Jasmine Baturiyya ce

By Amiratuoo

117K 8.8K 1.4K

Completed (Currently Editing and Re-uploading) JASMINE haifafiyar kasar ingila (England) ce. Ya'a ga hamshaki... More

🌷JASMINE🌷
🌷Shafi na 1🌷
🌷Shafi na 2🌷
🌷Shafi na 3🌷
🌷Shafi na 4🌷
🌷Shafi na 5🌷
🌷Shafi na 6🌷
🌷Shafi na 7🌷
🌷Shafi na 8🌷
🌷Shafi na 9🌷
🌷Shafi na 10🌷
🌷Shafi na 11🌷
🌷Shafi na 12🌷
🌷Shafi na 13🌷
🌷Shafi na 14🌷
🌷Shafi na 15🌷
🌷Shafi na 16🌷
🌷Shafi na 17🌷
🌷Shafi na 18🌷
🌷Shafi na 19🌷
🌷Shafi na 21🌷
🌷Shafi na 22🌷
🌷Shafi na 23🌷
🌷Shafi na 24🌷
🌷Shafi na 25🌷
🌷Shafi na 26🌷
🌷Shafi na 27🌷
🌷Shafi na 28🌷
🌷Shafi na 29🌷
🌷Shafi na 30🌷
🌷Shafi na 31 🌷
🌷Shafi na 32 🌷
🌷Shafi na 33🌷
🌷Shafi na 34 🌷
🌷Shafi na 35🌷
🌷Shafi na 36🌷
🌷Shafi na 37🌷
🌷Shafi na 38🌷
🌷Shafi na 39🌷
🌷Shafi na 40🌷
🌷Shafi na 41🌷
🌷Shafi na 42🌷
🌷Shafi na 43🌷
🌷Shafi na 44🌷
🌷Shafi na 45🌷
🌷Shafi na 46🌷
🌷Shafi na 47🌷
🌷Shafi na 48🌷
🌷Shafi na 49🌷
🌷Shafi na 50🌷
🌷Shafi na 51🌷
🌷Shafi na 52🌷
🌷Shafi na 53 🌷

🌷Shafi na 20🌷

3.6K 199 21
By Amiratuoo


Wata daya kenan da tafiyar Alamin kasar Germany tare da Mahaifinsa domin nema masa lafiya, sau uku kadai suka yi waya da Jasmine, wayar da bata fin ta minti uku ba, dan ko lafiyar Alh Yunus zata tambaya sai dai ta kira Dr Stephen. Kamar yadda Dr Stephen ya faɗa mata  jikin Alh Yunus yayi sauki sosai domin kuwa har ya fara magana da zama da kansa, tashi da tafiya ne dai sai an rike shi.

Jasmine tana ta kokarin neman mahaifiyarta sai dai har yanzu bata gano wani abu ba hatta mutum da ta dauka aikin binciken babu abunda ya gano face wacce take tunanin ita ce mahaifiyarta ta Dr Halima matar tsohon gwamnan Kano, ba ita bace ba dan har gidanta taje. Duk da kuwa  tsohuwar first lady na matukar kama da mahaifiyarta sai dai Jasmine na zargin  ko dai Dr Haliman na da alaka da mahaifiyarta saboda kamanin sun ɓaci. 

Duk da Jasmine bata tare da Matthews tafiyar Alamin ta kara jawo su kusa domin kuwa kullum sai sunyi waya babu abinda Matthews bai sani ba game da zamanta a Nigeria. Abu daya ne har yanzu ta kasa sanar da shi shine aurenta da Alamin. Duk da tasan auren ba na gaske bane amma gani take kamar cin amanar Alamin take idan suna waya da Matthews sam bata iya sakewa kamar da shi kamar da.

Hajiya Saudat kuwa gabaki daya  daina fitowa daga bangarenta gabaki daya duniyar tayi mata zafi, kullum cikin fargabar bayyanar abunda ta aikata take, duk da tasan babu wanda yasa abunda ta aikata daga Jasmine sai Alamin.

Jasmine na zaune a babban falon gidan tare da su Hajiya Kaka suna hira. Sai dariya suke suna fara'a, suna ta tsokanar Hajiya Kaka. Sallamar da suka ji ce ta katse masu hira. Suna amsawa Muktar daya daga cikin ma'aikatan gidan ya shigo da akwatin guda biyu a hannunsa. Khadija ce ta yin saurin tambayar ma'aikacin "Akwatunan waye wannan?"

