Jasmine Baturiyya ce

By Amiratuoo

117K 8.8K 1.4K

Completed (Currently Editing and Re-uploading) JASMINE haifafiyar kasar ingila (England) ce. Ya'a ga hamshaki... More

🌷JASMINE🌷
🌷Shafi na 1🌷
🌷Shafi na 2🌷
🌷Shafi na 3🌷
🌷Shafi na 4🌷
🌷Shafi na 5🌷
🌷Shafi na 6🌷
🌷Shafi na 7🌷
🌷Shafi na 8🌷
🌷Shafi na 9🌷
🌷Shafi na 10🌷
🌷Shafi na 11🌷
🌷Shafi na 12🌷
🌷Shafi na 13🌷
🌷Shafi na 14🌷
🌷Shafi na 15🌷
🌷Shafi na 16🌷
🌷Shafi na 17🌷
🌷Shafi na 18🌷
🌷Shafi na 19🌷
🌷Shafi na 20🌷
🌷Shafi na 21🌷
🌷Shafi na 22🌷
🌷Shafi na 23🌷
🌷Shafi na 24🌷
🌷Shafi na 25🌷
🌷Shafi na 26🌷
🌷Shafi na 27🌷
🌷Shafi na 28🌷
🌷Shafi na 29🌷
🌷Shafi na 30🌷
🌷Shafi na 31 🌷
🌷Shafi na 32 🌷
🌷Shafi na 33🌷
🌷Shafi na 35🌷
🌷Shafi na 36🌷
🌷Shafi na 37🌷
🌷Shafi na 38🌷
🌷Shafi na 39🌷
🌷Shafi na 40🌷
🌷Shafi na 41🌷
🌷Shafi na 42🌷
🌷Shafi na 43🌷
🌷Shafi na 44🌷
🌷Shafi na 45🌷
🌷Shafi na 46🌷
🌷Shafi na 47🌷
🌷Shafi na 48🌷
🌷Shafi na 49🌷
🌷Shafi na 50🌷
🌷Shafi na 51🌷
🌷Shafi na 52🌷
🌷Shafi na 53 🌷

🌷Shafi na 34 🌷

1.3K 127 33
By Amiratuoo

Kamshin girki da Jasmine taji ne yasa tayi hanyar kitchen dinsu. Tana shiga ta tarar da Alamin a gaban gas cooker yana zuba kwai acikin frying pan. Murmushi tayi ta karasa inda yake sannan tace "Good morning,"

"Morning Love," Amsa Alamin ya bata bah tare da ya juyo ba.
"Girki kake yi?"

Fuskarsa dauke da murmushi ya juyo ya jingina a jikin counter kitchen din sannan yace mata "Yeah, I wanted to suprise my wife with breakfast,"

Girgiza kai Jasmine tayi tana murmushi tace "That's so nice of you, lallai kana ji da matar nan taka. Me kake dafa mata?"

"Pancake, toasted bread and omelettes, daga wannan na gama." Ya bata amsa yana juya wainar.

Setting din dinning table Jasmine ta taya Alamin sannan taje ta hada fruit juice din zata sha. Suna fara cin breakfast din Alamin ya tambayeta "Do you like it?"

Murmushi tayi tace "I love it, yayi dadi sosai and you have finally convinced me ka iya girki,"

Dariya Alamin yayi yace "Da ma baki yarda da kwarewata?"

"Ina? ba haka nake nufi ba, kawai dai ka kara tabbatar da kwarewar taka ne." Jasmine ida maganarta tare da kurbar ruwan lemonta sannan ta kara cewa "Yau zan koma Hospital wajen su Khadija, I was thinking about girka masu abincin rana na kai masu tunda na san an riga da an kai masu abinci safe,"

Girgiza kai Alamin yayi yace "Hakan yayi, karfe nawa zaki tafi sai muje tare, kinga daman yau Doctor yace za'a sallami Khadija,"

"Okay, daman ita bata ji ciwo ba sosai. wajen karfe sha biyu 12:00 haka zanje na kai masu da wuri,"

"Okay, Yaushe zakiyi girkin na taya ki ko ba kya so taimakon kwareren mai girki," Alamin ya tambayeta cikin zolaya.

Daga gira daya Jasmine tayi tana kallonsa, cikin tsokana itama tace "Wato dan Allah ya taimake ka kayi pancake ba tare da ya kone ba shine ka zama kwareren Chef?"

"Wato dai kin janye maganarki ta dazu,"

Dariya tayi tace "Something like that," ajiye fork din hannuta tayi ta cigaba da cewa "And Ina tunanin chan bangaren zanyi girki saboda da dan yawa zanyi, zan kaiwa sauran patients  din ma."

"Hakan yayi kyau," kawai Alamin yace sannan ya cigaba da cin abincinsa bai kara cewa komai ba.

Dago idanunta Jasmine ta kalleshi ya cin abinci tace "Yau baza ka wajen aiki bane?"

"Kin gaji da ganina ne?" Ya tambayeta tare da saka idanunsa acikin nata.

