Page 25

162 29 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 25

Zare mayafin yayi, tare da kura min ido, cire hular kan shi yayi tare da mai da gashin kan shi baya.

A karon farko da muka kalli cikin idanun juna, tare da dauke kan shi kamar bai damu ba, kawai sai ji nayi ya buge hannu na, tare da kaiwa kafana duka, zai kwashe ni, mayafin da ya wular nayi maza na fada kai tare da dukar kujeran da yake zama ya shura mishi.

Tarewa yayi da kafar shi, sannan ya tako gabana, Allah ya taimake ni na dauki karamin wukar yanka tuffa, kamar yadda ya kawo min sara, a dokin wuya na, haka na kai mishi wukar wukar a kirjin shi, sai da ta huda Sulken jikin shi tare da tab'a fatar shi ta ratsa har zuwa tsokar kirjin shi, rike hannu na yayi tare da sake takobin shi. Yana kallon fuskana.

Jinin da yake zuba akan farin jallabiyar. Wani irin tsoro ne ya kamani, na kasa cire hannun kuma na kasa daina tura mishi wukar.
"Zaki kashe ni!"
Ya faɗa a sanyayye, wani irin rawa jikina ya dauka lokaci guda nayi baya da wukar tare da zare shi a kirjin shi, zuɓewa yayi a jikina, jini na zuba kamar an bude kofar ruwa. A hankali ya shiga zamewa daga jikina, wani irin rawa cikina ya dauka tare da bin shi da ido, wancan lokacin da na hadu da mutumin dajin nan ya dawo min, jin shi nake kamar a lokacin ne muka hadu da mutumin da nake son na kuma gani.
*NOMAN!!!*
Zuciyata ta ambata, da sauri na ture shi ya fadi kasa, nima jikina ya dauki rawa, a karo na babu adadi. Wani irin kuka ne yazo min lokaci guda na mikewar nayi zan fita da gudu naji ya fisgo ni. Mutumin nan dan duniya ne. Idanun shi a rufe, rike Ni yayi gam kuma yana kwance babu alamar numfashin sa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji ka cece ni kar nayi kisan kai wallahi kashe ni zasu yi,Wayyo Allah Kanwata Airan."

Bai sake ni ba duk da kokuwar da nake yi, dashi fisgo ni yayi kan shi tare da, kifani akan shi.
"Wayy..."
Hannun shi ya saka tare da d'anne min bakina, sai da ya nace.
"Wash"
Daidai shigowar Fudail da Darakshan, sai Mahaifiyar shi, sake matsa bakin yayi nace.
"Ashhhh!"
Da sauri suka juya, sannan ya kuma make min bakin fashe da wani shakakken kuka nace.
"Wayyo Allah na, na tuba ka bar ni haka."
"Uhmmmm!"
Da sauri Mahaifiyar shi ta bar gidan, tare da jadadda musu cewa su tabbatar idan ya gama tana niman shi.

A cikin kuwa kamar yadda na ji mishi ciwo haka Mehran yayi ta lugude da bakina, sai da yaga jini na diga sannan ya ture ni, na bugu da jikin pillar dakin, dif na dauke wuta.

Sakamakon buguwar da nayi, wanda ya haifar da suma na, bai damu ba, tashi yayi tare da nufar dakin shi, ya isa har cikin ban dakin shi ya cire kayan shi, tare kallon inda wukar ta lume, sai da ya wanke ciwon tass sannan ya dauki magani ya shafa tare da rufe gurin, ya saka wata riga, ya fito dakin shi ya kwanta.
*Me yasa ta shigo rayuwar shi? Me yasa yake jin kome irin na wancan yarinyar da ya hadu da ita a dokan daji? Me yasa take mishi kallon abubuwa dayawa? Toh waye Allah nan da ta damu dashi ne haka? Me yasa take ce mishi bai sallah bai azumi? Toh su din Sallah da Azumin me yasa ake yin su?*
Duk wannan tambayar da yake bai da amsar su don itace zata bashi su. Lumshe idanun shi yayi yana zane hoton fuskar wancan da ya hadu da ita cikin daren nan, wancan Yarinyar tana da fuska me dan tsawo, sannan a tsaye ba zata wuce wannan ta cikin gidan shi ba.

Gyada kai yake yana kuma tuno kusancin da ya shiga tsakanin su d'azun nan,ji yayi wandon shi yana harbib iska, ba tare da ya sani ba, sai jin yayi tsinkekken ruwa daga jikin shi tana zuba daga gurin, lumshe idanun shi yayi, a yanzun ya aci ace yana da iyalin kan shi, koda bai yi aure ba ace yana da matar da zata dauke bukatar shi a matsayin shi na namijin duniya.

Da wannan tunanin ya shiga barci.
~
A can fada kuwa, ba tare da sanin shi ba aka shiga kara haraji tare da cutar da talakawa babu ji babu gani,. Ana ladsbtar da kai dan dole, sannan ana bin mutane gida ana amso kayan da suka noma karfi da yaji.

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now