Amma kafin ya bata amsa Nadia ta shigo da tana tafiya da kyar cikinta ya tasa sosai. Steps din shigowa falon ta fara takawa zata shigo sai ta zame zata fadi, cikin sauri Alamin da ke biye da ita ya rikota kafin ta faɗi. Baya Nadia tayi ta fada jikinsa sannan ta ski wani makirin ihu ta makalkale Alamin kamar wacce taga wani abun tsoron.

Rike Alamin yayi ya dan matsar da ita daga jikinsa yace mata "Are you Okay?"  Shiru Nadia tayi bata bashi amsa ba sannan bata cika shi ba. Juyar kanta tayi suka hada ido da Jasmine ta sakar mata wani makirin murmushi.

Murmushin itama Jasmine ta mayar mata sannan ta kashe mata ido daya, duk da kishin da taji ya kamata. Daga mata  ɗan yatsanta na tsakiya tayi sannan ta dauke kanta. Dan ta gane zamewar karya tayi saboda tasan Alamin zai rikota zai bari ta faɗi ba, duk dan ta bata mata rai.

A hankali Alamin ya zame jikinsa daga rikon da Nadia tayi masa sannan yace mata "Muje, amma ki kula da steps dinnan kar ki kara zamewa."

Murmushi Nadia tayi masa  ta rike hannusa gagam kamar me tsoron wani abu, a hankali suka sauka daga matattakalar suka shigo cikin falon. Hajiya Kaka ce kawai tayi masu sannu da zuwa, dan Khadija da Basma kallo kawai suke binsu da shi ganin yadda Nadia ta rike hannu Alamin kamar idan ta cikashi zai bacce, kuma bai hanata ba sannan bai ce mata komai ba. A hankali suke tafiya har ya sama mata waje a falon ta zauna sannan shima ya samu waje ya zauna. Jasmine yi tayi kamar bata gansu ba duk da irin kallon da Alamin yake mata yana jira tayi masa magana.

Hajiya Kaka ce ta fara magana "Mai gidana ya naga ka dawo da ita a haka? me yasa baka fada mana zaku dawo ba, gashi ko girki ba'a yi maka ba." ta karashe maganarta tana kallon Jasmine, tana tunanin ko tasan da dawowarsa amma bata sanar da su ba.

Murmushi Alamin yayiwa Kakarsa, sannan ya juya ya kalli Jasmine yace "Ai ko kamar kin san yunwa nake ji," nufasawa yayi ganin Jasmine taki kallonsa ya cigaba da cewa "Nadia taki zama a asibitin, tunda taji zan dawo ta daga hankalinta sai ta dawo gashi har BP ta ya hau, shiyasa likitanta ya ce na taho da ita kawai, tunda kinga jikin nata yayi sauki, zai duga kira kawai idan an samu wani complications kuma a maida ita chan."

"Toh ai shikenan, Ke Khadijah tashi ki kawowa Yayanku wani abun yasha kafin mu ci abincin?"

"Wasa fa nake miki Kakale bana jin yunwa, hutawa kawai zanyi."

Dariya Hajiya Kaka tayi tace "Allah ya shirya min kai. Ina mahaifin naka, ya jikin nasa?"

Cikin zolaya Alamin yace "Kaji masu ɗa, Jiya fa kuka yi video Call Kaka,"
Hannu ta daga tace masa "Ungu wannan mai garinku."

Dariya Alamin yayi yace "Abba ya samu sauki sosai Hajiya Kaka. Nima wani aiki ne ya dawo da ni, amma da na gama zan Uk." Alamin ya bata amsa.

Wani kyakyawan saurayi ne ya shigo falon da sallama. duk suka juya suna kallonsa, baƙi neh shi amma ba sosai ba, ga shi dogo mai dogon hanci da manyan idanu farare. Sanye yake da kananan kaya wayanda suka matukar karbar shi.

Basma na kallonsa ta juyo da sauri suka hada ido da Jasmine, wani dan murmushi suka sakarwa juna wanda su kadai suka san ma'anarsa, Jasmine tace "Handsome." A hankali yadda iya Basma ce da ke kusa da ita taji.

Murmushi mai sauti Basma tayi ita tace "I know I know, but he's mine." a hankali tana kallon Jasmine. Tuntsurewa da dariya Jasmine tace "Come on, I'm just admiring a fellow handsome human, beside I'm already tied," kashe mata ido daya sannan ta juya ta kalli Alamin taga shima kallonta yake. 