Kasa Jasmine tayi da kwayar idanunta tace "Aa, I'm just asking naga da safe kake fita,"

"Well, yau babu inda zani I want to spend the day with my lovely Wife,"
Murmushi tayi ta ajiye glass cup din da ke hannunta sannan ta mike tare da daukar plate dinta sannan tace "Kash, sai dai lovely Wife din taka tana da aikin yi yau,"

"Ina zaki," Alamin ya mike tsaye shima yana kallonta.

"Ka manta aiki girki zanje na fara,"
"Tun yanzu? Bai yi safiya ba," Alamin ya tambayeta yana hade girarsa.

"Aa, karfe 9:30 fa," Ta bashi amsa tana duba Iwatch din da yake hannunta.
Alamin bai samu damar taya Jasmine aikin girkin ba saboda a bangaren su Hajiya Kaka taje yin aikin sannan ba ita kadai tayi aikin ba ma'aikatan Kitchen din na tayata yin girkin. Haka yayi ta zama shi kaɗai yana jiranta.
Daman ya ki fita aiki ne da niyar ya zauna a gida su wuni tare, abunda ya dade bai yi ba tunda ya fara gina kamfaninsa kusan shekara tara 9 kenan. Gashi  Allah ya daukaka masa kamfanin yanzu, shi kansa yana son hutu sai dai bashi da damar hutawa saboda yawan ayuka, mussamman da ya fara kula da kasuwancin mahaifinsa ayukan sun kara yi masa yawa, bayan ya hade business dinsa da na mahaifinsa sun koma daya ayyukan sun ragu ta wani fanin sannan sun karu ta wani fanin. Meetings guda uku ya soke saboda ya zauna a gida tare da Jasmine duk da ba ranar karshen mako bace. Alamin ji yake akan Jasmine babu abunda ba zai iya rabuwa da shi ba da tsaf zai iya bada duk abunda ya mallaka muddin Jasmine zata zauna tare da shi.

********

A tare Jasmine da Alamin suka shiga cikin asibitin suna tafiya ajere gwanin ban sha'awa har suka karasa male ward suka duba drivers din Khadija da Hajiya Saudat. Daga nan suka wuce female ward dakin Khadija, suna zuwa suka tarar bata nan ta tafi wajen mamanta. Haka suka kama hanyar dakin Hajiya Saudat. Da sallama suka shiga dakin, mahaifiyar Nadia ce ta amsa masu cike da fara'a, Khadija suka hango kwance akan wata doguwar kujera tana bacci, dakin cike yake da yan uwan Hajiya Saudat, Gaisawa suka yi cikin mutunci suka bawa Alamin da Jasmine wurin zama. Alamin na zaunawa wayarsa ta fara kara, zaro ta yayi daga Aljihu ya duba sannan ya mike tsaye ya fita, bai jima da fita ba ya dawo ciki, kusa da Jasmine ya matsa sannan yace mata "Something came up a office, I have to go love, zaki bini office din ko nasa a maida ke gida."

Girgiza kai Jasmine tayi tace "No, ka barni a nan, Jan jira Khadija ta tashi and Basma ma ta taho sai mu koma tare da ita,"

"Okay, take care." Sallama Alamin yayiwa yan dakin kafin ya juya ya fita.
Shiru Jasmine ta zauna tana kallonsu suna hira babu wanda ya kulata acikinsu, Muryoyi suka fara ji a kofar dakin kafin Nadia da Cousins dinta suka shigo. Basma ta gani a cikinsu hakan yasa tayi murmushin jin dadi daman ta gaji da zama ita kaɗai. Karasowa inda Jasmine take zaune Basma tayi ta zauna a kusa da ita suka fara gaisawa.

Mata hudun da Jasmine ta tarar a dakin ne suka tashi zasu tafi, Maman Nadia ta bisu  suka fita tare zata rakasu. Daga Hajiya Saudat da Khadija da suke Bacci sai Jasmine, Basma, Nadia da Cousins dinta guda biyar ya rage a dakin.

"Nifa a rayuwata idan akwai mutumin da na tsana to mai cin amana, snatchers kenan," Murya Nadia taji tana magana sai dai bata tanka mata da ko kala Jasmine bata ce bah.

Wata daga cikin yanuwan Nadia ce ta kara da "Ke dai bari, sai ki gansu limi limi kamar mutanen arziki amma munafikai ne. Ni har yanzu na kasa gane wani irin rashin daraja ne da za'ayi yi auren mutum babu dan uwansa ko da ko mutum biyar ne,"

"Kika sani koh neman kai ake da mutum, daman chan ta riga ta gama yawon ta zubar," Shewa suka yi suka tafa cike da nishadi.

Gyra zama Nadia tayi tana hararar Jasmine da ke danne danne a wayarta tace "Uhmm, ai ba wannan neh abun mamakin bah, Auren ko wata biyu bai ba fa ta fara amaye amaye duk yadda akai ma da abunta ta zo."

