Part 13

161 6 0
                                    

*💫❤LOVE CYCLE✨*

Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......

Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (13)✨
kallon hisam fannah tayi tace "yaya Amoon" ya gyada mata kai yace "na gaishe ki".. Tace "inaka gansa" yace "on phone yaya sultan yabani yace wai ze dawo ki aje masa abun dadi".... Murmushi kawai tayi ta kalli mummy dake hada masu breakfast tace "mummy I never expect my family to be so simple lyk dis" murmushi mummy tayi ita kanta taji dadin yanda kowa ke faran faran da ita da yaran ta.. Tace "so friendly Allah ya kara karfin zumunci" hisam yace "aunty me zance masa yace anjima zamuyi waya".. Tace "kace masa ina amsawa kuma zan aje masa" hisam ya zauna dining ya fara breakfast itama fannah joining dinsa tayi bayan sun gama suka tafi part din baffa suka gaisar da mutanen gidan ta zauna wajen mama da umma suna ta tsokanar ta tana ramawa da can idan suna tsokanar ta sede tayi murmushi amma ynx da sake dasu ramawa take dan sun jata a jiki.. Daganan gida ta koma ta shiga dakin ta ta kwanta bacci.. Ranar wuni tayi bacci ko ta tashi tana daki babu wanda ya shigo kamar yanda babu wajen wanda taje Farouq ne ma sukayi waya dashi.. Ya tafi wajen aiki..hakan yasa tunanin Aliyu ya dawo mata sabo fal cikin ranta... Allah ya sani tana son wnn bawa.. Letter din daya barmata da dauko tai bitar ta yafi a girga.. Kuka kau tayi sa kamar me... Gani take kamar ya tafi knn baze dawo ba... Amma a kasan ranta tanaji watarana Aliyu ze dawo gare ta.. Tanaji a ranta shima yanacan cike dakewar ta.... Ta lumshe idanun ta hawaye na kara zubowa "my lyf can't be complete without you.. Aliyu come pls".... Mummy kanta yau ta kula da yanayin diyar tata shiyasa a kullum take Adduar Allah ya dawo mata da wanda take so..ta kula soyayyar da take masa me karfi ce.... Hafsat ce ta shigo bayan sun gaisa da mummy ta wuce dakin fannah.. Ganin yanayin ta duk se jikin hafsat yy sanyi da sauri ta karasa kusa da ita tana tambayar ta lpy... Murmushi fannah tayi tana kokarin kawar da damuwar ta... Ganin takardar hannun ta yasa hafsa ta fizga tana dubawa....
Dan lumshe idanu hafsat tayi don tuni ta gane meke damun yar uwar tata dukda bata fada mata ba amma ta fahimce ta kuma ta tausaya mata... Ta dafe kafadar fannah a hankali tace "wnn ne ya sakaki kuka".. Fannah ta gyada kai tare da fadawa jikin hafsat ta fashe da kuka me karfi.. "My lyf can't be complete without him and he just left without saying good bye and I don't knw where to meet him".. Sosai hafsat taji tausayin ta.. Ita kanta tasan ace sadeeq ya fita a rayuwar ta ba abu bane me sauki.. Hafsat ta dan bubbuga bayan ta kafin ta fara lallashinta ta a hankali Fannah ta dago tace "mena masa har haka seda ya koyamun sonsa snn ze tafi ya barni yamun adalci knn.. Sister am just trying to be ohk but deep inside me am hurt I want him back" sosai take kuka tana fadama hafsa irin sonda take masa.. Hafsa ta rinka lallashinta seda ta bari tayi kuka me isar ta snn ta fara kwantar mata da hankali.. Har seda taji sanyi snn ta barta sukayi sallahr magrib da isha'i duk tare sukayi dinner se wajen 9 snn Sadeeq yazo su tafi tare lokacin fannah ta sake jikin ta... Sadeeq na kallon fannah yace "yaude kin rike mun ita ko" fannah tayi dariya "amun afuwa yayana" hafsa tace "ba dole ba nazo na iske ta tana kuka soyayya na lallasheta" Sadeeq ya wara idanu... Da sauri fannah ta koma ciki cike da kunya.. Suma suka wuce hafsa na basa lvri.....
