Part 3

270 11 0
                                    

*💫❤LOVE CYCLE✨*

Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wada mafita
Saboda duniya
Love cycle......

Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle.. (3)✨
*Not edited*
Bibdiya a UK suke saune su yan bautar rana ne sun hadu da Muhammad lokacin tana shekarar ta ta farko a sch shikuma yana ta uku sun fara ne daga abota har abin ya zamar masu soyayya.. Bibdiya bata yarda da addinin su ba KO daya ta dade ta naso ta shiga Addinin musulunci sede tana tsoro dan tasan yanda iyayenta suka tsani musulmai har kashe ta zasu iya yi.. Tunda suka hadu da Muhammad ta nuna masa tana son Addininsa ya dauki aniyar ze musuluntar da ita kuma ze aureta..... Wnn knn
Lokacin da ya koma bada jimawa ba sukaje wajen wani malami bibdiya ta karbi Addinin musulunci inda ya saka mata suna Halimatu.... A boye Ta fara Addinin ta a gidan su batare da sanin kowa ba... Sede watarana Muhammad na gida bibdiya tazo wajen sa tana kuka jikin ta duk sahun bulali wani waje duk ya farfashe tace iyayen ta sunce se sun kashe ta inhar bata bar masu gida ba tayi tayi ta fahimtar dasu amma sunki... Daukarta Muhammad yy zuwa gidan su amma se iyayen suka masu korar kare suka ce basu ba ita... Daga nan zamanta ya dawo wajensa gidansa take kwana take komai sede yasan zaman su haka baze yiwuba babu aure hakan yasa ya yanke shawarar idan yaje gida ze sanar da iyayensa game da Halimatu yasan zasu ji tausayinta su aura mashi ita.... Sun dade kafin Muhammad ya samu waya daga gida na cewar family dinsu an haifi maza da aka dade anaso wato jikoki maza dan duk mata ake haihuwan masu.. Matar Ibrahim ta haihu haihuwa ta uku knn maimuna haihuwa ta uku knn ta se Ahmad da yy ta farko wanda se ynx ya samu haihuwa matar sa ta haifi namiji itama se Aminu da be dade da aure ba shima namiji matar Rabiu ce kawai ta haifi mace ita tabiyo maza duka befi kwana bibiyu ba tsakani.. Hakan yasa Baffa ya shirya gagarimun suna dan murnar wnn haihuwa da ya samu a lokaci daya...bikin sunan aka hade su gaba daya shiyasa duk wanda baya kasar ma ya dawo wato Muhammad da Ahmad knn shi dama Ahmad matar sa a can America ta haihu haka ma matar rabiu a Sudan... Dan haka kowa ya dawo wnn biki na suna .. Taro akayi sosai nagani na fada inda yara sukaci sunan su yaron maimuna (Usman) suna ce masa Sultan yaron Ibrahim (Umar) suna ce masa faruq yaron Ahmad (Aliyu) suna ce masa haydar but sbd sunan baffa ne se suke ce masa Amoon, yaron Aminu (Abubakar) anace masa sadeeq, yarinyar (Aisha) suna ce mata humaira.. Ahaka ya saka duk sunayen sahabbai... Alokacin ne aka tasa Muhammad gaba akan ya shirya ba dan saura shekara daya ya gama karatun fa ga sakeenah nan tana jiran shi dan a hada dana Raheenah... Anan ne yake ce wa mamansa yana da wacce yake so ya mata bayanin ta da komai nan tace fafur bata yarda ba karma ya kawo wnn tunanin dan baffansa baxe saurare sa ba hakan yasa yace "to shi ne nan da shekara biyu dan yana so yadan fara aiki a can ne sbd shi tun ma kafin ya gama harya samu upper yanaso yafara aikin kafin yy aure.. Da wnn suka yarda shikam jikin sa yy mugun sanyi yana so daga haka ya kara shekara daya lokacin halimatu ta kara tun ta daga nan tasamu abinyi amma yasan ynx yy aure besan inda ze aje ta ba.... Koda ya koma sosai suka shaku da Halimatu seda ya share shekara har uku be dawo ba ko bikin Raheenah daurin aure kadai ynxo be tsaya sunyi magana a kansa ba..a lokacin kuma ankara haihuwar yara maza Rabiu yy fu'ad Ahmad ma ya kara salim snn sa'datu tayi Habib... Hakade...
