki alkhairi a rayuwarki,ki daure ki cinye ƙaddararki kinji?" nayi nodding kawai don nasan in nace zanyi magana kuka zanyi,shima nasan fuskantar hakan ne ya sashi cemin "Shiga cikin ɗaki akwai zuma kan mirrow na ki ɗauka naki ne" nayi widening murmushina ina jin ƙaunarsa tana ƙara shigata don Daada kullum burinsa yamin abinda nake so,yasan ina son zuma shiyasa yake yawan min kyautar ta. Tun a room ɗin dama na buɗe na fara sha har na iso inda yake na zauna a gefensa har yanzu murmushina beyi fading ba nace "Daada,nagode sosai Allah ya faranta maka kamar yadda kake mana ya bamu ikon kyautata maka da yi maka biyayya" murmushin shima yayi sannan yace "Ameen,Allah ya miki albarka" na answer da "Ameen" sannan na fita.

Tun daga ranar kuma nayi ƙoƙarin cire Sadeeq daga raina though nasan ba iyawa zanyi ba amma ina trying wajen kawar da tunaninsa by keeping myself busy all the time,abun mamaki kuma ko a makaranta ban ƙara ganinsa ba kuma sai naji hakan be dameni ba. Ban gayawa Ni'ima munyi breakup ba don nasan zata iya cewa zata masa magana and yanzu kuma ni bana buƙatar sa a rayuwata not when he played with my intelligence,he left wounds that can never be heal in my heart don haka bana son wata taraiya ta ƙara haɗani dashi.
Ana cikin haka kuma exam's tazo na kuwa ƙara dagewa da karatuna,har muka gama exam bana ji na bar tunaninsa yayi galaba a kaina. Muna gama Exam's da sati ɗaya Daada da Cousins ɗinsa Baba Modibbo da Baba Ali sukaje tambayar auren Hamma Sageer gidansu Ni'ima sai na Hamma Giɗaɗo gidan Yayar Daada Yakumbo Mero,aka tsayar da wata biyu.
Da yake ance duk abinda aka sa masa lokaci sai yazo kamar wasa sai ga wata biyu sunzo,dama duk ɓangarorin suna ta shirye shiryensu don haka ranar Friday ɗin da magana ta cika wata biyu cif aka ɗaura musu aure bayan masallaci,asabar mukaje Kamu gidan Yakumbo Mero su Umma kuma sukaje gidansu Ni'ima,washe gari lahadi kuma akayi walima a gidanmu aka kai amare twins house ɗinsu dake Na'ibawa.
Bayan bikinsu Hamma da sati biyu kuma Adda Basma da bata samu zuwa ba saboda tsohon cikinta ta haifo mana yaro namiji,Daada yace bayason duk wasu al-adu da ba addini ne ya shari'anta ba don haka ba sai tazo gida ba Ni da Aunty muje mu zauna da ita,haka kuwa akayi mukaje kuma naga mijinta yaji daɗin decision ɗin Daadan.
Ranar suna Hamma Bassam yazo da wannan abokin nasa Hanif,aiko yana ɗora ido a kaina ya dinga bina yana majiyar na bashi lokaci ko contact nidai shiru nayi masa har sai da Adda Basma tasa baki sannan na bashi number kawai amma bawai don zan iya ƙara yin soyayya da wani ɗa namiji ba.






Shukrah.

SHUKRAHWhere stories live. Discover now