Page 28

151 25 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 28

A hankali na sauke idanuna daga cikin nashi cikin matsanancin kunya, jikina yana kuma rawa. Dake Allah ya taimake ni muna daura wani fallen yadi a kirjin mu, yadda babu abinda zai sami nonuwar, a Sannun yake saussauta rikon har Allah ya taimaka ya sake ni, kawai na kuma tafiya zan fadi Yasaka hannun shi ta k'uguna.

Hannu na duk biyu suna kirjin shi a dunkule na rufe idanuna, ina sauke ajiyar zuciya. Cikin mutuwar jiki ya janye Ni daga jikin shi ya shiga wankar shi. Kin yin kome yayi ya tsaya yana jirana na mishi.

A Sannun na ja kafana zuwa gare shi ina me shafa wata ruwan sabulun wanka na, na fara goga mishi da wata soso irin auduga nan, ina mishi ina me dauke kai na, har na kammala mishi tare da ajiye sosan na shigo dakin na dauki Mayafi sabuwa kal na koma na kai mishi, sai da ya gama b'ata min rai da lokaci sannan ya amsa daga hannuna.

Wato ina ga Mehran so yake na dauke shi ko ya koma jinjiri ina ina ina dashi, haka Ni daya nayi ta masifa a rai na, kamar zan dake shi. Yana gama mulkin shi ya fito, dan har na riga shi fitowa, ina zan iya rayuwa da mutumin da yake abu kamar kwai ya fashe mishi a cikin shi.

Bayan na gama na fita sami baki suna jiran shi, dawowa nayi ba gaya mishi. Takowa yayi gaba na, yana zuwa ina matsawa har muka kure bangon d'akin.

Hannun shi naji a kwaib'ina, da sauri na kai mishi bugu yayi maza ya tare, na kuma buge hannun ya tare, kallon kwayar idanuna yayi, wani irin budewa kwayar idanun shi yake, ban tab'a sanin cewa akwai abinda zai haifar min da nutsuwa ba sai da na kalli cikin idanun shi, har wani irin budewa dan bakin tsakiyar idanun shi yake tare da fitar da wani shegen maiko, ji nayi kafaffuna basu iya daukata, kirjina kuwa kamar ana buga min wani abu, ji nayi numfashina ina kokawa dashi, dan haka ban san lokacin da na zube a kirjin shi ba, mayafin da yake daure ne a k'ugun shi suka nemi zuɓewa kasa, cizon lebbena shi yayi cikin wani irin yanayi da bai san yana tare da shi ba, sai da na fada jikin shi, dan tsabar mugunta, janye jikin shi yayi na zube a gurin, sannan ya duba dakin babu wani abu sai alkyabar shi da Fudail ya dauko mishi, yafawa yayi sannan ya fito.

Mik'ewa suka yi tare da kallon shi.
"Sultan Mehran ya jikinka?"
Niman guri yayi tare da zama yana kallon gefen shi wanda yake dauke da kayan ciye ciye, a hankali ya motsa bakin shi kamar me fama da ciwon baki yace.
"Da sauki!"
Kallon shi suka yi, sannan suka sunkuyar da kansu. Gyaran murya Amir Hood da Mir Umdatuddawla yace.
"Sultan Aamaan Abdus Samad, mun tawo baki daya ne mu baka hakuri da!"

D'aga musu hannu yayi sannan ya kalle su daya bayan daya sannan nuna musu kofar fita, kan shi kwance saman matashin kujeran.

A hankali suka yi ta mik'ewa daya bayan daya, suna fita, karshe dai ya rage shi daya a falon, fitowa nayi ina ƙoƙarin shiga kitchen, bin bayana yayi da ido, ganin yadda na b'ata kayana da jini ya sashi dauke kai, bai ce min kome ba, har na gama abinda zan yi na fito na koma dakin, tasowa yayi tare da shigowa, wai zai gaya min abinda ya faru da jikina shine ya tako har inda nake tsaye, sai ji nayi an wurgani gado, na tashi da sauri. Ya kuma mai dani tare da zama a bakin gadon ya janyo kafana, a hankali ya ture ni ta daya gefen kyakyawan zanin gadon ne ya b'aci da jini, yana ganin na Fahimci haka ya mike tare da barin d'akin.

Saka kai na nayi a tsakanin cinyoyina, na rufe idanuna sa karfin tsiya. Ina sauke ajiyar zuciya. Tashi nayi na shiga wanka nayi sosai sannan na gyara jikina, ina gamawa na taso tare da nufar kitchen na daura mishi gasheshen nama sai madara da nayi gyaran shi. Na kawo mishi.

Tunda na kai dakin yana zaune tare da kallon yadda na gyara gadon tsaf, zama yayi ya fara cin abincin a hankali. Tunda na gama ya nutsu na fita daga dakin.
~~
Tunda Sultanah Hoyam taga ya sami sauki, ta shiga aiko mishi yan mata tsalla-tsalla. Wai suzo su dauke mishi kewa, sai dai abinda ka kasa Fahimta akan shi yan matan baya barin su, su shiga min dakin, sai dai kuma zai fito falo dasu ya zare kayan shi ya kwanta suna mishi tausa, dake Allah ya taimaka bana jimawa a cikin hailata, kwana hudu ne, lokacin ana sallah saura kwanaki ƙalilan za ayi.

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now