Page 39

197 25 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 39
_Daga wannan Pagen din insha Allah wanda zai zo shine karshe!_

Taimaka mishi nayi ya mike tare da kai shi dakin shi, muka shiga bashi taimakon gaggawa, saboda yankan da aka mishi, har jinin ya tsaya, sannan na lalle shi tare da Mik'ewa zan fita yace min.
"Me yasa min fuskar ki?"
Shafawa nayi sannan na ce mishi.
"Babu kome!"
Gyada kai yayi sannan ya koma tare da kwanciya da kanshi yana fadin.
"Kar ki manta da tafiyar mu,"
"Insha Allah! Sai da safe!"
Na juya tare da ficewa daga dakin, ina fitowa waje na hango Fudail.

A hankali na karasa gare shi, sannan muka nufi cikin garin.
"Me yasa ba zaki iya tafiya ba, ga damar tafiya amma ba zaki tafi ba! Ko kina tsoron Mehran ne kar ya saka a kashe ku?"
Kallon shi nayi na wasu dakikai, sannan na cigaba da tafiya na, tare da kallon gabana.

"Haba Wakiliyar Mehran, me yasa ba zaki amsa min ba?" Ya faɗa cikin raha da Tsokana,
"Tausayin MEHRAN nake ji! Shi ya hana ni tafiya, da tun tuni nayi tafiya ta."
"Ko kema kina son shi ne?"
"Ko kana kishin shine?"
Na fada ina murmushi tare da tsare shi da ido, fisgo ni yayi tare da hadani da jikin wata bishiya, yana kallon fuskana da nake kallon shi babu tsoro.
Kan shi ya sunkuyar zai hada da fuskana nayi maza na kare hakan tare da kai mishi duka.

"Ni ba kazama bace! Na haɗa jiki da shugaban ka, kuma na hada da kai wannan shine kolokuwar cin fuska da mutuncin Aamaan." Na fisge kai na, tare da mai da hankali na akan tafiyar da muke.

Duk yadda yaso su fahimci juna taki asalima kamar bada ita yake ba, ga shegen kwarjinin da tayi mishi.
....
Koda na shiga keb'entaccen shashi, na sami Sultanah Fazilatul nisa a zaune tana kallona, bata ce min kome ba, har zan wuce tace min.
" Me yasa kike rusa shi daga kasa? Abinda kike aikatawa zai ja a dakatar dashi na tsawon shekaru uku zuwa goma.

Abinda kike bukata ba zai samu ba, idan har kika sake kika bar masarautan nan, tabbas Aamaan zai iya fuskarta tsigewa daga muqaminsa. Tare da mai dashi daya daga cikin masu jiran gado.
Don Allah Karki janyo min abin kunya da tashin hankali, sannan zai fita daga cikin gidan sarautar har sai ranar ya dawo da martabar shi. Duk da ba laifi bane hukunci ne laifin da ya aikata, na girmama Baiwar shi sama da dattawan Fada.

Don Allah Karki saka ni asarar duk faffutikar da nayi, domin zasu mai dashi wancan fadar da yake wancan dajin ne. Gashi bai da goyan bayan gwamnatocin shi.

Bai da goyan bayan mahaifina bai da goyan bayan Hoyam, kuma ba lallai bane sauran mutanen fada su taimaka mishi, don Allah Karki ja min asara biyu."

Kura mata ido nayi tare da kallon yadda take cikin tashin hankali, sannan nace mata.
"Wai ke meye Matsalarki da Shine? Ina ruwanki dashi ne? Meye nufinki akan shi Ni kam ma zargin ki nake, Wacece mishi ke?"
Wani irin rugugi garin yayi tare da sake wata irin tsawa, wanda ya haifar da walkiya me shegen haske, tare da haska ko ina,cikin d'aga murya tare da izza me hade da iko tace min.

"Nice Mahaifiyar shi!" Wani irin tsawa aka kuma bugawa me shegen ƙarfi wanda ya saukar da wani irin ruwan sama babu kakkautawa, ta tako gabana tare da kallona.
"Tun daga lokacin da kika iya dukar Jasrah a cikin gidan nan, maganar Uwaisul Qarni ya tabbata zaki zo taimakona!" Da sauri na kalle ta tare da sake baki na.
"Kinyi mamaki ne? Bayan na tabbatar dake ma kin san shi? Ba abin mamaki bane, haka bai wadatar dake ba, sai da kika yi mata duka ta kasa koda amsar kanta. Sannan Ni nasan cewa ke ba daga karamar ahali kika fito ba, amma bansa daga wani ajalin kike ba.

Ba zan miki dole ba, sai dai ki sani kece kika kunna fitilar Mehran! Kuma kece kika kashe fitilar Mehran, nasan koda na hanaki ba zaki hanu ba, amma bana cire rai da rahamar Ubangiji, zaki dawo gare mu."

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sDove le storie prendono vita. Scoprilo ora