Ganin Muhammad yana shirin share shekara ta hudu ne yasa Baffa ya dasa Aya a kansa ya fara tunanin something is wrong duk da yasan aiki yake se yaji gama daya hankalin sa be kwanta da zaman sa can ba aure ba.... Muhammad kau aiki yake sosai kudi sun zauna har yagama gida halimatu ma suna exams dinsu ta karshe ne yanaso ya gabatar da ita ga iyayen sa amma yana tsoro baze iya aure ya barta ba sbd besan yanda zatayi ba zata iya komawa ruwa Ranar kwatsam sega baffa shida Ibrahim a parlor suka iske Halimatu tana karatu... Wani kallo ya mata kafin ya daka mata tsawa yace mata daga da ina... Tsawar da baffa yy ita tafito da Muhammad daga daki... Cak ya tsaya ganin su Baffa... Baffa yace "me wnn take a gidan nan" kasa magana yy gaban sa na faduwa baffa ya girgiza kai yy yace well LA kyau ta to ta gaggauta barin gidan nn kai kuma kafin jibi na ganka a Nigeria amma ma bani kunya... Daga haka suka fice cike da fushi.... Zubewa Muhammad yy a wajen yana kallon Halimatu data rude cike da tsoro.. Yama rasa me zeyi kawai ya yanke shawarar ya tafi da ita ya masu bayani haka kau akayi a ranar suka wuce Nigeria da Halimatu da take cike da tsoro... Muhammad tawa baffa bayanin komai da kudinsa akan halimatu se baffa yace "Allah ze bashi lada amma baze yarda ya aureta ba dan baze iya hada jini da ita ba nan Muhammad yace shifa se ita dan baze iya auran wata ba baze iya rabuwa da itaba sbd shine silar rabuwar ta da iyayen ta nan Baffa yace sede yanemi wani uban bade shi ba... Hakan ya daga hankalin Muhammad gashi duk yan uwansa sun juya masa baya seda Muhammad ya hadasa da Liman da kuma wani malam hamisu snn ya yarda aka daura auren Muhammad da Halimatu sede me a ranar Baffa yace yabar gidan ya cire sa daga cikin jerin yaran sa baya bukatar ganin sa shide be masa baki ba amma baya son ganin sa kusa dashi.. Hankalin Muhammad ya tashi gashi cikin yan uwansa babu me masa magana se sa'adatu da Raheenah... Yana ji yana gani yabar gidan mahafinsa sukazo suka ci gaba da rayuwa da Halimatu tana yawan cewa su su koma su roki gafara yasan zasu hakura yace aa ta bari se sun haihu yasa baffa ze yafe masu... Halimatu bata haihu ba seda suka shekara hudu ta haifi yarta kyakkyawa ya sakawa yarinyar sunan mahaifiyar sa wato khadijah.. Daga nan suka dauko hanyar dawowa Nigeria cike da farin ciki da kuma sa ran baffa ze amshe su.. Lokacin yaran duk sun girma da dan wayonsu .snn an hafi suma mata yan jarirai dasu akwai yusrah, sumayyah, jidda, fareeda, da Hafsat.. Duk kwanaki ne tsakanin su.. .. Yanda Muhammad yy tunani ba haka bane dan baffa cewa yy ya bar masa gida baya bukatar sa baya bukatar ganin sa yacire sa daga jerin yaransa da haka yatafi ya basa waje... Kuma ko yan uwansa babu wanda ya nuna yy farin ciki da ganin sa kodan baffa ya nuna baya bukatar sa knn... Hakan ba karamin cin ran Muhammad yy ba yaji shiko baze kara zuwa wajensu inhar basu neme sa ba yaji kasar ma bayason ta... Tun daga nan suka dawo UK da zama suka cigaba da kula da khadeeja da suke cema fannah sosai Muhammad yake son fannah dan yana ganin bashi da wata dangi sama da ita se matar sa dake mugun yi masa biyayya yana matukar alfahari da ita mace ce mai roko da addini da sanin yakamata ya daga sosai wajen koya mata hausa ta kau rike kamar yarenta.. Snn wasu al'adun hausar ma duk sunayi dan yanaso Fannah ta san yaren ta kuma alhmdullah ta taso cikin sa.. Duk wata soyayyar su na kan fannah dan ita kade suke kallo a matsayin dangin su snn ita kade suka haifa se da ta shekara tara snn suka mata kani Aliyu suna ce masa hisam suke nan su hudu suke rayuwar su se abokanai na mutunci tun mummy na masa maganar komawa Nigeria harta dena dan tasan beso koda Fannah ta matsa tana so ta tasani dakyar yabata lvr ranar kau yini yy suku ku dan kamar an fama masa inda yake masa kai kayi.. Shekara goma shatara knn be taka kasar sa Nigeria snn be ga wani dan uwansu ba... Amma yana dan jin lvrin su kamar Ahmad yana US dan rabi rayuwar sa anan yake rabi kuma a Nigeria shida iyalansa rabiu ma yana dan zama sudan haka ma Ibrahim yakan dan zauna Us amma ba kamar Ahmad ba... Sede basu taba haduwa ba.. Snn babu wanda yasan gidan sa... Daddy yy arziki sosai kamar yanda yasan suma family dinsu sun kara akan dan familyn Radda ya kara bunkasa wurare dayawa ansansa shiyasa shi ya dena amfani da Radda sbd bayaso wani yaji lavarin sa koyasan inda yake haka ma su fannah baya musu amfani da Radda duk da wasu sun riga sunsan sa da Radda amma abin da sauki... Wnn knn
....