Duk abunda Jasmine da Basma suka yi kuwa akan idon Alamin ya faru, dan tuni ya hade rai kamar ba shi ya gama dariya ba yanzu, a hankali ya juya ya kalli abokinsa da ya shigo. "What are you doing here." Alamin ya tambayi shi.

Murmushi abokin nasa yayi sannan yace "Zuwa nayi na gashe da Hajiya Kaka, mun dade bamu gaisa bah."

Dariya Hajiya Kaka tayi sannan tace "Najibullahi, ai na dauka ka daina zuwa gaishe ni."

Sosa kai Najib ya fara yi amma kafin yace wani abu Alamin yayi saurin cewa "Yanzu ma ba danke yazo ba Hajiya, tafiya ce ta hada mu da shi, tare muka taho daga Germany kuma gobe zai wuce Abuja."

Girgiza kai Hajiya Kaka ta farayi tana kallon Najib tace "Na rasa me yasa yaran yanzu ba kwa son zumunci, ya chan wanjen Kakar taka."

"Kaka tana nan lafiya, tace a gaishe ki."Najib ya bata amsa.

Tashi Alamin yayi da yaga Najib din bashi da alamar tafiya ya samu waje ma ya zauna, har yana kokarin fara hira da Kaka. "Kasan muna da aiki sosai gobe, muje ka ga takardun." Alamin ya faɗa a tsaye yana kallon Najib, Dan babu wasu takardu kawai so yake Najib ya fita saboda irin kallon da yaga kannesa suna wa Najib din.

Murmushi Najib yayi yace "Hakane fa, muje." Ya mike, ɗan ya gane me Alamin din yake nufi.

Amma kafin su fita Hajiya Kaka tayi saurin dakatar da su "Ina zakuje, yanzu zamu ci abincin fa."
"Hajiya akwai wani aiki mai mahimmanci da zamu yi idan muka dawo ma ci." Alamin ya bata amsa.

"Haba cin abincin minti nawa ne, balle ma matar ka ce yau tayi girkin da kanta. Kamar tasan zaka dawo yau. Maza muje," Hajiya Kaka ta mike da kyar domin tafiya dining room.

Fasa fita yayi saboda jin Jasmine ce tayi girki duk da dazu da yace yana jin yunwa basu gaya masa tayi ba"Shi kenan." kawai Alamin ya ce suka yi hanyar dining room din tare da Najib. Ba'a san ransa ba dan kuwa sontake Najib ya tafi gashi yasan idan ya koreshi Hajiya Kaka ta rika mita kenan.

Suna isa Dining room din kowa ya samu waje ya zauna, Jasmine ce kawai a tsaye ta sallami Ma'aikatan da suka gama jera abincin akan dining table din. Warmers din abincin ta bude ta fara zuba ma su, bayan ta gama zubawa kowa, itama ta samu waje ta zauna.

Hajiya Kaka da Khadija nata kallon abincin gabansu suka tsaya yi sun kasa ci dan basu taba cin irin girki ba, Nadia ko yatsina fuskar take tayi tamkar taga wani abun kyamar.

Dariya su so su bawa Jasmine, mikewa tayi a hankali tace "Wannan girkin, abincin kasar Spain, wannan sunansa Pisto Manchego, haka ake shan ta kamar soup." Ta nuna soup din da ta zubawa kowa a wani karamin kwano. Sannan cigaba da nuna abincin da ke cikin plates tana bayani akansu "Wannan kuma sunansa Paella da shinkafa na yi shi as you can see."

Lemon da ta hada Jasmine ta dauko ta zubawa kowa a kofinan tangaran guda biyu ta ajiye gabansa sannan tace "Wannan lemunan guda biyu kuma akwai Sangría Red color dinnan kenan sai Rebujito shi kuma cocktail neh."

Da sauri Najib ya ajiye kofin lemon sa da ya fara sha yana ji ta faɗi sunan lemin, Alamin ma saurin dagowa yayi yana kallonta. Yadda fuskokinsu yayi ba karamar dariya abun ya bata ba. "Karku damu bansa red wine aciki ba grape juice ne maimakon red wine." Ta faɗa tana dariya.

Ajiyar zuciya Najib yayi sannan ya cigaba da shan lemon nasa wato Sangría, shiko Alamin Rebujito ya dauka ya fara sha.

Wani dogon tray da ke tsakiyar dining table din Jasmine ta nuna tace "And finally wannan sune deserts din mu, leche frita da Teramisu, a ci lafiya." Ta na gama fada ta zauna itama kowa ya fara cin abincin.

