Page 37

180 28 1
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 37
A raunane ta kalle su, kafin ta juya ta bar falon, can lambu ta koma ta zauna, kallon juna Sultan Abrad yayi da Nawwas, sannan ya sauke ajiyar zuciya yace mishi.
"Wai da gaske kana son Ikram?"
Da mamaki yake kallon shi, abinda zuciyar shi take raya mishi ba kome bane kace Eh kome ta famjama famjam, amma ya kore tunanin haka ta hanyar amfani da hikima yace mishi.

"Haba ina babban kaya sai amale ai Ikram sai irinku saraki ba irin mu yardaddun ku ba, ai tafi karfina." Nawwas ya faɗa cikin girmamawa. Gyada kai yayi tare da kallon shi, sannan ya fashe da dariya yace mishi.
"Haba ai nasan kai ma wasa kake, manta da batun ta, muna zuba ido muga abinda ai faru".

   ~~~
SAMAIND

     Yau kwana biyu da fara bawa Yan matan da suka zo gurin Mehran horo, a cikin su har da Jasrah da Mahlika. Yaran Gwamnonin Yankunan shi. Sosai suke daukar abinda ake musu.

               Dan haka na maida hankali akan kaiwa da komowa duk abinda ake bukata daga gare shi, nice akan gaba.
"Ikram! Ana son magana dake a lambun tarihi"
"Ke Inam waye?"
Na tambaye ta kasa kasa,
"Wani ne wai Sarwat." Da sauri na juya baya na, tare da duba ko dakaru na biye dani.

Ajiyar zuciya na sauke tare da nufar Lambun tarihi. Da sauri.
Ina shiga na hango shi tsaye,  yana me juya min baya.
"Sarwat! Kasan kasadar da ka kawo kanka kuwa? Ina Noman din yake?"

Juyawa yayi ya zuba min ido, hautsina kayan cikina yayi ban san lokacin da amai yazo min ba, na toshe baki na.
"Meehhh! meehhh!! meehraan!!!"
Rufe baki na, nayi da sauri tare da fashewa da kuka, na zube akan gwiwata.
Durkusawa yayi  tare da d'ago kai na,
"Sabida bani da amfani shine kika manta da suna na! Noman Anwarulkharim! Shine cikekken sunan. Wakiliyar SULTAN Mehran. Nagode sosai, hakan ma Arziki ne. Ina kuma baki hakuri da abinda zan gaya miki, nazo ne mu koma gida.". Jan fasali yayi tare da kallona.

"Kiyi hakuri! Idan kin shirya ranar da zasu zab'e mishi matan shi, ranar zamu bar garin nan, sannan bazan miki dole ki bani ba, amma mahaifanki zan mai dake, dan kina da damar zama da Sultan Aamaan Mehran, ko zab'an zama da mutanen Gezira. Idan kuma na matsa miki, Kuma  kiyi hakuri, nagode."

        Rike hannun shi nayi tare da cewa.
"Ka rufa min asiri meye yasa kake bani hakuri, zan bika zan bika naga Airan. Zan bika naga gidan mu. Zan bika sabida kai ne kawai a zuciyata, wallahi babu ranar da rana zata fito ta fadi banyi kukan rashin ku ba, Noman ina kaunar ka, ko yau ka tashi mu tafi."

Girgiza kai yayi tare da cewa.
"Kiyi hakuri! Airan ta rasu."
Kukan ne ya tsaya min cak, baki na sake, wasu irin kwalla ne suke zuba min wannan bai sauka ba, wannan ya sauka, ban san lokacin da ya bar gurin ba, ina zaune baki a bude, na dimauce.

             D'ago ni aka yi, tare da juyar dani, baki na a sake. Ina kallon shi tare da dakarun da aka baza ana niman Noman, saka kai na yayi a kirjin shi tare da rungume ni, sai lokacin na sami damar sake ajiyar zuciya, me tafe da kuka. Sosai nake yi. Tunda nayi wannan kukan har mukan shiga cikin gidan, ban kuma kuka ba, hawaye na ne ya kafe tare da saukar min da zazzaɓi, sosai na kwanta babu lafiya.

  Tsawon kwana uku bana ko magana abin  duniya Dame shi..idan na kalle shi tausayi yake bani, dan haka ranar da na fara magana abinda nace mishi.
"Karka ajiye ni a cikin abubuwa masu kyau, Ni bakar kaddara ce! Ba lallai bane na zame maka farar aniya. Ina baka hakuri domin Ni ba mazauniya bace.

       Zanen Qaddara ta ce ta kawo ni daular ka, ko ina nan ko bani nan ka rike al'ummar ka, domin suna bukatar ka. Mehran mulki yana bukatar nutsuwa da fahimtar al'umma bai daya,  sai kuma ina rokon ka, ka amshi addinin Musulunci kai ma zaka ji dadin a ranka. Amma babu dole domin mulkin adalci koda ba musulmi bane Allah yana mishi jagora, mulki musulmi idan babu adalci Allah yana rusata!"

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now