Dan lumshe idanu tayi a hankali bacci ya dauketa....
Se gab da azahar ta tashi snn tayi sallah ta tafi dakin mum can suka zauna har daddy ya dawo sukayi dinner tare.. Snn ta koma dakin ta tahau chat... Bata wani jima tanayi ba ta sake kwanciya wani baccin se safiya washe gari friday basu da lectures dama practical ne zasuyi ta an daga se Monday dan wani sabon doctor ne ze zo ya masu bayani akan wani surgery na ido... Weakend dinta maryam ce tazo sun dade suna fira da shirme a gida kafin su tashi suje gidan su Vaneesa daga nan suka fancama yawo cikin gari... Ranar Sunday kuma wuni tayi tana research game da surgery din da zasuyi gobe dan ita tanaso taga tana communicating a class Fannah yarinya ce me kokari da ko a department dinsu masu irin kanta kadan ne....
Monday...
Tsaf ta gama shirin ta ta dauki komai da take bukata ta dauki labcoat dinta ta fita.... Koda taje apartment din maryam har ta gama shirin ta a nan wajen maryam tayi breakfast daganan suka wuce a babban teaching hospital din dake sch din tayi parking suka shiga ciki sunzo gab da zasu shiga lab din ne ganin kowa da labcoat yasa ta fara zare idanu ganin babu tata a hannunta maryam ta kalleta tace "hey girly where is ur labcoat?" Dafe kai Fannah tayi "oh god na barshi a apartment dinki" maryam ta zaro idanu tana duba wrist watch dinta snn tace "huh is already tym bamu san halinsa ba kar mu fita ya shigo kokuma bari na kira maid dita seta shigo taxi ta kawo ko" gyada kai Fannah tayi tana tunanin Allah yasa kar ya shigo dan bata sani ba ze barta ta zauna ba labcoat koko... Bakin kofa suka tsaya suna jira da adduar Allah yasa tazo kafin doctor din ya shigo... Sede addu'ar ta bata karbu ba dan mutane ne suka fara shigowa ana natsuwa cewa gashi nan... Zuwa sukayi suka zauna gaban Fannah se faduwa yake mutane se kallon ta suke ganin bata da labcoat.... Tsit akayi sbd shigowar sa.. Yayinda lokaci guda gaban Fannah ya yanke ya fadi lokacin da ta daura idon ta akan guy dinta da ta gefawa tissues sanye cikin suit blue black da suka matukar amsar sa snn suka dace da fatar jikin sa gashin kansa da yake baki yasha gyara inda ya kwanta lufluf kyawawan idanunsa sanye cikin farin glass se yakara ma fuskar sa wani kyau lips dinsa da suke pink se ya kara wani haske... A tare maryam da Fannah suka kalli juna cike da tsoro.. Kallon sa sukayi jin cool voice dinsa na ratsa kunnen su... "Am Dr. Amah nice meeting you all" a tare akace "welcome sir"... Dan binsu ya rinkayi da idanunsa yana nazarin su kafin ya sauke su akan Fannah.. A lokacin ji tayi kamar ta shide sbd tsoro ko maryam da ba ita ake kallo ba dauke numfashi tayi.. Yana kallon ta da kyau yace "hey you".... Daga mayan idanun ta tayi ganin ita yake kallo yasa Muryar ta na rawa tace "si...sii.. Sir" yace "where is ur lab cloth" wani miyau ta hadiye ganin yanda kallo ya dawo kanta tace "sir.. I.. I.. Forget ..t..it but its on the..way.." Katse ta yy yana daga mata hannu kafin ya dubi sauran yan class din yace "class a medical student is coming into the lab for practical without lab cloth is that student a serious student" a tare akace "no sir"... Juyowa yy yana kallon ta tare da nuna mata kofa yace "out of my class" muryar ta na rawa tace "sir.. am srr... " "I said out my Frnd".. Ya katseta cikin tsawa... Da sauri ta fita tana danne kukan da ya taho mata... Bata son missn class din nan ko kadan ko daya batayi marhabun da cewa wnn shine doctor dinsu ba bata fi minti biyu da fita ba aka kawo mata labcoat din ta dawo tana kuyo cool voice dinsa inda yake bayani cike da kware.. Seda ta saita natsuwar ta kafin tace "permission to join the class sir".. Wani kallo ya juyo yana mata kafin ya dauke kai yace "come in but stay by the door and keep standing ur punishment for coming late".... Tsayawa Fannah tayi tanajin kamar ta tafi dai dai class din is very important da wlh bata zama.. Tana kallon yanda yake kowaya