Part 29

188 5 0
                                    

*💫❤LOVE CYCLE✨*

Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......

Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (29)✨
Amoon ya wuce dakinsa ba tare daya kalli kowa dake cikin parlorn ba.. Yanda yake hadiyar zuciya a lokacin kamar wani mayunwacin zaki.. Yana shiga ya daki banko kofar da karfi yana nishi tare da cizgar lips dinsa.. "He's just hoping to see tomorrow dan yaga wane isashshen ne ze shigo cikin family din nan da sunan wanda ze auri Fannahr sa"... Ya runtse idanu yanajin yanda zuciyar sa ke wani irin bugawa.. Bude kofar akayi.. Ya daga jajayen idanun sa yana kallon sadeeq daya shigo.. Dauke kansa yayi ya cigaba da sauke ajiyar zuciya da karfi.. Kallo daya zaka masa kasan ransa yakai kololuwar baci .. Bude fridge sadeeq yayi ya dauki bottle water ya mikawa Amoon bayan ya bude... Karba Amoon yayi ya daga...ya shanye tass snn ya juya yana kallon sadeeq yace "inde har Fannah ta auri wani baniba, to mutuwa zanyi that's the end of me"... Sadeeq yace "stop saying that.. Inde Fannah har Fannah matarka ce wlh seka aure ta idan kau kaga baka aureta ba to ba matarka bace that's ur destiny".. Dan murmushi Amoon yayi wanda daga gani kasan he's boiling from inside yace "Abbakar bazaka gane ba Fannah is my hope she's my future".. Sadeeq yace "just keep praying and kayi hakuri nasan wnn duk kishi ne kesa wnn abun ko a yanayin condition dinka ai ka kwantar da hankalin ka..ni nasan sbd yanayin condition din yusrah suka matsa seka aureta sbd idan aka barta zata iya shiga wani hali tunda ba lafiya ta gama isarta ba.. Kuma kaga tunkan tasan kanta takesonka. And babu yanda za'ai a hana jiddah kuma tunda tun suna yara suke sonka".. Amoon yayi shiru bece komai ba amma yasan zuciyar sa bazata daukar ganin Fannah da wanin sa ba...
Fannah kam daki ta shiga tasha kukan ta fuskar Amoon kawai take hangowa tasan bashi cikin yanayi me dadi..
Bayan tafiyar su sultan akayi kiran su fareeda.. Nan take ya fada masu duk hukuncin da suka yanke.. Abbu ya kalli fareeda yace "maganar sultan ki barta ga sageer nan inshaallahu nasan bazaki samu matsala dashi ba".. Gyada masa kai fareeda tayi gaban ta na faduwa.. Sageer din da bawani shiri suke dashi ba mutumin da yakeda mugun jin kai amma shine za'a aura mata.. Haka nan de kawai ta Amince zata aure sa amma zuciyar ta bnd bugawa babu abinda take.. Ita tana da mugun tsoro shiyasa ko Amoon bata shige masa... Yusrah kam farin ciki sosai jin Friday za'ayi baikon su da Amoon duk da harda jiddah Amma de tana farin ciki... Jiddah kam jikin ta yayi mugun mata sanyi.. Taga a yanayin da Amoon ya fito daki dazu hakama na Fannah hakanan kawai se jikin ta yayi sanyi... Chucu kam duk da tana farin ciki sede tausayin yayan nata da Fannah ya rufe hakan.. She wish ace itace yusrah da Jiddah data hakura yau kodan sbd farin cikin su da yanda suke son junan su...
A ranar dayawa basuyi bacci ba cikin wadan da Abun ya shafa wasu farin ciki wasu kam kwana sukayi kuka irin su Fannah da fareeda.. Fareeda na ganin yanda sultan keta kiran ta da kuma tura messages.. yana bata hakuri da kuma rokonta akan dan Allah kartayi accepting sageer.. Babu amsar data basa.. Duk da tasan a lokacin can ita taja sultan ya barta amma dole itama ta share sa kamar yanda ya share ta wnn karon sbd fannah.. Kuma dukda tanasonsa dole tayi hakuri tunda Abbu ya hadata da sageer...