Dandawa Hajiya Kaka ta fara yi sai kuma ta zage tana ci, tsoho da kwadayi kafin kace me ta fara yabawa da girkin Jasmine dan yayi mata dadi sosai duk da batai tsamanin zai yi dadi ba. Iya yawon kasashen da tayi, abincin turawan da ci ba su yi ma ta dadi ba shi yasa duk inda taje bata cin abincin kasar ta fi son abincin Afrika ko na kasashen larabawa. A tunaninta abincin turawa jagwalgwalo musamman da taga suna zuba madara a cikin pasta.

Santi kowa ya ringa yi yana yabawa Jasmine girkinta, Alamin ma ya yabi girkin nata sosai dik da Jasmine din bata tanka masa ba murmushi kawai tayi. Nadia ce kaɗai bata ce komai ba sai bata rai da ta ke dan bata so girkin yayi dadi ba.

Khadija ce ta fara daukan daya daga cikin deserts din da ke kan tray ta fara ci, juyowa tayi ta kalli Jasmine tace "Wannan kamar cake amma meyasa kuke kiransa Teramisu."

Kafin Jasmine ta bata amsa Najib yace "Teramisu ai ba Spanish desert bane abincin yan Italy ne right." ya juya yana kallon Jasmine.

Murmushi Jasmine tayi tace masa "Hakane," Jasmine ta ɗan yi murmushi "Amma ya akayi ka sani? Alot of people don't know that,"

Murmushi Najib ya sake yace mata "Una volta vivevamo in italia, e tu?" (Mun taba zama a kasar Italy, kefa )

"You speak Italian, Sono stato anche in Italia per tre volte (Ni Sau uku kawai na taba zuwa Italy)." Jasmine ta bawa Najib amsa itama cikin harshen Italy.

"Impressive," kallonta Najib yayi cike da mamaki yace "Ci sei stato solo per tre volte, come hai imparato la lingua così fluentemente? " (Sau uku kika taba zuwa, amma ya akayi kika iya yaren sosai haka)

"Ho alcuni amici in Italia, ecco perché "(Ina da kawayen yan kasar Italy da yawa shi yasa)."

"You're Multilingual? How many languages do you speak?" Najib ya tabayeta.

Kafin ta bashi amsa Alamin yace masa ya masa "Tashi mu tafi," Zuciyarsa sai tafasa take saboda kishi. Hirar tasu ta yi yawa ɗan yana jin duk abunda suke faɗa da yaren. Ji yayi yake kamar ya shako abokin nasa ya fitar da shi waje dan tun sanda Jasmine tace handsom, gabaki daya yanayinsa ya chanja. Hakan ya tashi Najib suka fita ba tare da sun karasa cin abincin su ba.

Suna fita Hajiya Kaka ta tashi, ta gama cin nata amma kafin ta tafi sai da tasaka a jiye mata ragowar abincin flasks din dan anjima zata sake ci, mussamman ma Pisto Manchego saboda shi ruwa ruwa ne. Shiko lemon Sangría gabaki ma dayanshi Hajiya Kaka ta dauka ta tafi da shi Bangarenta.

Khadija da Basma kuwa fada suka fara yi akan dayan lemon Rebujito, sai da Jasmine tace gobe zata sake yi musu wani Khadija ta hakura su ka raba da Basma.

Wata muguwar harara Nadia ta gallawa Jasmine tace "Wai ke a tunaninki tunda an daura maku aure shi kenan kin mallake shi, to bari na faɗa miki wallahi baki isa ba, dan kuwa da zarar na haihu zai kora ki. Daman chan ke substitute ce ke, a rashi na ne aka karo ki kuma yanzu mai waje yazo dole mai tabarma ya nade."

Har Jasmine ta bude bakinta zata mayar mata da wata maganar mai daci kawai sai ta fasa, murmushi kawai tayi tace "Ayi dai mu gani." Sannan ta tashi tayi tafiyarta ta bar Nadia a zaune tana jin kumbura.

*****
Washe gari

A kofar dakin Jasmine Alamin ya tsaya yana bugawa, ganin ba'a amsa ba ya bude dakin yaga bata ciki. Nemanta ya fara yi dan jiya bai dawo da wuri ba bayan fitarsa bai samu ganinta ba da ya dawo. Bayan ya raka Najib bangaren baki,  sannan ya hana shi shigowa cikin gida har ya tafi.
Gym dinsa Alamin ya nufa bayan ya duba kaf part dinsa bai ganta ba. Yana shiga ya hango ta akan yoga mat, sanye da kayan motsa jiki a jikinta. Bakar half vest da bakin leggings ne a jikinta ta tufke gashin kanta. Tana ta wani irin lan kwashe lankwashe, tsayawa kawai yayi yana kallonta, yadda take iya lankwasa jikinta ne ya matukar burgeshi, karasawa kusa da ita yayi ya taba kafadarta sannan ta bude idonta, ta cire earpods din da ke kunneta.