Washe gari yaya khaleefa ya kawo maryam farin ciki wajen fannah kamar me ranar tare suka wuni yaya khaleefa yaso haduwa da jiddah amma taki yarda dole ya tafi yabar maryam da sunan su Fannah zasu dawo da ita... Maryam da already ta saba dasu ta shige cikin su ana ta fira fannah ta zagaya da ita cikin gidan sosai ta yaba da kyawunsa.. Maryam har seda ta kai magrib snn ta fara shirin tafiya.. Fannah de bata so ba..... Sultan ne ya shigo bayan sun gaisa take masa introducing maryam nan ya zauna suka kara gaisawa kafin ya tafi sama domin gaisar da mummy... Maryam ta dunkule hannu tace "wow ur family are so cute dubi Farouq so handsome and ga kuma yaya sultan dubi jidda no wonder wnn kyawun naki ba banza ba badan Dr Amah ba danace ki dauka a nan ciki kawai amma da ace sun fisa kyau danace kyau da sede ya barmasu.. Wata harara fannah ta mata "baki da amana wlh.. Koda ace sunfisa kyau ashe zaki iya juya masa baya".. Maryam ta ware idanu "ni na isa ai inshaallah keda amah har tattaba kune".. Murmushi kawai fannah tayi cike da farin ciki... Mikewa sukayi sultan ya sauko yana kallon su yace "dama ba kwana zaki mana ba".. Tace "no se wata rana de.. Fannah marairaice "yaya pls muje muyi dropping dinta" yanda tayi din yy bala'in tafiya da sultan...
Tare suka tafi sukayi dropping din maryam ... A kan hanyar su ta dawowa ya dube ta yace "jiya nazo sena tarar kina zance"... Ta ware idanu "zance kuma".. Shima yy kamar yanda tayi yace "yesso" murmushi tayi se kuma kamar zatayi kuka tace "yaya sultan ni kuma a ina".. Yace "yesterday evening a baya".. Ware idanu tayi "wai yaya Farouq" yace "good koba zance kuke ba" ya fada yana duban ta... Dariya tayi tana dan rufe bakin ta "we're just discussing fa" yace "really" ta tura baki "he just asked me about my boyfriend".. Kallon ta yy da sauri rufe fuskar ta tayi tana murmushi har dimples dinta suna lotsawa. Sultan yadan lumshe idanu kafin ya bude akanta yace "uhm nima a bani lvrinsa toh".. Kallonsa tayi yace "ko bazaki bani ba se Farouq" girgiza masa kai tayi.. A wani eatry ya tsaya "lets take coffee☕" budewa tayi suka jera yy ordern kayan ciye ciye.. Yana kallon ta yace "oya tell me about him"....
In brief fannah ta basa lvrin Amah... Sultan ya rutse idanun sa gaban sa na faduwa.. A idon ta kuma yaga tsanin son da takewa wnn saurayin nata cire sa ba abu bane me sauki.. Sede da sauki wnn tunda dawowar sa rayuwar ta babu tabbas matsalar sa Farouq dan shima yasan yana sonta ba kadan ba but inshaallah zeyi duk yanda zeyi yaga ya sameta .. Kallon fannah yy yace "hope you're not deceiving ur self akan cewa seya dawo rayuwar ki". Shiru tayi tana kallon sa.. Yace "srry dear but be kamata ya tafi ya barmana little sister dinmu ba" kamar zatayi kuka tace "amma ai ze dawo ko yace sure ze dawo amma sena masa tsiya because he left my sister with lots of missing"... Fannah ta rufe fuskar ta da tafi hannun ta cike da farin ciki .. A haka yay ta sakata farin ciki deep down kuma yana tunanin ta yanda ze bulloma lamarin.. Hakade har suka koma gida...