cike da kwarewa kuma ana ganewa ynx ana masu daga farko ne kafin sucida gaci... Ana masu bayani ne dallah da komai 4wks zasuyi sunayi snn su duba result...tym na kurewa yace "who is ur class rep"... Nunata akayi.. Hakan yasa ya kalleta shima kafin ya kallesu da mmki yace "did she deserve or have any qualities of being a leader?" Shiru duk akayi ta be baki yace "well I knw she don't even know her responsiblity so class we shall meet next week bye" daga haka ya shige wani office dake Lab din.... Fannah ce farkon fita tasamu wani waje ta zauna ta fashe da kukan da take dannewa... Maryan ce tazo tana lallashin ta sbd tasan she's is hurt ya dizgata over... Vaneesa ma ta fara bata hakuri.. Seda ta dena kukan ne maryam tace "mujeki basa hakuri tun kafin abun yy nisa babban course yake daukar mu rasashi matsalane... Gyada kai kawai fannah tayi tana danne bacin ranta zatajene kawai sbd tana tsoron caurse dinnan... A office din suka samesa tsaye yana gyara wrist watch dinsa suka gaisar dashi dage gira yy batare da ya amsaba yace "what?".. Maryam ta zunguri Fannah... Murya ba rawa Fannah tace "sir am..am sr...srry for the other and today pls forgive me is a mistake sir".... Ta fada kanta kasa... Budar bakin sa se cewa yy "can I have my way pls" ya fada cike da wulakanci ba shiri suka matsa ya fice ya barsu tsaye kamar gumaka.....
Juyawa Fannah tayi ta fice tana share hawayen ta da sukaki tsayawa suna fitowa maryam na iskota.. "Pls Fannah calm down everything will be settle ohk"... Cike da tsiwa Fannah tace "let it continue be like that I will not apologize again because I hate down grading i can't take it wlh"... Maryam tace "Fannah you knw this not the solution ryt just calm down lets find a way to settle this kinsan de kece a kasa ko" cike da masifa Fannah ta bude baki zatayi magana maryam tayi saurin rufe mata baki ganin Dr. Amah din yazo ze wuce ta saitin su.. Harara fannah ta zabga masa yayinda maryam tayi saurin gaisar dashi ganin ya juyo sun hada ido .... Kafin ya Amsa Fannah taja wata tsuka tabar wajen duk binta sukayi da kallo kafin ya juyo ya kalli maryam da take wani zare idanu cike da tsoro... Murmushi ya sakar mata wanda seda taji kamar ta shide itama ta mayar da yake snn tabi bayan Fannah da sauri......
A garden ta iske fannah ta kifa kai tana na kuka rungume ta maryam tayi kafin ta kama hannun ta sutafi wajen mota... Maryam ce ta jasu ita ta kai Fannah har gida rudewa mumm tayi tana tambayar meya faru... Maryam tace "kanta ne ke ciwo"... Dakin. Fannah ta shiga maryam na kallon Fannah tace "fannah just think of what you did kin kyauta knn" fannah ta tabe baki kafin tace "kawai bazaki gane ba maryam" shhhhhh maryam ta katse ta "naji but a matsayin ki na dalibar sa yakamata ki basa hakuri koda kau me ya maki dole ki sauke kanki kasa"... Tana gama fadin haka ta fice bayan ta aje mata key din motar ta.... dan tabe baki fannah tayi tanajin wani irin haushin Dr. Amah din.. Lumshe idanun ta tayi a hankali bacci ya dauke ta...se 2 ta tashi da sauri tayi wanka ta tayi sallah snn ta fito cin abinci... Mumm da hisam na parlor dining ta wuce ta zubo aplate snn ta dawo parlor ta zauna tana ci.... "Meya sakaki kuka a sch yau"... Ajiyar xuciya ta sauke tasan inhar tayi karyar ciwo mumm zata gane ta... Tace "mumm is just misundersterding nida wani lecturer"... Mumm ta gyada kai cike da daure fuska tace "I see can you start growing da har kika fara samun matsala da lecturers dinki so listing to me attentively kije kisamesa and apologize if not I will show you the real me ai naji tym din da maryam na maki maganar kinaso ki zama masiffiya ko?" Kamar Fannah zatayi kuka tace "am srry mom i'll apologize".... "Better"... Daki fannah ta koma idanun ta cike da hawaye wlh da ba dan mummy ba sede sucigaba da tafiya a haka......

More comments more typing...
✨✨✨
Urs
Nafisatu😍

LOVE CYCLE❤✨Where stories live. Discover now