Dagowa Jasmine tayi ta kalli Nadia dan kalamanta sun so su bata dariya wai har kura ce zata cewa kare maye. Kuma ita da sau daya ma ta taba ganin Alamin din kafin wannan auren nasu na bogi, murmushi kawai tayi ta cigaba da dana wayarta.

Kwafa Nadia tayi ganin Jasmine bata tanka masu ba yadda taso, "Miko min kulolin chan naga me kariyar nan ta kawo mana,"

Hade rai Basma tayi da jin kalaman da Nadia ke jefawa Jasmine, cikin fushi tace "Haba Anty Nadia, ko ma me ya ke tsakaninki da Jasmine tunda ta auri Yaya Alamin ai bai kamata kina jifanta da irin wannan muggayen kalamai ba, Ko bah komai ai matar yayanmu ce,"

"Ke dalla rufe min baki wacca bata san ciwon kanta ba," tsawa Nadia ta dakawa Basma "Koh rashin kunya zaki min!"

Basma ta bude baki zatayi magana Jasmine ta hana ta. Harararsu Nadia tayi tace "Ai da kin kyaleta na hada ku duk na koya muku hankali,"

Bude kular abincin da Jasmine ta kawo suka yi, tuni kamfin Fish Pepper Soup ya cika dakin, Ya tsine fuska Nadia tayi tace "Karima, dandana mana kiji koh ta sa wani abun, tunda munci sa'a ba naman Alade ta kawo ba,"

Chokali Karima ta dauka ta debi soup din tana kaiwa baki Nadia ta kashe mata ido, da karfi ta furzar da na bakinta cikin na kular. Tuntsurewa da dariya sukayi kafin Karima tace "Abinci sai kace na gidan yari anya ko bah ta zuba wani abu aciki bah, dan ji nake kamar nasha ruwan battery." Janyo daya kular sukayi suka bude Chicken Biryani Rice ce aciki itama kamshin ta cika dakin yayi. Ya tsina fuska Nadia tayi ta yi tsaki sannan tace "Allah ya kiyaye mu ci wannan jawalgwalon naki," Yawu ta tofa aciki sannan tace "Ku fita da abincin nan ku zubar dan ko kare bazai ci wannan kazantar ba,"

Ran Jasmine yayi matukar bacci duk da tayi niyar sharesu kasa jurewa tayi tace "Haba Nadia, ba fa ke na kawowa abinci nan ba, wacce na kawowa ko gani batayi yi ba kin bata shi, kina Muslima ai kin san haramun ne almabazanatar da abinci,"

Tafi Nadia ta fara yi kafin ta tuntsure da dariya tace "Yau kuma ni tubabbiya zata yiwa wa'azi, ki bari addinin ya isheki tukun kafin ki bude arnen bakin nan naki kiyi min wa'azi,"

Mikewa tsaye Jasmine tayi itama Nadia ta mike tare da cigaba da ce "Koh kin dauka bamu san tarihinki bane, duk danginku arna neh. Babanki mah ai a arnanci ya mutu,"

Tas kake ji karar mari kafin wani tas din ya kara biyowa, kumatu biyu Nadia ta rike tana kallon Jasmine. Idanun Jasmine sunyi kore  sosai saboda tsananin baccin rai juyawa tayi ta fita daga dakin batare da tace komai ba ta bar Nadia rike da kunci da kuma mamakin marin da tayi mata.

Basma ce ta fito da gudu ta biyo Jasmine amma bata ganta ba, babu inda bata duba ba hakan yasa ta kira  Alamin cikin gaggawa, asibitin ya dawo cikin hanzari, ta bashi labarin duk abunda ya faru. Cikin fushi ya shiga dakin da aka kwantar da Hajiya Saudat. "Nadia, Nadia," Da karfi yake kiran sunanta shi gabki daya mah ya manta tana dauke da juna biyu. Mikewa Nadia tayi jikinta yana rawa saboda irin bacin ran da ta gani a fuskar Alamin, kafin yace komai ya fara dauketa da mari.

****

Jasmine na zaune akan kujera Alamin ya shigo falo da sallama, fuskarta dauke da murmushi ta amsa kamar bata dade da gama kuka ba. A hankali Alamin ya karaso inda take hannusa dake boye a bayansa ya fito da shi dauke da flowers ya mika mata. Wani kayataccen murmushi Jasmine tayi tace masa "Thank you," sannan ta kai flower kusa da hancinta ta kara cewa "It's so beautiful, Thank you," Dago da idanunta tayi taga Alamin yana yi mata hoto, "What are you doing?"  ta tambaye shi tare da ajiye flowers din a gefenta.

A kusa da ita Alamin ya zauna ba tare da ya bata amsa bah ya cigaba ta kallonta, hakan yasa ta da matsa daga kusa da shi tare da yi murmushi sannan ta kara ce masa "Why are you looking at me like that?"