Fannah kam taci kuka harta gode Allah chucu ce me lallashin ta... Amoon ya tura mata message amma bata duba ba bama tason dubawa sbd tanaso tabi umarnin iyayenta...
Washe gari kamar yanda Abbu yace sageer yazo ya samu fareeda.. Itade ta gamajin abinda ya fada mata a matsayin wanda ke sonta ko daya bama tajin zata fara sonsa.. Sultan kau kamar zeyi hauka sharesa tayi ta nuna kamar ma bata san yanayi ba ...
Can bayan la'asar Abbu yayi kiran Fannah... A hanyar ta ta zuwa ta hadu da Amoon dauke kai tayi zata wuce.. Yace "dama idan kika je kinuna beyi maki ba"... dan kallon sa tayi taga bama ita yake kallo ba ta dauke kai tayi wucewar ta.. Parlorn Abbu ta shiga ta same sa bayan ta gaisar dashi ya amsa ya danyi mata nasiha tare da fada mata ribar hakuri snn ya nuna mata parlon da yake ciki .. A hankali ta tashi ta shiga jikin ta duk a sanyaye tayi sallama ya amsa mata kanta kasa ta zauna.. Ta gaisar dashi ba tare data dago ba .. Ya amsa snn yace "khadeeja".. Dan dagowa tayi ta kallesa.. Shima matashi kamar su Amoon din duk wani abu daza'a soshi ya mallaka sede ina batajin zata iya son wani bayan Amoon duk maganganun da yake bama tajinsa.. Tade ji sunan sa Yusuf. Amma nan har ya gama surutun sa ba jinsa take ba..
itade seda yace ze tafi zuwa gobe ze dawo snn ta dago ta kallesa murmushi tayi snn tayi masa sallama.. Parlorn Abbu ta wuce ta yace "ya tafi mamana".. Ta gyada masa kai.. Yace "masha Allah ya kukayi dashi".. Tace "na amince Abbu".. Murmushi Abbu yayi "Allah ya maki Albarka" a sanyaye tace "Ameen".. Wnn karon bata iske Amoon ba se jiddah tare da farouq.. Babu wanda ta tankawa a cikin su ta shege daki sbd kukan dake cinta...
Yusuf yazo ze shiga mota knn aka yi masa sallama ya juyo yana kallon Amoon da murmushi ya mika masa hannu suka gaisa... fuskar Amoon babu yabo ba fallasa yace "nasan neman aure kazo ko".. yusuf na murmushi yace "sure khadeeja".. Amoon ya dake gira trying hard be fito da bacin ransa ba yace "advisibly kar ka kara zuwa imda sunan wajen ta kazo cos tanada miji".. Dan kallo sa yusuf yayi snn yace "but ni ba'a fadamun tanada miji ba".. Amoon yace "for ur on good kar na kara ganin ka da matata".. Daga haka ya juya yabar Yusuf daya bisa da kallo.. Can kuma ya shiga motar sa...
