Part 27

164 6 0
                                    

*💫❤LOVE CYCLE✨*

Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......

Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (27)✨
Karasawa tayi wajen motar ta... Maryam na ciki tsokana ce cike da bakin maryam but ganin yanayinta seta gumtse abunta ta koma lallashi . Tana bada hakuri da kwantar mata da hankali .. Ita de Fannah batace komai ba amma ranta gaba daya babu dadi.. Bata taba tunanin zata sha wahalar soyayya irin haka ba... Suna karasawa gida sallah kade tayi ta kwanta.. Maryam tace ta taso suyi lunch tace bazataci ba kanta ke mata ciwo.. Nan fa hankalin maryam ya tashi.. Wnn ciwo kan da Fannah take bata sonsa.. Dibar Abincin tayi ta kai mata sama.. Duk yanda tayi da ita taci kinci tayi.. Har seda ta kira mata mummy.. Mummy nazuwa ta fashe mata da kuka.. Mummy ta rungume ta tana bubbuga bayan ta.. Tasan abinda ke damun diyar tata.. Is not easy ace mutumin da kk so kk mutuwar gani ace bazaka aure sa ba.. Mummy bata hanata ba har seda tayi kukan me isarta snn mummy ta fara bata abincin da kanta.. Bayan ta koshi ta bata magani daga nan bacci ne ya dauke ta... Shima baccin duk ba wani me dadi ba duk nasu Amoon ne da sauran family din....
Ko washe gari kin zuwa sch tayi sbd ciwon kan .. Maryam ce kade taje.. Wanka kawai fannah tayi ta kwanta , dan kallon break dinta da aka aje mata tayi ta dauke kai.. Ta juya tare da janyo jacket din Amoon ta rugume tanajin kamshin sa me dadi.. Ta lumshe ido a haka bacci ya dauke ta.... Har maryam ta dawo bata tashi ba motsin maryam ne ya tashe ta.. Maryam ta dubi break din ta kalle ta.. "Don't tell me tunda na tafi bacci kike".. Fannah tace "wai har kin dawo"... Maryam ta zauna gefen gado "oh ni wnn soyayyar taku harni wahala nake sha wlh".. Dariya Fannah tayi tace "se akace maki sbd shine bnd lpy"... Maryam ta nuna mata jacket din "ga sheda nan abun yakai ma baki iya bacci seda shi a kusa dake".. Fannah ta watsa mata harara.. "Bnsan saka ido".. Maryam ta tabe baki "anyway yana parlor".. Babu shiri fannah ta zauna tana zare idanu "what wa? you mean yana parlor me yazo yi"... Maryam na kunshe dariyar ta tace "see you dalilai dayawa.. Shima fa gidan su ne snn ga kuma matar sa a ciki"..... Wata harara Fannah ta zabga mata. Ganin yanda take kunshe dariya.. Aikam ta fashe da dariya... Fannah ta hade rai... Seda maryam tayi me isarta snn tace, wajen ki fa yazo ki shirya ynx ze shigo nan din"... Fannah ta marairaice ce "na shiga uku" Mikewa Maryam tayi tabar fannah da zare idanu ...janyo hula tayi tasaka se Kuma ta ja blanket ta rufa tanata zare idanu ....tun kafin ya shigo ma kamshin sa ya mata sallama ..runtse idanu tayi kamar me bacci ..bayan ta tabbatar ta kauda jacket dinsa dake gefen ta .. Da sallama ya shigo.. Zuciyar Fannah se bugawa take.. Idon sa na kanta ya karasa kujerar dake gaban mirror ya ja zuwa gefen bed din ta ya ya zauna.. Ya zuba mata idanu.. Duk da yasan ba bacci take ba se bece da ita komai ba kuma idon sa ta kanta ta.... Fannah tana jin yanda ya tsare ta da idanu gaba daya seta tsargu.. Can de ta kasa jurewa ta bude idanun suka hada idon tura baki tayi "kallon fa".. Ya ware idanu... "To ina ruwanki keda kike bacci"... Ta hararesa, "taya zanyi bacci