Page 38

193 29 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 38

"Sai na Fahimci ashe bazan iya wannan b'arnan ba, domin Mehran ya d'aga muryan shi sabida ke? Ya kuma ragewa Hoyam matsayinta tare da rage na mahaifina. Ikram na Fahimci kin yin min abinda ban ma saka ki ba, Nagode sosai. Amma ki sani baki gama aikinki ba, domin akwai mutanen da sun shigo domin daukar fansa da laifin da nayi akan Mehran."

Hawaye ne ya zubo min tare da rike hannunta, bakina ya gaza furta kome kallon ta nake a hankali ta cigaba da cewa.
"Sun dauke Jasrah na kawo ta ne domin tayi min aikin da kika yi sai na fahimci bata da bushewar zuciya irin naki.

Bata da kome bata da kwarjini da kamala, bata da nutsuwar zuciya da ruhi, na san nayi laifi masu girma, tun daga ganin ki na fahimci kece zaki share min kuka na, amma ban tab'a sanin cewa kina da naki rayuwar ba, na zata idan kika zama makusanciya da shi zai sanya ki manta kome da kome ki fuskanci wata rayuwa, sai na Fahimci ba haka ba.

Mehran yana rayuwa ne ba tare da yasan me yake yi ba, Mehran yana rayuwa ne ba tare da ya gane halin rayuwa ba, amma haduwar shi dake ya sanya fahimtar darajar da Allah yayi mishi. Shairah, zo ka mata bayanin yadda zata fahimta."

"Ba zan fahimci sakon da zata shiga bayan wanda zuciyata take ciki, don Allah karki kara labta min azabar da nake ciki. Me yasa sai ni? Me yasa ba zaki zabi wata tayi miji aikin ba sai ni? Wato mareniya wacce bata da gata da galihu na shigo tsakanin ku kuna gwara kai na, meye nayi muka haka ne?

Me yasa na fito karamar ahali, shin kuskure na ne ko Kuskuren kaddarata ce, me yasa kowa yake son cillani wata rayuwa na daban, meye laifin rayuwata?"

Na fada da karfi ina kuka, tare da shasheka, na rasa Uwa na rasa Uba, na rasa kome nawa, sai yau kalaman Ummina yake dawo min da tace.
'''Bilqusul Ikram! Duniya tana da fadi da yawa, ƙaddara mace ce da ba a san me zata haifar ba, ina ji a jikina bai zama dole na amfanar da gaba ba, amma tabbas rahamar Ubangiji yana bibiye da rayuwar wanda yayi imani dashi
Karki manta! Halayyar da dabi'u suna tafiya ne kunnen doki, gashi ba zan kai ba balle nace zan so ki rayu kamar sarauniya! Zan so naga yadda zaki amshi karfin mulkin'''

Ajiyar zuciya na sauke tare da kallon kasa, hawaye na zuba min, abinci ta ajiye min da kanta tare da zama a gabana, wanke hannun tayi sannan ta fara diban abincin wanda aka dafa shi da nikekken nama, tana bani a baki hawaye na zuba min, itama haka. Tare da kallon yadda idanuna suke zubda kwalla.
"Ya kamata na cire wannan abun ki huta kema, ki rayu kamar sarauniya! Kinsan me ake kira da mulki? Ki zama sarauniya yana nufin ki adana darajar ki da budurcin ki ga sarki ne! Ina son ranar da ya amshi budurcin ki ya zama itace ranar da za a kiraki Sultanah Bilqisul Ikram Mustapha, ina son wacce ta iya fitowa daga yankin gabashin sahara ta mulke fararren fatan wannan yankin.

Ina son izzar da nake hangowa da ikon nan ya tabbata akan ki, zama Magajiyar sarauta ba abu ne me sauki ba, idan har zai zo da sauki toh ina rokon Arzikin kar a tab'a kimar yaron can! Kar wani namijin ya kusanci nahiyar shi, ba dan Ni ba, ba dan na isa ba, ina rokon a kare budurcin shi domin cikar muradin mu, so nake ki wargaza."

"Hmm!" Na fara dariya ina kallon ta, tare da cewa.
"Na wargaza rayuwar su, ki wargaza nawa. Bayan nasan kome akan ku ahalin Abbasiyyah, cin amana yafi yankan takobi kaifi a cikin zuciyar ku, cin amana yafi kome faruwa a cikin gidan nan..
Wata goma sha daya nayi ina zaune daga nan zuwa nan har na isa shashin Sultan Mehran, yau kice zaki min farar dabara."

"Akul Ikram! Kamar yadda zuciyar ki take cikin kauna da bege haka itama nata zuciyar take kwana da begen shi, taya hakan zai kawo karshen rikicin masarautan nan? Sultanah Fazilatul nisa ce a gaban ki kike gaya mata maganar da tafito bakin ki?"

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now