Page 36

167 24 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 36

    Kidime na fara bin hanyar da naga ya bulla, da gudu gudu, sauri sauri. Har na kusan cimma shi tare da kiran sunan shi.
"NOMAN!!!!"
Na kwala mishi kira, fisgo ni aka yi da sauri na juya ina kallon shi, tare da juyawa nayi tare da kiran shi da cewa.
"NOMAN! Don Allah kazo." Kiran shi nake Mehran yana ja na, har yaga dai zan tara mishi jama'a, sakani barci yayi ta hanyar tab'a wuyana, sannan ya sabani a kafad'ar shi, muka shiga masarautan wanda babu nisa da kasuwan.
"Ka tabbatar ka nima shi, karka sake ya rayu!"

       Yana nufar kofar da zata kaika cikin farfajiyar dakaru ne a ko ina, suna ganin shi dauke da mace, suka shiga zuɓewa a gaban shi, har cikin gidan ya nufa da Ikram, ran shi na kara b'aci, tabbas lokaci yayi da zai dakatar da ita ga shiga harkan kowani namiji, tunda ya fahimci yanzun ta haɗu da wancan banzan.

         Haka ya ajiye ta, yayi ta yawo a turakar shi zuwa cikin falon shi, yana jiran Fudail. Kamar ya tafi yayi aikin da kanshi, amma babu halin haka yayi ta zuba mishi ido.
    --- Haka Fudail ya gama niman me kama da Noman bai samu ba, karshe dai ya dawo babu wani labari.

    ~~ Waiwaye.
Oman.
Zuba mishi ido Azizatul Nissah tayi tare da cewa.
"Kazo da al'amari me girma,  amma zan taimaka maka, domin  inda Ikram take ba sauki shiga gurin amma zan maka lamani daya, shine zan fita da kai ka gudu, ka tafi SAMAIND tana cikin fadar kasar, a matsayin baiwa. Amma maganar gaskiya Yayana da Nawwas cutarka zasu yi ba wai zasu bar maka ita bane.

   Yayana yana sonta, Ni kuma ina son Nawwas, shi kuma yana sonta, amma idan suka rasata zasu zauna lafiya sannan kai ma zaka same ta a cikin salama, idan kuma ka sake suka fahimci hakan tabbas zasu yi yunkurin kashe ka ne."

       Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Sarwat sannan yace mata.
"Na amince."
Haka kuwa suka shirya tare da fita bayan gari, karshe dai Noman da Sarwat suka gudu abin su..tafiyar da zasu yi a jirgin ruwa kwana biyu, sai gashi sunyi shi a cikin kwana ɗaya rak da wuni guda, ranar da suka shiga garin ranar Mehran ya dauki Ikram zuwa Madinatul Mah.

  Yaso ya bisu, amma babu halin haka. Domin Sarwat ya hana shi.
"Akan me zaka hanani bin bayanta?"
"Ikram tana tare da Sultan Aamaan! Idan ka sake ka bisu wallahi yagalgala namar ka zai yi, sannan kuma ya hanaka ita, d'azun naji wasu dakaru suna maganar cewa, ai dan ya bata Wakiliyar shi ce, Mahaifiyar shi ta azabtar da ita, dan haka baka san yadda aka yi har ya zame ta a matakin wakiliya ba, don Allah karka manta ni Maraya ne, daga kai sai ita nake dasu. Idan ka sake wani abu ya same ku, zan iya mutuwa."

    Kurawa Sarwat idanun yayi cikin tausayi, haka ya danne damuwar shi, har ya shiga fadar Sultan a matsayin me kula da dabobbin da ake ci, duk yana jin kome akan Mehran da Ikram,  yanayin da yaji labarin ne ya kashe mishi jiki, anya zata yarda ta dawo gare shi kuwa? Yadda kowa yake fadan albarkacin bakinsa.

       Lokacin da leken Mehran ya wuce a tunanin shi da ita suka wuce, sai daga baya ya lura babu kome a keken, shine ya juya tare da bin bayan inda keken ya fito, ya hango irin kallon da sukewa juna ita da Mehran, yaji zafin haka da kishinta, wato har ta manta dashi ta faɗa rayuwar wanin shi, yana nan yana dakin soyayyarta.

    Ko lokacin da ta hango shi kallon tsana da k'iyayyar yake mata, bawai kallon nazo gare ki mu koma bane.

            Shi yasa daga ta gan shi yayi maza ya b'acewa ganin ta, abin tausayi. Yana tafe hawaye na zuba daga idanun shi tare da danasanin akan zuwan shi da yabar ta kawai yasan Allah zai bashi wacce ta fita, amma haka ya dibo jiki ya tawo ba tare da sanin abin da take cikin shi ba.

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now