bayan kazo kamun tsaye".... Ya gyara zama yace "ai naga kamar idan ina kusa se baccin yafi maki dadi".. Tace "tayaya".... Jacket dinsa ya nuna mata dake gefenta.. "Gashi nan".. Kallon jacket din tayi se kuma ta hade rai.. "To me ne hadin ta da bacci na"... Ta gyara zama "it suppose to be in the press not on the bed".... Tace "toni nasan meya kawoshi nan ne".. Ta basa dariya amma beyi ba yace "how are you feeling".. Tace "Alhmdllh".. "What's wrong with you".. Kanta ta nuna masa.. Turo kofar maryam tayi ta shigo duk suka bita da kallo tana rike da tray.. Ta mikawa Amoon "yaya Aliyu pls help us ka bata wlh bataci komai ba".. Karba yayi snn ta juya ta fita.. Ajewa gefe yayi ya ciro wani abu kamar touch cikin pocket dinsa.. Yace "muga idon ki".. Dan matsawa kusa da ita yana dan haska idanun ta for some seconds.. Snn ya kashe yace "kina sakawa kanki damuwa ko".. Shiru tayi batace ce komai ba.. Yace "srry inshaallahu everything will be ohk".. Dan gyada masa kai tayi.. Yace "srry for yesterday am srry love.. I caused us all this" yanda yayi din duk se taji ya bata tausayi itama setaga duk ya rame tasan shi kansa yana cikin damuwa sosai dauriya ce kawai irin tasa.. A hankali tace "duk ka rame kayi rashin lpy ne".. Ya kalleta se kuma ya girgiza kai.. Yace "just pray for us pls pray for us".... Idanun ta ya cika da kwalla.. Wayar ta ne yy ringing duk suka kalla sultan ne... Amoon ya ringa kallon wayar zuciyar sa na tafarfasa yanada wani mugun kishi inde akan Fannah ne... Lura da hakan da Fannah tayi ne yasa ta dauki wayar ta kashe gaba daya.. Dan sauke ajiyar zuciya yy se kuma ya kalle ta.. Ta langwabar da kai "srry..". Yy murmushi tare ta kamo hannun ta a hankali yace "I love you".. Ta dan lumshe idanu a hankali se kuma ta bude kamar zatayi kuka tace "am afraid".. Shafa gefen fuskar ta yayi a hankali yace "do you love me?". Gyada kai tayi tana hawaye.. Kafin a hankali tace "yes I love you.. I love you Aliyu.. I don't knw how to say it but you're the only person I love"... Se kuma ta fashe da kuka...rungume ta yayi cike da farin ciki "I love you too, I love you more and more dear".... Ya fada cike da tsananin sonta.. Da bayajin akwai wani mahaluki dayake mata kalarsa kuma bayaji ze iya bari wani ya mallaketa ba shi ba sede idan babu ransa sede idan mutuwa zeyi".. Fannah tanajin yanda zuciyarsa ke bugawa.. Gashi sosai ya rugumeta ... A hankali ya dago ta yana share mata hawayen.. Ta danyi murmushi tare da janyo jacket dinsa ta rungume tace "I love this jacket".. Yace "really zan kawo maki irinta".. Ta girgiza kai.. "No wnn nake so.sbd taka ce", yayi murmushin dake Kara masa kyau yace "abuna naki ne".. tace "thank you".. "Ba thank you ba abinci zaki zo ki ci and ni zan baki da kaina".. Fannah ta noke kafada.. Dauka yayi aje mata a cinya "I'll watch you eaten.. One day I will feed you my self".. Fannah tayi masa gwalo.. Murmushi kawai yayi yana kallon ta happily... Ita kanta Fannah duk setaji ciwon kan ya tafi rabon data samu tym dashi irin haka har ta manta...... Koda ze tafi ji tayi kamar karya tafi.... Yana tafiya maryam ta shigo tana kallon ta Fannah tace "yade kallon fa".. "Dole na kalleki ai har kinji sauki sbd maganin ki yazo".. Murmushi kawai tayi "kinga laifi na?"..