Murmushi Alamin yayi ya jingina ajikin kujerar da su ke zaune ya lumshe idanunsa yana tunanin irin wulancin da Basma tace su Nadia sun yi mata, shi ya dauka zai dawo ya tarar da ita tana kuka koh kuma zata kawo kararsu wajensa sai gashi bata yi ko daya daga cikin abubuwan da yake tunanin bah, hasali ma da murmushi ta tarbeshi da ya dawo. Ba tare da ya bude idanunsa ba Alamin yace mata "Laifi ne idan na dauki hoton kyakyawar matata,"

Shiru Jasmine tayi tana murmushi bata ce komai ba, Alamin ya cigaba da cewa "Na dauka yau will be different, tunda nayi clearing din schedule dina na wannan sati, I'm sorry for leaving you at the hospital,"

Juyawa Jasmine tayi ta kalleshi idannunsa a lumshe, gani tayi ya kara kyau a idonta hakan yasa murmushi fuskarta ya kara fadada tace "Babu komai, ai emergency neh. Amma still kana bukatar hutu M." Hannuta Jasmine ta dora akan goshin Alamin da taga gumi a akai duk da sayin AC da ya cika falon. Sanyin hannunta da yaji a kansa ne yasa ya bude idanunsa ya sauke so akan fuskarta. "Kanka ya dau zafi and you're sweating? Baka da lafiya ne?"

Girgiza kai Alamin yayi alamar Aa bata tare da yace komai bah, hakan yasa Jasmine ta cigaba da cewa " Kamata yayi ka tafi hutu M, koh na sati biyu neh ka huta you can go to Mauritius ko Maldives it's a nice place for vacation,"

Wani kayatacen murmushi Alamin yayi dimple dinsa ya lotsa sosai, a hankali ya dora idanunsa akan na Jasmine yace "Zanje, amma sai dai mu tafi tare,"

Da sauri Jasmine ta dauke hannunta da ta manta akan goshinsa sannan ta dauke fuskantar ba tare da tace komai ba, hannu Alamin yasa ya juyo da fuskarta tana kallonsa tare da dagowa daga jikin kujerar. Da sauri Jasmine ta mike tsaye ta juya zata bar wajen, rike mata hannu Alamin yayi yace "Ina Zaki?"

"Kitchen, zan sa flowers dinnan a cikin ruwa," Jasmine ta bashi amsa tare da daukar flowers din da ya kawo mata "Sannan zanyi girki,"
Murmushi Alamin yayi yace "Girkin dare zaki yi mana,"

Girgiza kai Jasmine tayi tace "Eh," hakan yasa Alamin ya sake mata hannu tare da mikewa tsaye.

Yana kallonta ta shige Kitchen din sannan shikuma ya nufi kafar bene.
Jasmine na juya yankanken kayan miyan da take soyawa taji motsin mutum a bayanta, murmushi tayi da jin kamshin turare ya cika Kitchen din, kin juyawa tayi saboda tasan Alamin. Hannayesa Alamin ya saka a kugunta ya rungumeta ta baya ya saka hancinsa acikin gashinta, lumshe idanunsa yayi yana shakar kamshin da gashinta yake yi. A hankali ya bude idanunsa sannan ya sa hannu ya fara warware mata braid din da tayiwa gashinta. Da sauri ta juyo hakan yasa Alamin janye ta daga wajen gas cooker zuwa jinkin kitchen counter. Hannu daya ya sa ya rike ta da ita dayan kuma a cikin gashin ta. "Daga masa gira daya tayi tace "What are you doing M,"

Kafadunsa biyu Alamin ya daga alamar babu komai kafin yace "Aiki nake so na taya ki,"

"Amma ai wannan ai ba taya ni aiki kake ba, hanani aiki kake kokarin yi, you are distracting me," Ta kare maganarta tare da saka hannunta ta cire hannunsa da yake jinkinta.

Matsowa kusa da ita Alamin ya kara yi hakan yasa ta saka hannuta akan kirjinsa dan kar ya kara matsowa kusa da ita. Murmushi Alamin yayi ya kalli hannunta da ke kan kirjinsa sannan yace "Really? am I that distractive?"

"Idan aiki zaka taya ni, ka soya min wannan ni kuma zan kwaba flour (filawa) din chan,"

"Okay," kawai Alamin yace ya matsa ya je ya wanke hannunsa sannan ya koma wajen gas din ya fara juya kayan miyan da ke kai, hakan yasa Jasmine yin murmushi itama ta wuce ta fara hada kayan kwaba filawar.
"Kayan miyan naki ya soyu fa,"

"Okay, ka sauke shi. Na gama,"

Alamin na saukewa ya kashe Gas Cooker sannan ya dawo inda take kwaba filawa, a bayanta ya tsaya ya karasa warware mata kitson kan ta. Juyowa Jasmine tayi ta galla masa harare tace "Kasan wahalar yin braiding dinnan ka kunce min,"

Dariya ta bawa Alamin ganin yadda tayi kicinkicin da fuska, cikin dariyar yace "I like your hair like this,"

Kwafa tayi ta juya, cikin hanzari ta dauki kwanon da ta debo fulawa ta juye gaba daya filawar a kansa. Mamaki ne ya hana Alamin motsin dan bazata tayi masa, dariyar Jasmine ce ta dawo matsa da hankalinsa kanta "Nima I like you like this," Ta faɗa cikin dariya. Murmushin mugunta Alamin yayi cikin zafin nama ya mika hannu zai kamota, ihu Jasmine ta danyi ta kauce, dariya Alamin ya yayi ganin yadda ta fita daga kitchen din da gudu ya biyo ta da gudun yana kokarin kamata.