Part din su baffa suka shiga taje ta gaisar da umma snn ya rakota kalli gidan su fareeda kafin tace "duk yau bn ganta ba pls muje" tare suka shiga suka iske umman su a parlor bayan sun gaisa Fannah ta wuce sama dakin fareeda.. Zaune ta iske ta tana karatu... Tana ganin Fannah ta saki murmushi tana dan hararan ta... "Habawa duk kin manta dani" Fannah ta kama kunnen ta "i'm srry dear naga kinata fama da test ne".. Fareeda ta yamutsa fuska "ai mun gama gobe ki shirya muje".. Fannah ta ware idanu ''babu wani matsalako" girgiza kai tayi "babu" "ohk then idan kin shirya ki kirani".. tace "make sure kin gama komai da wuri cos we're leaving before 9... Fannah ta ware idanu kafin ta dage kafada "ohk no bad".. Har kasa ta rakota anan ta hadu da sultan bayan sun gaisa ta koma suka wuce har gate sultan ya rakota.. Tace bazaka shiga ba.. Ya girgiza kai yace "gudnyt sleep peacefully karfa ki tsaya tunanin Aliyu just keep it in ur mind that he is coming back to you" murmushi tayi tana gyada kai kafin ta juya da shige ciki.. Ya tafi zuciyar sa cike da fargabar kar yazo ya rasata...
Bayan sunyi sallama da mummy da daddy ta shiga bedroom dinta wanka tayi ta gama shirin baccin ta tsab snn ta dauki wayar ta.. Missed calls din farouq ta gani.. Bin kiran tayi fuskarta a shagwabe yana dauka tace "yaya na" daga can bangaren yace "cutie kinmanta dani".. "No bro".. Yace "yesso" tayi dariya.. "Yaya nabar wayar a gidane taya zan manta da kai you knw you're my best bro"... Dan lumshe idanu farouq yy yana jin sanyi a ransa kafin yace "ni kikaje".. Tace "munje kai maryam ne nida yaya sultan tace ma tana gaishe ka".. "nima ina gaisheta.. Shine kikabar wayan bayan kinsan zan kira I thought kinyi bacci ma just missing my cutie"... Tace "miss you more bro yaushe zaka dawo am so lonely tunda ka tafi".. Yace "nafi missing dinki fa just 2dys da banganki ba kinji yanda nake ji"... Tadan langwabar da kai kamar yana kallon ta tace "yaushe zaka dawo pls".. Ya danyi murmushi kafin yace "nanda 2weeks".. Kamar zatayi kuka tace har 2wks" Dan ita har ranta bataji dadin tafiyar nan tasa Dubai ba sbd duk tafi sabawa dashi fiye da kowa yace "sure dear ai zamuna waya"... Gyada kai kawai tayi sun dan dade suna fira kafin ya mata sallama tayi bacci...
.......
Fannah ce zaune saman gadon ta se lumshe idanu take cike da bacci kusan 1hour knn fareeda ta kirata ta shirya amma har ynx ta kasa tashi... Komawa tayi ta cigaba da baccin ta... 9 saura fareeda na dakin fannah turus ta tsaya tana kallon ta kafin can ta fara tashin ta.. Fannah ta sauke idanun ta a kan fareeda da take shirye babu shiri ta wartsake ganin kallon da fareeda ke mata.. Fareeda tace "kin sande baxan jiraki ba coz is tym already".. Fannah ta dubi agogon dakin kafin tace "sorry dear inshaallah i'll meet you dear yaya sultan ze kawo ni".. Fareeda ta langwabar da kai "promise" da sauri Fannah tace inshaallah...