Fannah dake zaune jikin gado tana share yan hawayen ta ta daga ido ta dubi jiddah da farouq da suka shigo.. Dauke kai tayi ta cigaba da goge hawayen ta da sukaki tsaya mata... Jiddah ta zauna gefen ta farouq kuma ya tsaya jikin mirror yana kallon ta yace "jiddah is here to apologize".. Jiddah tace "kiyi hakuri for all what happened and still happening ina son yaya Amoon amma na hakura dashi because of you ke yake so bamu ba dan haka na hakura".. Ba tare da ta kalli jiddah ba tace "babu komai and maganar yaya Amoon kuma ni na hakura Abbu na hadani da wanda zan aura"... Jiddah ta dafa kafadar ta "Fannah nasan kina son Amoon and shima ke yake so.. Tunda nake bn tabajin yaya Amoon yace yanason wata ba se akanki nasan koda mun aure zuciyar sa na tare dake.. Ni ynx nayi wa yaya khaleefa magana and inshaallahu zuwa Friday zasu zo ayi mana baiko".. Fannah de batace komai ba sbd ita kade tasan yanda take ji... Mikewa jiddah tayi ganin Amoon fita sukayi farouq na bayan ta.. Duk da Fannah taji kamshin turaren sa Fannah bata dago ba.. Amoon ya karaso Yana kallon ta ganin yanda take kallon wani direction din yace "hope kin sallamesa".. Ba tare data kallesa ba tace "why will I do that bayan shine aka zabamun"..yace "aka zaba maki ai ba zabin kiba".. Ta juyo ta kallesa.. "Nima ynz zabi nane coz na riga na amince ma Abbu".. Amoon ya rinka kallon ta yace "look into my eyes and tell me kin amincema wani da aure bayan ni".. Kin yarda tayi ta kallesa.. Yace "khadeeja".. Fashe masa tayi da kuka "pls Aliyu let me ka kyale ni dan Allah na rokeka ka rabu dani".. Se kuma ta juya tana ta kuka sosai... Sosai ta basa tausayi amma yasan duk abinda take ji be kai rabin wanda yakeji ba ya fita damuwa..he wish ace ze iya yin kuka he wish yace ze iya rungume ta suyi kukan tare daganan su samawa juna solution. Juyawa yayi a hankali ya fita... Seda taji karan rufe kofa snn ta dago.. Se kuma ta juya taci gaba da kukan .. Dakin dad dinsa yaje.... Dad yasan maganar data kawo dan nasa shiyasa yayi saurin dakatar dashi.. "Aliyu kayi hakuri da hukuncin da Aka yanke maku kawai ni bazan iya yanke komai ba wnn umarnin Baffa ne ba namu ba"... Tashi Amoon yayi ya fita.. Dad ya bisa da kallo...
Sultan ko duk yanda yaso ko haduwa ma yayi da fareeda taki yarda ko kiransa bata dauka.. Ya tura text na ban hakuri yafi a kirga.. Yaje wajen mom tayi masa kaca kaca.. Ta korosa daga yau zuwa gobe kade aka basa ya samo mata ko a dauki wata a hadasu kawai.. Shi wlh ynx har zuciyar sa yasan ya hakura da Fannah fareeda yake so.. Itama gashi ynx taki sauraren sa...
.....
Tunda yusuf ya gama parking yaga Amoon zaune seda gaban sa ya fadi.. Amma ya dake.. Amoon ya bisa da kallo zuciyar sa na tafarfasa...
Fannah ta tashi bayan taga message din yusuf cewa ya karaso.. Hijab kawai ta saka ta fita zuwa can inda yake.. Karasawa tayi a hankali tayi masa sallama.. Ya dago "welcome beautiful".. Dan murmushi kawai tayi.. Ta zauna ta gaisar dashi ya amsa.. Zeyi magana knn ya tsaya Yana kallon Amoon daya nufo wajen.. Fannah ta juya ita kanta ganin Amoon seda gaban ta ya fadi.. Amma ta dake.. Yusuf yace "who is he".. Fannah ta dan kakalo murmushi "my brother".. Shide Yusuf be yarda ba dan yanda yaga Amoon ya taho cike da tsananin kishi a idanun sa yasan ba brother dinta bane.. Amoon na karasowa ba tare da ya kalli yusuf ba idanun sa akan Fannah yace "Fannah leave".. Ta dake tace "why"... A dan tsawace yace "I say leave".. Yusuf ne yace "brother I think ba haka yakamata kayi ba besides hakan ma da kakeyi be dace ba".. Amoon ya dubesa da jajayen idanun sa yace "how dare you to tell me what to and what not to do I say how dare you".. Yusuf ya rinka kallon sa... Amoon ya nuna sa da yatsa "this should be the last tym da zan ganka a gidan nan da sunan kazo wajen ta,". Fannah tace "Aliyu pls stop this kasan de shi zan aura ko".. Amoon yace "shout up don't dare repeat that Again baki da wani miji daya wuceni".. Snn ya maida duban sa ga Yusuf "and you wnn da kake gani matatace.. She's mine wlh koda wasa ka na kara ganin ka anan duk abinda nayi maka kai kaja get ur legs out of this house".. Fannah ta dawo gaban Amoon idanun ta cike ta hawaye.. "Aliyu stop this pls stop this shi wnn din shi zan aura".. Ya kamo ta look into my eyes and tell me shi zaki aura.. Ki kalli idanu na kinga Alamar zan bar wani ya aureki I said ki kalle ni kice mun na wani kike so Fannah kalleni".. Ya fada a tsawace.. Dagowa tayi tana kallon idanun sa zatayi magana Amma ta kasa dan babu abinda ta gani a ciki se tsabar "fitina, so, rigima, da kuma tsananin kishi".. Fashewa tayi da kuka sosai tana girgiza kai.. Amoon ya maida duban sa Akan Yusuf zeyi magana yaji murya Abie.. "Amoon you're very stupid you're very very stupid".. Amoon yayi shiru yana sauke huci idanun sa sunyi jajur.. Abie ya karaso.. Yana kallon Yusuf yace "kayi hakuri kaji inshaallahu hakan bazata sake faruwa ba.. Yusuf ya gyada kai tare dayiwa Abie sallama ya tafi.. Abie ya zauna saman daya daga cikin kujerun.. Hakan yasa su Amoon suka durkusa shida Fannah da taketa sharar hawaye.. Abie yace "Amoon you're playing with us ryt.., mun zama tsararrakin ka ko? Knn kai bamu isa musaka doka kabita ba who are you.. Mufa muka haife ka".. Amoon de kansa na kasa be dago ba.. Abie yace "kaga idan har baka natsu ba wlh zaka sha mamaki dan sena mugun saba ma".. Fada sosai abie ya masa ko ehem be ce ba.. Seda ya gama snn amoon ya tashi ya tafi.. ya juyo kan fannah da kanta ke kasa.. Nasiha yayi mata sosai snn yace ta tashi ta tafi"..
..
A daren ranar Amoon ya fito knn sbd ko daya be saka komai cikin sa ba ya fito dining ya nufa ze hada tea ko kallon yusrah dake zaune beyi ba gaisar dashi tayi bema kalle ta ba bare sa ta saka ran ze amsa.. Muryar ta na danyin rawa tace "yaya na hada maka tea din?".. Dagowa yayi ya kalle ta yace "yusrah wlh daga yau kika kara shiga harka na a gidan nan sena karyaki kuma kisani bazan aure ki ba bake nake so ba inde har kika bari aka daura auren nan you'll regret marrying me".. idanun ta cike da hawaye tace "yaya Amoon kayi hakuri".. "Srry for ur self.. Na riga ba gaya maki idan kinga dama ki bari a daura auren bacemun anan idiot".. Juyawa tayi hawaye sunki tsaya mata ta shige daki.. Amoon na juyowa suka hada idanu da mom dake tsaye da alama duk taji abinda yace.. Dauke kansa yayi ze tafi tace "Aliyu".. Ya tsaya tace "Ashe dama bakada mutunci? Ashe rashin kunyar taka da taurin kan naka har ya kai haka?.. Mu zamu yanke hukunci ka gaya mana bamuyi dede ba? And har kana cemata karta sake ta aure ka zatayi regretting.. Kai ko tausayin condition dinta bakayi kk fada mata haka.. To dan Allah idan an aura maka ita ka kashe ta ko ka sake ta a ranar nan zamu san ka isa damu daga haka ta wuce dakin da yusrah ta shiga.. Tabe baki Amoon yayi..