Ranar Fannah ta ware.. Ita kanta mummy tasan dalilin ware war tata kuma taji dadi kullum Addua take ma diyar tata Akan Amoon ita kanta tayaba da hankalinsa dakuma irin kaunar da yake wa Fannah. Tana kuma adduar Allah yasa rabon ta ne"..... Koda dare ranar bnd chart da Amoon babu Abinda take.. Ko a rayuwar su tada bata taba sakewa dashi ba irin yau..". Ita kanta bata taba sanin haka yake ba seyau data sake dashi.. Da kyar ya bari tayi bacci... Suna tashi daga lectures ya tura mata message wai ta jira inda suka saba haduwa.. Duk yanda tayi da maryam ta bita kin zuwa tayi.. Hakanan ta wuce.. Tana zuwa seta gansa a zaune.. Ta karasa tace "ashe kana nan shine kace na jiraka..". Ya aje wayar sa yana kallon yanda tayi kyau.. Yace "wancan karon nine nazo na sameki so today I decided kixo ki sameni"... Dan murmushi tayi seta tuna ranar daya fara samun ta anan wajen ranar da yace zasu zama frnds..... Zaunawa tayi tana murmushi.. Yace "it all started here anyway yaushe zaki rakani hand ball"... Ta kallesa tana ware idanu fuskan ta dauke da murmushi tace "naje ka kara buga mun handball ka ki bani hakuri. Idan kuma nayi magana kace zan saka maka ciwon kai".. Ya danyi dariya.. Dan yana sane ya buga mata ball din nan.wancan lokacin." Ta hade rai "oh dariya ma na baka ko karfa ka manta ko hakuri baka bani ba wancan tym din". Ya ware hannu yace "hakurin me bayan kin rama you throw a tissue for me ko kin manta"... Dan hararansa tayi "kai abubuwa nawa kayi mun see you".. Yace "srry ynx de yaushe zamuyi an jima ku shirya sena nazo muje" ta gyada masa kai... Kamar yanda yace hakan kau akayi suka shirya suka shirya harda hisam.. Yazo ya dauke su.. Fannah ta rinka satan kallon sa ganin yanda kayan suka mugun yi masa kyau.. Dan hada ido sukayi ya kashe mata.. Suna isa su maryam suka bude suka fita zata fita yayi saurin kamo hannun ta.. Ta juyo tana kallon sa yadan kashe mata idanu yace "se satar kallona kike nayi kyau ne".. Tace "zero bakayi ba".. Dariya yayi sosai har seda ta shagala da kallonsa.. Yace "ba'a son karyata babba amma karya kike".. Fashewa tayi da dariya.. "Tace "oh. Hakama zakace".. Bude kofar yayi ya fita...itama fita tayi.. Tuni dama maryam taja hisam sun tafi wasan su.tare sukayi komai dashi se wani langwabe langwabe take shikam ya biye mata karshe ma cewa tayi batayi shima tace bazeyi ba.. Dole ya hakura ya siya masu kayan ciye ciye.. Se yamma sosai snn suka koma gida.. Su maryam na fita daga motar yace "I will be living tomorrow" ta kalle sa da sauri "zuwa ina" yace "America dama ai just squeeze amma inada aiki dayawa".. Tace "se yaushe knn".. Ya dube ta.. Da sallah kawai mu hadu a katsina"... Ta ware idanu "har sallah".. Dan ita har tsoran komawa take baffa ya bata wanda yace.. Kuma tsoro takeji kamar yasan tunanin da take knn ya kamo hannun ta "inshaallahu wnn karon baza'a samu matsala ba babu dadewa saura 2weeks ramadan and ga waya nan koda yaushe kuma tare kinji".. Gyada masa kai tayi jikin ta a sanyaye yace "I love you".. A hankali tace "love you too"... Yadan langwabar da kai kamar zeyi kuka "to ki saki ranki mana".. Budewa tayi ta fita.. Dan zata iya fashe masa da kuka. Dan murmushi yayi jikinsa a sanyaye ya yaja motar.. Fannah ta daure batayi kuka ba...ta zauna gefen gado tayi folding hands dinta trying hard batayi kuka ba.. Duban wayar ta dayayi kara tayi alamar shigowar sako.. "Don't cry pls I love you" shine abinda ya turo mata se hawaye sharrr maryam tace "to me arhar hawaye me kuma ya faru".... Nan ta fadawa maryam yanda sukayi ta karasa da fadin tsoro nake ji maryam".. Maryam tace ki kwantar da hankalin ki inshaallahu komai ze zo da sauki..