Koda fareeda ta fita seta koma baccin ta.. Se 11 ta tashi tayi wanka ta dauki atamfan ta da aka dinka mata ta saka ta iya saka kayan hausawa bata son sune sbd nauyi suke mata da kuma can England bawani saka su ake ba..kayan sunyi matukar yi mata kyau tadan yi ture kaga tsiya taga anayi.. Snn ta yafa mayafi.. Sosai tayi kyau kamar ka sace.. Breakfast batayi ba tayiwa mummy sallama ta tafi part din baffa.. Tayi dan sallama ta shiga parlourn sultan ne zaune yana breakfast jin kamshin turaren ta ya daga kai yana kallon ta seda yy da gske snn ya gane ita .. Wara idanu yy "wow lil sis are you" Murmushi tayi wanda ya kara fito da kyawunta yace "kinyi kyau" tayi kasa da kanta tana wasa da ring din da Amah ya bata.. Kafin tace "yaya inaso naje sch dinsu fareeda pls can we go together"... Cike da farin ciki tace "why not give me some minutes" daga haka ya shiga dakin sa. Ita kuma da wuce part din mama.. Bata wani dade a can ba ta tafi wajen umma dan sunfi dasawa kodon fareeda oho... "
Suna gama yin parking wajen department dinsu fareeda wayan Fannah ta fara ringing duk suka kalli wayar a tare idanun sultan ya sauka akan best bro.. Wani abu yaji ya soki zuciyar sa.. Ita kam fannah murmushi tayi ta dauki wayar tare da fadin "yayana"... Tuni sultan ya gane wa take nufi kodaga ganin yanda suke waya kade ya isa ya nuna tsananin shakuwar dake tsakanin su.. Yasan kuwa duk lokacin daya nuna yana sonta baze sha wahala ba zata karbe sa.... Tace "yaya Farouq bana gida fa muna sch din su farida".. Yace "iye keda wa kikaje".. Karban wayan sultan yy ya kara a kunne "hey mr muna tare . ita kade kk kira knn bnda mu"... Farouq yace "kai bros yne".. "No babu wani bros Dubai tayi dadi ka manta dani Fannah kade kasani".. Dariya Farouq yy "kai bazaka gane ba ina Fannah bani ita... Sultan yace "nooo sede anjima" daga haka ya kashe wayar ya rike a hannun sa ya dubi Fannah muje.. Dan tura baki tayi tace "shine ka kashe".. Budewa yy ya fita itama ta bude ta fita tayi wani rau da idanu.. Ta zagayo suka jera... Yace "see kinyi kyau a haka".. Tsayawa tayi kamar zatayi kuka.. Ya ware idanu "oh sbd na hanaki waya da best bro shine kk fushi.. Sbd kin fi sonsa a kaina"... Da sauri tace "lahhh aa fa" yana Hararan ta yace "uhm to yane" murmushi tayi ta fara tafiya.... Tace "duka ina sonku"... Girgiza kai yy yana murmushi itama murmushin tayi tana dariya... Tunda sukayi parking fareeda ta gansu.. Yanda suka fito suka jera suna tafiya da maganar da suke ne kamar wasu masoya.... Slow ta farayi tana tafiya zuwa inda suke.. Jikin ta duk a sanyaye dan gani take kamar sultan son Fannah yake.. Sede bata fatan hakan... Tana karasowa inda suke ta rungume Fannah.. Tana kallon yanda atamfar ta mata wani kyau sosai.. Sultan yy ta kallon ta ganin yanda duk tayi wani irin yace "you look somehow.. Anything wrong".. Ta langwabar da ka "yaya duk nagaji wlh daga zuwa yunwa nake ji"..tayi masa karya... Yace "lets go and get something".. Ta gyada masa kai suka juya zuwa mota.. Fannah tace "yaya my phone".. Yace "am not giving you".. Tace kila fa ze kira".. Yace "to ya kira mana".. Ta dubi fareeda.. "Kinga wai don yaya Farouq ya kira shine ya amsa fa"... Sosai gaban fareeda ya fadi.. "Why will he collect her phone dan Farouq ya kira inde babu wani abu"... yace "to fareeda ta kwatar maki.".. Fareeda tayi yake "yaya ai kasan munfi ka yawa ko" yy dariya "kuma sarkin yawa yafi sarkin karfi ko".. Duk dariya sukayi...