Tiris Jasmine tayi ta tsaya ganin Nadia da Cousins dinta zaune a falon, Alamin da bai gansu ba yana karasowa ya janyo Jasmine, ganin batayi kokarin guduwa ba yasa ya kalli inda take kallo, kannensa ya gani zaune, shi har ya manta ya ce su zo. A hankali ya saki Jasmine sannan ya wuce sama ba tare da yace masu komai ba.

Wata irin muguwar harara Nadia ke watsa wa Jasmine da ke tsaye bata motsa ba. Jin tsanar Jasmine take yana kara ratsawa acikin ranta mussamman ma da tazo taga suna wasa da Yaya Alamin dinta, ji tayi kamar ta saka kuka saboda bakin ciki. Wai yaushe ma Yaya Alamin ya san Jasmine dinnan da har suke irin wannan soyayyar? Ko dama chan budurwarsa ce? Idan ta zauna tana tunanin yadda abubuwa suka faru komai mamaki yake bata, dan tasan da matsiyaciyar Baturiyyar nan bata zo gidan su ba da yanzu ita ce matar Yaya Alamin, da yanzu da ita ake wannan soyayyar.

Kitchen Jasmine ta wuce ta cigaba da aikinta duk da kuwa mamakin ganin su Nadia a bangarensu take, Sai dai bata ce masu kala ba gudun kar suyi mata wani cin mutuncin. Sannan taga Alamin bai ce masu komai duk yadda aka yi yasan da zuwansu. Jasmine ta gama saka Pie dinta acikin oven Alamin ya shigo sanye da sababin kaya da alama wanka yayi. Murmushi yayi mata yace "Har kin gama girki?"
Girgiza kai tayi tace "Sauran kaɗan,"

"Alright, muje ke suke jira,"

"Ni kuma?"

"Eh, lets go," Mika hannu Alamin yayi alamar ta taho, hakan yasa Jasmine yin shiru ta tako inda yake sai dai bata saka hannunta acikin nashi ba kamar yadda yaso. Suna fita Jasmine taci birki da taga sun nufi inda su Nadia ke zaune, juyawa Alamin yayi ya kalleta tsoro ya gani a fuskarta ta yadda take kallonsu, ji yayi ransa ya kara baci sosai amma sam bai nuna ba, hannun ta ya kama ya rike. Tana juyo yayi mata murmushi tare da jan hannunata suka cigaba da tafiya har suka isa falon. Suna zama cousins din Nadia suka sauka daga kan kujerun da suke zaune suka koma kasa, Nadia ce kawai ta cigaba da zamanta. Wani mugun kallo Alamin ya jefa mata da sauri itama ta sauka kasa domin ta san halinsa. Batare da Alamin yace masu komai ba suka hade baki a tare suka ce "Baturiyya dan Allah kiyi hakuri, mun tuba bazamu sake..."

Tsawa Alamin ya daka masu fuskarsa a murtike "Matar tawa? Baku san sunanta ba?"

"Kansu a sunkuye suka ce "Yaya Alamin kayi hakuri,"

Tsaki yayi yace "Bani zaku bawa hakuri bah, ita da kuka yiwa rashin kunya zaku bawa hakuri,"

Shiru suka danyi tare da kallon juna kafin suka ce "Anty Jasmine, Allah ya baki hakuri. Mun tuba In'sha Allah baza mu kara ba, dan Allah ki yafe mana,"

Juyawa Jasmine tayi ta kalli Alamin gani tayi gaba ki daya ya chanja daga sweet funny Alamin dinta zuwa Alamin din da ta sani a baya. Rasa me zata cewa su Nadia tayi dan ita bata taba zaton zasu zo su bata hakuri ba, kuma daga dukkan alamu tasan Alamin ne ya sasu.

"Dan Allah ma ku sake, wallahi ko kallon baza wata a cikinku ta kara yi wa matata Uhmm," kwafa yayi sannan ya cigaba da ce "Kun san me zan muku,"

Gyada kai suka dinga yi tamkar wasu kadangaru "In'sha Allahu ma baza mu sake ba,"

Juyawa Alamin yayi ya kalli Jasmine da kanta ke sunkuye "Sweetheart, kin hakura?" Ya tambaye ta tare da sa hannu ya dago da fuskarta.