Hankalin Fannah ya kwanta sbd yanda maryam ta kwantar mata da hankali.. Ranar da daddare sun dade suna waya kuma hankalin ta yadan kwanta... Washe gari Amoon ya wuce America Fannah sam sam bataji dadin tafiyar sa ba..
Tunda yatafi be yarda ya barta da kewar sa ba kullum suna waya wani lokacin harda vedio call... Wnn karon shakuwar su tafi ta da... A haka har a aka shiga watan azumi... Kowa ya maida hankalin sa kan ibada.. Ana saura sati sallah su Fannah suka koma Nigeria.... Koda taje kamar yanda tayi tsammani ne su jiddah babu wanda yabi ta kanta.. Itama bata bi ta kansu ba sbd tasan wanda suke domin shi ita yake so ba su sede tanajin tsoro sbd bata manta da maganar baffa ba akan cewa ze sama mata wani kuma taga alamar har ynx sultan na kan bakansa...
Yanda chucu ke nan da nan da Fannah kade ya isa ya nuna maka cewa tana son yayan nata da ita.. Itama sun kulle sosai da farouq.. Ana saura kwana biyu sallah ne tafiyar su kt shiyasa kowa ya fara shiri dan dama duk sallama acan sukeyin ta a mota ci duk suke tafiya kowa ze sami motar da ze shiga su tafi..sultan ya turo mata message akan cewa su tafi a motar sa.. Amma ta share batayi masa reply ba.. Ranar da zasu tafi duk suna gidan Baffa sun fito duk za'ayi tafiyar tana ganin sultan se kallon ta yake amma ta nuna kamar bata gansa ba.. Baffa na fitowa dasu Abie kowa ya mike duk suka fita.. Da abie da baffa da daddy mota daya suka shiga.. Fannah ta rinka kallon motar Amoon dake wajen da tunanin Ko wani ne ze tafi da ita.. Bata gama tunanin da take ba taga ya bude ya fito.. Babu shiri ta ware idanu cike da mmki.. Dayawa ma kallon sa suke da mmki.. A wajen daga dad se mammah da saleem suka san ya dawo jiya amma ko chucu bata sani.. Ya karasa wajen iyayen nasa ya gaisar dasu snn yaje yana mikawa su sadeeq hannu harda sultan.. Su chucu suka gaisar dashi.. Yadan kashewa Fannah idanu ta dauke kai tana murmushi dayawa a wajen sun gani amma babu wanda ya kula dad dinsa ya girgiza kai kawai.. Mammah tace "kai da suwa zaku tafi".. Yadan sosa kai.. "Mammah zan tafi da chucu da Fannah or chucu su tafi da farouq I will go with Fannah and fareeda".. Kowa a wajen kallon sa kawai yake harda Fannah dan har kunya taji.. Karasawa yy ya bude front seat yana kallon Fannah yace "get in".. Kanta kasa taki dagowa Abbu ne yace "jeki mana mamana".. A hankali ta karasa fareeda ma tabita".. Dadi kamar ya kashe chucu domin taga yanayin reaction din su jiddah da sultan bana farin ciki bane.. Murmushi kawai Dad yayi yana kara mmkin dan nasa.. Be kara bi takan kowa ba ya bude motar sa ya shiga.. Yayi reverse snn ya dago suka hada ido da sultan kashe masa ido yayi snn yaja motar ya fice da mugun gudu.....
More comments more typing...
Urs
✨✨✨
Nafeesatu...😍😍

LOVE CYCLE❤✨Where stories live. Discover now