Page 27

178 22 0
                                    

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Page 27
Daga cikin mutanen da aka tafi da yaran su, sunyi kokarin taimakawa da gudummawar su, na magani amma babu nasara, asalima sai muke ga babu wani canji,

Dan haka na kalli Lingesa nace Mishi.
"Zan sami Hulba da habbatul saudat! Sai y'ay'an zaitun!"

"Zaki samu!" Muka juya zamu fita, finciko Ni, Sultanah Hoyame tayi tare da cewa.
"Idan Sultan MEHRAN ya mutu gawarki ba za'a same ta bama balle ke din."

Ban kulata ba, muka fita, cikin gaggawa nasa aka nika min hulbar, sannan na zuba mata ruwan zafi na sannan na kuma dafa wani hulban da Habbatul saudat tare da garin zaitun, na zuba a wani ƙaramin buta, sannan muka nufi dakin shi, muna zuwa. Ka bude min cikin shi na zuba kwab'abben hulban sannan na saka suka d'aga shi yasha.

Sannan muka koma gefe muna jiran abinda Allah zai yi, kasa nutsuwa nayi na nufi waje nayi Alola tare da gabatar da sallah, sannan na dawo bakina dauke da kirariwa Ubangiji na. Sun bani damar nan da kwana biyu idan babu canji zasu nimo wani taimakon. Dake ana ta jaraba masu maganin, muna gurin Sai ga Narmin da wata matashiyar budurwa, cikin wani irin shiga tazo duba shi. Kus-kus suka yi da Sultanah da Narmin sannan ta kalle mu, kafin tace mana.

"Zaku iya bata guri zata yi aikinta." Kallon ta nayi haka kawai naji raina bai kwanta da ita ba, juyawa muka yi zamu fita sannan na juya na kalle ta, sam bata da gaskiya ko na miskala zarra, haka muka fita ban san me suka yi da Sultanah Hoyam ba itama ta fito.


Tunda suka kawo me maganin nan bana ce ba, amma jikin Mehran babu yadda yake, kullum zata zo da safe, zata zo da dare. Wai tana bashi magani. Haka kawai na shiga dakin tare da d'aga ciwon amadadin gurin ya kame sai ma ya kama ci kamar ana tab'a shi, dan haka bayan tafiyar da dare, kawai na fita har shsshin bayi na samo lalle da kashin shanu, sai Hulba da Habbatul saudat da zaitun. Na saka na hada tare da zuba Mishi ruwan zam-zam wanda na samu a gurin Narmin, sannan nazo na kwab'a na zuba a gurin ciwon.

Idan akwai bakin sihiri sanadin kashin shanuwan nan zai nuna, idan kuma guba ce zata motar gurin, idan kuma dajine ma zai nuna alamar shi, dan haka ina sakawa na tsaya a dakin har asuba na tashi nayi sahoor, sannan na duba ciwon, wasu irin tsutsa suka cika saman maganin, fita nayi na kira Fudail yazo muka kwashe tass, sannan yace min.
"Me ya faru?"
"Kwashe maganin wancan matar nayi, sannan na saka mishi wanda nagada a gurin mahaifina, Insha Allah zuwa gobe da yamma ciwon zai kame, sai dai ina son son Allah a hanata shigowa domin kuwa."

"Baki da lafiya! Ba zai yiwu ba, kawai ki kyale ta tayi abinda taga zata iya! Kema kiyi wanda zaki iya. Bana son kusancin ku yana."

Rike k'uguna nayi tare da sauke gwaron numfashi sannan nace mata.
"Baka da lissafi! Taya ina ganin tana cutar shi zan."
Fisgo ni yayi tare da Hadani da bangon dakin, yana huci duk kowani dakika ji nake kamar zuciyata zata buga idan na fahimci yadda kike kai Gwauro ki kai mari, a gaban Mehran ji nake kamar na kashe kowa na hana shi ganin ki.

Me yasa ba zaki Fahimci yadda zuciyata take kaunark..."
Girgiza kai nayi wani irin kuka yason taso min, na shiga cewa.
"Zuciyarka bata maka adalci ba, bata maka adalci ba, bata maka adalci ba, tuntuni ina da wanda nake kare kaina domin shi, kabawa zuciyarka hakuri akwai wanda yayi dashe a cikin tawa, bana jin har abada zan iya samun sama dashi don Allah ka rabu dani."

Na kwace hannuna tare da juyawa na fita daga d'akin, wani lungu na shiga tare da tsugunawa na fashe da kuka, sama da yadda nake jin zuciyata take min, me yasa nake fuskarta wannan matsalar?,shi me yasa maza suke kowa min farmaki da tallar kaunar su? Shin Ni daya ce mace ko kuma akwai wasu matan da su ba zasu je gare su ba?

ᎠᎪႮᏞᎪᎻ.. 𝘉𝘐𝘠𝘜!!!   dynasty'sWhere stories live. Discover now