Murmushi Jasmine tayi masa tace "Eh, na hakura,"

Juyawa Alamin yayi yace masu "Kun ci sa'a, Ku fita ku bani wajen,"

Da sauri suka tashi har yar rige rige suke suka fita daga dakin, Nadia kawai aka bari a zaune. Kallonta Alamin yayi cikin bacin rai yace mata "Ke baki ji me nace bane, ko baki da kunne?"

Bata rai Nadia ta danyi kafin tace "Yaya Alamin, I want to speak with you,"

"Ina jin ki," ya bata amsa a takaice.
Juyawa Nadia tayi ta kalli Jasmine sannan ta kalli Alamin, alamar bata son yin maganar a gaban Jasmine sannan tace "In private please,"

Wani dan karamin murmushi Alamin yayi yace "Komai zaki faɗa ki faɗa a gabanta, dan ko ta tashi sai na sha wahalar faɗa mata. Kinga gwara ki faɗa mana a tare,"

Kallonsa Nadia tayi kawai ta saka kuka har da shesheka, yinkurin mikewa Jasmine tayi Alamin ya rike ta.  "Ke nayi miki kama da shasha ko ni sa'an wasan ki ne," Tsawa ya dakawa Nadia hakan yasa ta tsagaita kukan nata kadan. Cikin sheshekar kuka tace "Haba Yaya Alamin, wallahi ni baka min adalaci, a gaban kowa kake min faɗa kamar ba wacce zaka aura ba."

Dariya Nadia taso ta bawa Alamin amma sam bai nuna hakan ba a fuskarsa da ke a murtuke, ko uffan bai tankawa Nadia ba, haka ta cigaba da cewa "A gaban Kishiyata fa kake mun faɗa, kuma harda sawa na bata hakuri, ni tun kafin na shigo ma ai ta gama raina ni,"

"Ita da kika yi mata rashin kunya a asibiti girmamawa ce? Ko baki san matar Yayanki bace?"

"Amma ai..." Nadia ta fara magana Alamin ya katse ta "Amma me? Gwanda ma ki cire wannan shashancin daga zuriyarki ki yi focusing akan lafiyarki, domin ni bazan taba aurenki. Kanwata ce ke, Jasmine kuma Matatace the sooner you accept this the better."

Ihu Nadia ta saka da jin kalaman Alamin, kuka ta cigaba da yi na gaskiya ba na makirci ba. Mikewa Alamin yayi cikin fushi yace mata "Get out, kafin nayi ball da ke,"

Kokarin tashi Nadia ta fara ta kasa da sauri Jasmine ta mike ya nufi inda take, hannu ta sa dan taimaka mata amma Nadia na mikewa ta hankade Jasmine, Alamin ne yayi saurin rike Jasmine gudun kar ta faɗi, cikin zafin nama ya juya zai bi Nadia, Jasmine tayi saurin rike shi, murya a sanyaye tamkar mai raira waka tace masa "Please M, ka kyaleta bata da lafiya and she's pregnant. Ko ka manta mace ce ita"

Ajiyar zuciya Alamin yayi kawai ya ja Jasmine suka koma kujera suka zauna. Wani kayattacen murmushi Alamin ya saki kamar bashi ya gama faɗa ba yanzu, juyawa yayi yace wa Jasmine "Where were we?"

Wani irin kallo tayi masa cike da mamakin chanjawar yanayinsa "Ban gane ba?" ta faɗa tana kallonsa.

"Ina nufin a Ina muka tsaya dazu," Ya bata amsa tare da saka hannu ya janyota kusa da shi. Murmushi tayi kumatunta suka fara yin ja'a.
Sa hannu Alamin yayi ya taba kumatunta da sukayi ja cikin tsokana yace mata "Are you blushing?"

Ture hannunsa tayi daga kan fuskarta tace "I'm not,"

Murmushi yayi yace "Okay, then look at me,"

Kokarin tashi Jasmine tayi ya jayo ta ya dawo da ita, hanneyenta biyu ya kama ya rike. A hankali tace masa "Alamin, let go of me,"

"Never," Alamin ya faɗa a hanzarce yana kallon fuskarta.

Ba tare da ta kalleshi ba tace "Girki na zai kone fa,"

"Babu komai, sai nayi mana order wani," Ya bata amsa.

Dago da kwayar idanunta tayi ta kalli shi tace "Seriously M,"

Murmushi Alamin yayi ganin Jasmine tasa idanunta a cikin nasa yace "Ko ke fa, nafi son ki rika kallona,"

Juyawa kwayar idanunta tayi tace "I'm talking about girki na, ka sake min hannu inje In duba,"

"Fine, tunda kin damu da girkin nan naki, bribe me sai na cika ki,"

"What?" Daga gira daya tayi.

A takaice Alamin yace mata "Kiss me,"
Zaro idanu Jasmine tayi da karfi tace "WHAT!" ji tayi kamar an tsotse mata ruwan jikinta.

"Eh, kinji me nace,"  Ya bata amsa babu ko alamar damuwa ko wasa a fuskarsa.