Basu tsaya cikin sch dinba waje suka je wani babban eatry ya siya masu abinci ... Yanda hankalin sa gaba daya yake kam fannah yasa hankalin fareeda kara tashi.. Tama kasa natsuwa taci abinci... Taji duk ma ya fita ranta.. Haka de taita daurewa tana yake har suka dawo sch suka aje ta.. Sukuma suka shiga cikin gari.. Sosai Fannah ta sake da sultan . Wanda hakan ya masa dadi... Kusan fareeda ta dawo basu dawo ba seta kasa natsuwa jidda da hafsat sukazo amma ta kasa natsuwa cikin su suyi lvri koda suka tambayeta lpy se cewa tayi kanta ke ciwo.....
...
Satin su Fannah biyu amma kai kace sunyi shekara da family din nasu sun sake cikin su suna komai tare baka taba cewa daga baya suka saba...Fannah batada wata damuwa seta Aliyu da batajin akwai ranar de zebar zuciyar ta... Yayinda kusanci me tsananin ya shiga tsakanin su da sultan.. Sosai ta sake dashi har ynx farouq be dawo ba amma koda yaushe suna tare a waya hakan kau Ba karamin kusanci yake kara masu ba.. Wanda shine kesa hankalin sultan yana tashi.. Tabbas ya samu kusanci da Fannah amma yasan har ynx kusancin dake tsakanin Fannah da farouq ba kadan bane... Hakan yasa duk lokacin da farouq ya kira seya amsa sun gaisa.. Kuma yanayin hakanne dan ya kular da farouq yasan cewa yana sonta kuma suna tare idan ma shi farouq din yana sonta... Aikam kuma yaci riba domin sosai abin ke kaisa bango baya nunawa ne kawai amma har ransa yakejin haushin abinda sultan yake masa.. Kamar yanda sultan ke bukatar yasan yana sonta ya fahimta kuma ya fahimci da gangan yake masa sbd inde har akwai son Fannah a ransa zeji haushi.. Kuma yaji yes yaji.. Because he loves Fannah since from day one.. Shi idan sultan na sonta ba damuwar sa bane.. Abinda yake masa da ganganne is getting him.. Idan yana sonta why can't him try and capture her heart ba tare daya kuntata masa ba.. Amma inde hakane "sultan this just the beginning mucigaba da wasan"... Farouq ya fada yana duban kansa ta cikin mirror din dakin hotel din da yake a dubai....
Fareeda kam tun tana yaudarar kanta cewa sultan ba son Fannah yake ba harta dena dan ynx duk wani alamu na soyayyar fannah ta gani wajen sultan.. Sosai hakan ke damun ta tanade kokarin dannewa ne kawai .... Ko ynx haka duk suna part din baffa tunda safe jidda ce keta kiran Amoon amma yaki yin pinking kamar zatayi kuka ta dubi su Fannah tace "yaki dauka tunda na zo Abuja sau biyu ya dauki wayana... Fannah ta kalle ta cike da tausaya wa fareeda kam tabe baki tayi...ita duk son da take ma sultan bazata taba zubda class dinta a kansa ba komi halin da zata shiga akansa zata iya jurewa... Ta dubi Fannah tace "muje idan ynx zaki wuce"... Fannah ta tashi suka fita jiddah kam bama tasu take ba... Suna fitowa compound din sultan ya karaso inda suke... Yana kallon Fannah "shine har zaki tafi baki nemeni ba ko". Ta langwabar da kai... "I thought baka nan".. Fareeda ta gaisar dashi ya amsa yana kallon ta.. Snn ya dubi Fannah "and you should have check on me ai" tace "srry bro" yy Murmushi.. Fareeda de batace komai ba bnd kirjin ta dake bugawa babu abinda take.. Suna fitowa bakin gate din gidan baffa mota ya gama parking.. Seda ya gama kare masu kallo ta cikin motar.. Kafin ya bude ya fito.. Duk suka bisa da kallon mamaki.. Yana sanye cikin manyan kayan da suka matukar yi masa kyau.. Kyawunsa ya kara fitowa.. Ware idanu fannah tayi....

More comments more typing...
Urs
✨✨✨
Nafeesatu...😍😍

LOVE CYCLE❤✨Where stories live. Discover now