Yau koda yusuf yazo Fannah bata yarda sun tsaya inda Amoon ze gansu ba.. Abie ne ma yace suje can parlorn sa.. Shiyasa har suka gama firar su basu hadu ba.. Ta fito zata rakasa knn lokacin motar Amoon ta shigo gate din.. Seda gaban Fannah ya mugun faduwa yusuf kau bema gane wane ba.. Jin tayi shiru yace "kinyi shiru".. Ta kalli yusuf ta danyi murmushi and Amoon saw that smile.. Wanda Har kansa seda yaji ya wani mugun sara masa... ji yayi kamar yaje ya takasa da mota.. Se kawai yaga Fannah ta tsaya tana daga masa hannu shi kuma ya nufi mota.. Dan fannah bata so su hadu da Amoon shiyasa tayi masa sallama.. Ware idanu tayi ganin Amoon ya nufi yusuf da mota gadan gadan.. Cike da tsoro ta ruga tasha gaban yusuf.. Shine dalilin dayasa Amoon ya taka wani irin burki... Se kuma ya bude ya fito.. Yana kallon Yusuf yace "haven't I warned of coming to this hause ban fada maka ka fita har kanta ba".. Ya fada murya a kausashe.. Fannah tace "Aliyu ina ruwan ka da zuwan sa wajen ka yazo ko wajena.. Pls let us nace ka kyale ni". Ba tare daya kalle ta ba yace "idan kika cigaba dagaya mun haka sena saba maki ki matsa ko na hada na take ku gaba daya".. Cikin kuka tace "Aliyu babu inda zanje sede ka kashe mu gaba daya".. Yace "daga yau na sake ganin ka sede wani ba kai ba".. Fannah tace "zuwa babu fashi ai wajena yake zuwa ba wajen ka ba aurensa zanyi shidin ba kai ba"... Ya rinka kallon Fannah cike dajin zafin kalamanta zuciyar sa na wani irin tafarfasa he just wish ace bata wajen da yau seya take yusuf da mota sede a kashe sa.. Kamar ance ya juya idon sa ya sauka akan wani reg.. Da sauri ya nufesa ya dauka.. Ya nufi yusuf dashi hakan yasa Yusuf saurin shiga motar dan yaga Amoon da gske yake.. Kuma Amoon be tsaya ba seda yaje ya rotsa reg din nan a gaban motar Yusuf aikam tuni glass din yayi ratsa ratsa Fannah ta rufe baki cike da kuka.. Da sauri ta ruga ta tsaya gabansa.. "Amoon nifa sede yau ka rotsa ni and its over, between us nace shidin zan aura". Zuciyar sa na masa wani irin zafi yace "idan kika kara fada mun haka se nayi fata fata da motar ba na kuma konasa gaba daya".. Cike da tsiwa tace "na fada na fada Aliyu ka hada dani ka kona.. Bazan aure ka dinba..".. Ze sake magana yaji an sauke masa wasu lafiyayyun maruka ta both side.. Amoon ya dago... Dad dinsa ya gani.. Ze Kara marin sa Abba ya dakatar dashi yayi masa nuni da Baffa na magana.. Se a lokacin ma suka lura da motar baffa data Dad dasuka shigo.. Ga mutane duk an firfito.. Fannah ta ruga ta fada jikin daddy tana kuka sosai.. Baffa yace "yusuf ya fito".. Fitowa Yusuf yayi duk a tsorace... Baffa yace "driver ya maida ka gida and tell ur parents that jibi Friday suzo da shirin daurin aure ba sa rana ba idan yaso tarewa da duk wani biki ze biyo baya nan da bayan sallah babba. Godiya yusuf yayi snn ya wuce wajen da driver da yake a mota.. Snn yace ma Abie.. Wanda ze auri jiddah yazo da shirin daurin aure ranar Friday.. Kowa da kowa ya shirya.. Nan da Friday daurin Aure idan Allah ya kaimu zuwa bayan sallah biki da tarewar"... With shock fannah take kallon baffa kamar bata fahimtar abinda yake fada.. Hankalin ta a mugun tashe.. Shi kansa Amoon din tsayawa yayi ko motsi beyi ba jikinsa yayi mugun sanyi yayinda zuciyar sa ke wata irin bugawa.... Yana kallon baffa ya ya gama bayanin sa ya shige ...
.....
Urs
✨✨✨
Nafeesatuh....😍😍

LOVE CYCLE❤✨Where stories live. Discover now