Bude baki Jasmine tayi ta kasa magana, a hankali ta rufe bakinta tana cizar lebe ta kasa cewa komai. Lebenta ya kalla sannan ya kalli idannunta yace "Should I?"

Girgiza kai Jasmine tayi, tayi baya da fuskarta muryar ta a kasa sosai tamkar me rada tace "No, I will,"

Murmushi yayi mata har sai dimples dinsa ya lotsa shima cikin sanyi murya yace "Okay,"

"But ka cika min hannu," A hankali Alamin ya sakar mata hannu ya  maida hannayensa gefen cikinta ya rike ta. Turo baki Jasmine tayi tace "Ina nufin ka cikani gaba daya fa,"

Dariya Alamin yayi yace "Come on Love, kema kinsan bazaki iya yi min wayo ba. Ina cika ki zaki gudu,"

Murguda baki ta danyi tace "But this is not fair,"

Dariya tabawa shi sosai ganin yadda tayi da fuskarta, cikin dariyar yace "All is fair in Love and War,"

Kauda kanta Jasmine tayi tace "But we are not lovers,"

Hannu daya Alamin yasa ya gyra mata gashinta da yake rufe mata fuska, barin hannunsa yayi akan gefen fuskarta, idannun ya zuba mata yana kallon fuskarta yace "Inji wa?"

Shiru tayi bata ce masa komai ba hakan yasa ya kara cewa "Tunda baza ki iya ba let me help you out,"

Yar karamar dariya Jasmine tayi tace "Wai dan Allah da gaske kake?"

Janyota yayi ta matso dab dashi kafafusu na gogar juna, "Da kin dauka da wasa nake, Love we can spend the whole day anan ni ba zan gaji ba as long as you didn't do the needful,"

Ajiyar zuciya tayi tace "Fine, close your eyes,"

Jim Alamin ya danyi kafin ya rufe idanunsa bai ce komai ba. A hankali Jasmine ta shafo sajen fuskarsa tare da matsowa kusa dashi, ji tayi rikon da yayi mata ya sassauta hakan ya bata daman mikewa cikin sauri ta ruga da gudu. Bude idanunsa Alamin yayi yana dariya yace "You tricked me, this is cheating,"

Yar siriyar dariya Jasmine tayi tace "Kai fa kace all is Fair in love and war,"

Alamin na mikewa Jasmine ta yi Kitchen da gudu, har ya biyota Kitchen din yaji ana kiran sallar Isha'i, juyawa yayi tafi yin Alwala domin tafiya masallaci. Jasmine na sauke girkinta ta juye acikin warmers taje ta jera akan dinning, nata ta deba ta tafi sama dakinta da shi dan anan za taci saboda gudun sake haduwa da Alamin da take. Alwala Jasmine tayo tayi sallah sannan ta zauna ta ci abincin, tana gamawa ta kwashe kwanikan tana sanɗa ta sauka kasa ta mayar Kitchen sannan ta koma dakinta ta rufe.

Wanka tayi ta dauko pajamas dinta ta saka, ta zauna a bakin madubi ta taje gashinta, sannan ta dauko MacBook dinta ta hau kan gadonta ta zauna tana dane dane. Jamal Yayanta ya kira ta vídeo call, tana amsawa taga bashi kaɗai bane wani kayatacen murmushi Jasmine tayi ganin mahaifin Alamin tace "Tío Yunus!"

Murmushin Datijjo yayi cikin harshen español yace "Te has olvidado de este viejo," (Kin manta da wannan tsohon koh)

A shagwabe tace "Vamos tio, ¿Cómo puedo olvidar a mi tío favorito" (Haba Tío, taya zan manta da Kawu na da nafi so)

"Pero te negaste a visitarme, desde que vine a alemania, Ni siquiera una llamada telefónica," (Amma ai baki zo kin duba ni bah, tunda nazo Germany koh a waya ba kya nema na)

Shiru Jasmine ta danyi kafin ta kama kunneta biyu tace "Nayi laifi I am so so Sorry Tío, bazan sake ba,"

Murmusawa Alhaji Yunus yayi yace "Bethlehem, yaushe hausarki tayi karfi haka?"

Turo baki Jasmine tayi tace "Tío sunan nan kuma,"

Dariya Alh Yunus yayi yace "Har yanzu baki chanja ba Jasmine, Ina sirikin nawa?"

Zaro idanu Jasmine tayi ta juya ta kalli Jamal tace "Jamal, What did you tell him?"

Daga hanayensa biyu Jamal yayi har ya bude baki zai yi magana Alh Yunus ya riga shi "Ina Muhammad din yake?"

Shiru Jasmine ta danyi kafin tace "Yana falo, should I call him,"

Jamal ne ya bata amsa "Hurry up, Ki kira shi,"

Ajiye system din tayi ta tashi ta fita daga dakin. Dakin Alamin ta kwankwasa ta ji anyi shiru, a hankali ta bude kofar ta shiga, duba dakin tayi taga babu kowa acikin, har ta  juya zata fita taga Alamin a jingine a bakin kofa, daga mata gira daya yayi yana kallonta yace "Miss me already?"

