Concubines

447 55 12
                                    

*_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*

   _The Historical_
~BOOK ONE FREE~

*Ga masu nima babu tsada book 2,3, 500₦ abu na kuɗi abu ba kusa inji Bahaushe ba inji Ni ba! Da niman shi karfi da yaji Hajiya na, saya babu tsada 🙄*

Bismillah Rahamani Raheem

Page 3...

       "Karka ce zaka yi wani yunkurin! Masarautan nan cike yake da baƙar siyasa, idan ka sake wani shirme ya fito daga gare ka, zai zamewa kabilar mu abin kunya!"  Inji Amir Anas,

          Murmushi yayi sannan ya gyara zama, kafin yace.
"Kasan har yanzun bai gama gano meye silar mutuwar Sultanah Afeefah ba, dan haka kayi ƙoƙarin gano inda."

        "Amir Hood yana shigowa!" Inji Bafaden da yake bakin kofar shiga zauren tattaunawa, nasu na yarimomi masu jiran gado.

       Babban tashin hankalin su, kawo Baiwa da Sultan yayi cikin masarautar shine damuwar su,.idan so samu ne a fitar da ita daga jikin shi, domin suna da yakinin duk macen da ta fito ta jikin sarki karshe bala'i take zamewa masarautan, sannan kuma tana iya baza mulkinta na son ranta, dan haka suka fara nazarin yadda zasu tunkaro Sultan.

          ***
Kallon fuskarta yaƙe, yadda kwalla suka bushe a a saman fuskarta, shafa fuskarta yayi cikin nutsuwa, yana murmushi musamman yadda take ajiyar zuciya. Shi kanshi yasan cewa yayi mata bazata, domin ya saka mata karfi ainun.

    "Hoyam!" Gyara kwanciyar ta tayi sannan ta kuma lumshe idanun ta, sabida barcin da yake cike a idanunta. A hankali ya mike tare da barin gadon, ban daki ya shiga ya shirya kanshi.
Sannan ya fito, jin Rizwan yana buga mishi kofar shi ne ya sashi cewa.
"Hmm!"
Shigowa yayi sannan ya gaida Sultan.
"Manyan dattawan Fada suna son magana da kai. A zauren tattaunawa."
Bude wata takarda yayi ya dauki alkalami ya fara rubutu, yana gamawa. Ya mikawa Rizwan.
"Akwai wani mahayi zai tafi kasar Carboda ka bashi."

          Mik'ewa yayi tare da saka alkyaba, sannan ya saka kai zai fita, ya sami Narmin tana bakin kofar shashinsa, tare da wasu manyan masu tsaron lafiyar shi.
"Narmin ki kula da lafiyar ta."
Dukar da kai tayi sannan tace mishi.
"An gama Sultan."

      Suna barin shashin, ta shiga cikin da sauri, ta hango Hoyam, tana barci. Tashinta tayi ta fashe da kuka.
   
      Fita Narmin tayi tare da samun Shairah ta gaya mishi, zaro idanu yayi waje. Sannan ya kuma juya tare da niman Narjis ya gaya mata, take aka nimo masu kula da lafiyar matan masarautan, suka nufi har dakin Sultan, anan suka taimakawa Hoyam aka gyara ta sosai, sannan aka kuma dauketa zuwa Chamber na musamman, sakamakon ita din Zab'in Sultan ce.

               Sannan aka Narjis da Shairah suka nufi Shashin Sultanah suka gaya mata, murmushi tayi hawaye na zuba mata, tace.
"Ki bata bayi yan mata da zasu zauna da ita, kuma ku saka ido akanta, karku yarda ku.."

   "Na'am Sultanah!" Sannan suka fita, suna komawa aka duba bayi da kunyangi aka saka Narmin ta zab'esu sannan aka kai su Chamber din Hoyam, wacce take barcin gajiya domin babu abinda ba ayi mata na kulawa ba. Abinci ne kuma ana kawowa tace ta koshi a barta barci take ji.

**
Murmushi yayi tare da dauke kanshi, kafin ya kalle su kasancewar fuskar shi babu burbushin fara'a.
"Idan na fahimce ku, na zare ta daga cikin rayuwata, bayan kusan haka ba sauki ne a gare Ni ba, sannan kun dauko min labarin karni masu yawa, wato babban karni, na rabu da Hoyam sabida karta haifi namiji ta kwace masarautan ko ba haka ba?"

   Maida kanshi yayi sannan ya kalli Ubaidullahi. Aminin shi na kut da kutt, ya kuma lumshe idanun shi, sannan ya ce mishi.
"Ubaidullahi! Me zaka ce?"
Shiru suka yi sannan yace.
"Ai duk abinda ka zab'e naka ne, kuma muradinka ce, dan haka umarni zaka bani."

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now