Tabe baki tayi tace "You wish, aikoni aka yi,"

Dariya Alamin yayi yace "Come on Love, admit it kawai kewata kike,"

Yar karamar dariya Jasmine tayi tare da nade hannayen ta akan kirjinta tace "Jamal ne ya kira tare da Uncle,"

Barin jikin kofar Alamin yayi ya shigo cikin dakin sannan yace "When?"

"Yanzu, system din tana daki na,"

Fitowa sukayi tare suka shiga dakin Jasmine, "Barka da Yamma Abba," Alamin kansa a sunkuye ya gaishe da mahaifinsa cike da girmama.

"Muhammad ya wajen aikin? Komai dai lafiya?" Alh Yunus ya tambaye shi.


"Lafiya Kalau Abba, ya jikin?"

"Jiki gashi nan ka ki kawota ta duba ni ko sai na mutu sannan zaku zo?"

"Aa Abba, In'sha Allah kwanan zamu zo,"

Murmushi Jasmine tayi masa tace "In'sha Allah zamu zo Tío, kwanan nan,"

"Allah ya sa, Allah yayi maku Albarka ya kare ku daga dukkanin shari na Mutum da Aljan. Allah ya baku zaman lafiya ya haɗa min kanku."

"Ameen Abba, Mun gode," Sallama sukayi yi da Alh Yunus bayan su sha hira sosai dan sunfi hour daya da rabi suna waya.

"You seem very close to my Dad," Ya tambaye bayan sun kashe system din.
Murmushi Jasmine tayi tace "He's like a father to me, duk lokacin da yazo England a gidanmu yake sauka, gatan da Tío yake min tamkar shiya mahaifeni, bare da Papi ya rasu shi ya maye min gurbinsa."

"Allah ya jikansa ya jaddada rahama garesa,"

Murmushi Jasmine tayi tace "Ameen, Thank you."

Juyawa Jasmine tayi ta kalli Alamin da ke zaune a  kusa da ita tace "Baka faɗa masa ba?"

"Me zan ce masa Jasmine, tayaya zan fara fada masa. Matarsa ta fiye da shekara goma sha takwas ta ci amanarsa ko tana son ta kashe shi. Ban san me zan faɗa masa ba," Shiru ya ɗan yi sannan ya cigaba da cewa "Gashi ya fara samun sauki nasan dole na fada masa amma ta Ina zan fara?"

Shiru Jasmine ta danyi kafin tace "Bana tunanin kashe shi tayi niyar yi, kawai dai ta so ta nakasta shi ne yadda zata cigaba da zama in control a gida nan. Bata da wata riba idan ya mutu." Gyara gashinta Jasmine tayi sannan ta cigaba da cewa "You don't have to tell him anything M, ita da kanta zata yi confessing, nan da two weeks jikinta yayi kwari sai mu tafi da ita Germany din."

"Do you think he can handle it?"

"I don't know." ajiyar zuciya Jasmine ta danyi kafin ta cigaba da cewa "Sai dai kawai mu taya shi da addua Allah ya sanyaya masa zuciyarsa,"

"Ameen," Shiru suka yi sun fi minti 10 babu wanda ya kara cewa komai acikin su, kowa nasa tunanin yake. rufe MacBook dinta Jasmine tayi ta ajiye a kusa da lamp din da ke gefen gadon. "Alamin," a hankali ta kira sunansa. Jin bai amsa mata ba yasa ta juyo inda yake, yar karamar dariya ta saki ganin yayi bacci "Alamin, ka tashi ka koma dakin ka." Ta faɗa da dan karfi tana kokarin tashinsa. Ganin yaki ko motsawa yasa ta hakura dan tasan baccin nasa yayi nisa. Wayarta ta dauka ta bude ta messages da yawa, kishingida ta fara replying messages din..........



Assalam alaikum
Ban taba rubuta shafi mai tsayin wannan bah 5308 words da yawa 🤯🤯, Da fatan dai duk kun ji dadin wannan Shafi mai tsayi
Ya Azumi?
Allah ya karbi Ibadun mu
Ameen

Ya kuka ga marin da Jasmine tayiwa Nadia?

Shin anwa Nadia adalci da Alamin ya sake marinta?

Ya kuke ganin soyayyar nan tasu an samu cigaba koh ya?

Shi kuna gani akwai wani abu da zai iya raba Alamin da Jasmine?

Kar ku manta ku fado min ra'ayoyinku game da wannan shafi.

Don't forget to Vote ⭐️⭐️ and Comment

❤️❤️❤️

Continue Reading

You'll Also Like

353K 27.7K 29
Mini Story Uni Life Style Sweet Romance
91.5K 12.1K 55
Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta ha...
219K 13.6K 44
Yanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resem...
37K 1.3K 32
Karki kashe! Tsura ma screen din wayar tayi tana kallo, ta rasa me Rayhan yake nufi da ita sam a rayuwarta. Send me you pic I wanna see that beautifu...