Murmushi tayi masa ta mike tsaye "Good morning." Ta faɗa a hankali, sannan ta dauki karamin towel tana goge gumin da ke fuskarta da jikinta, cire robar da ke rike da  gashin kanta tayi ta sake shi ya zubo har kugunta.  Tsayawa Alamin yayi yana kallonta ya kasa dauke idanunsa daga kanta ba karamin kyau ta kara ba da ta saki gashin nata, sai kace wacce ta fito daga cikin zaneh, dan ko kaɗan bata da makusa a wajensa.

"Hey!" Jasmine ta sake faɗa hade da tafa hannunta a fuskarsa ganin yayi shiru bai ce mata komai ba sai kallonta da yake. "Penny for your thoughts."  ta tambaye shi tana murmushi.

Murmushi yayi yace "No, sai dai diamonds, let's go. Akwai abunda nake son na nuna mike."

Binshi Jasmine tayi a baya har suka isa falonsa, suna zuwa kuwa ya kaita daidai center table din falon, a hankali ya daga wani kyale da ya rufe abunda da ya ke son nuna mata, yana budewa sai ga tsunsaye Aku guda biyu acikin keji. Wani irin murmushi mai hade da dariya Jasmine ta saki tsabar farin ciki da sauri tayi wajen suntsayen tana dariya ta tsunguna ta na kallonsu.

"Ya sunansu?" Ta juyo ta tambayi Alamin.

Shiru Alamin ya dan yi sannan yace, "Basu da suna, ki saka musu ke na siyowa, they're yours."

Tsalle ta Jasmine tayi cike da farin ciki ta rungume Alamin, tana cewa "Gracias."

Zaro idanu Alamin yayi saboda shamatarsa da tayi, ji yayi gabaki daya numfashinsa ya tsaya. Ya kasa cewa ko uffan.

Da sauri Jasmine ta cika Alamin ta dan ja da baya da ta fuskanci abunda ta aikata, maida gashinta da ya zubo gaba baya ta ta sunkuyar da kanta a kasa tace "Uhmm, sorry that wasn't very dignified, I got carried away."

Murmushi yan dan yi bayan ya dawo hayacinsa yasa hannunsa ya dago fuskarta yace "You don't have to apologize, wannan ai ba wani abu bane after all you're my wife."

Shiru ta danyi kafin tace "Na gode sosai, amma ya akayi kasan inason Parrots?" Amma kafin Alamin ya bata amsa tayi saurin katse shi "You don't have to answer that nasan Jamal ne ya faɗa maka."

Murmushi Alamin yayi yace "Right, shi ya faɗa min, bayan Stacy ta mutu baki sake yi wani pet din ba."

Juyawa Jasmine tayi tana kallon tsuntsayen tace "I loved Stacy so much da ta mutu ji nayi kamar kanwata ce ta mutu, shiyasa naki siyo wata saboda bana son sabawa da abunda wataran zan rabu da shi ba."

Dan murmushi gefen bakin Alamin yayi wanda yakara fito masa da kyansa sannan yace "Yasmine kenan, there's nothing like forever a duniyar, everything die at a point, that's the cycle of life. Wani yazo wani ya tafiya."

Daukar kejin tsuntsaye tayi tana murmushi tace "Right, bari naje na zaba masu suna, Thank you once again." Wucewa tayi ta fi sama da su.

****

Jasmine na saukowa kasa zata fita ta hadu Alamin a falo shima zai fita, juyowa Alamin yayi yana kallonta yace "You look lovely.....uhm...the dress looks good on you."

Dariya Jasmine tayi tace "You look dashing yourself, office zaka?"

Gyda mata kai yayi yace "Eh, kefa?"

"Zamuje shopping da Basma, I need to grab a few things." Ta bashi amsa.

"Okay." Kawai Alamin yace.

Hango Nadia tayi tana laɓe tana jin abunda suke, bata san Jasmine ta ganta ba ko motsawa batayi saboda munafurci. Kalaman Nadia na jiya ne suka fado Jasmine rai, murmushin mugunta tayi, a ranta tace nima yanzu zan fara nawa wasan.

Karfin hali tayi ta taka a hankali cikin yanga da rangwada matso inda Alamin yake tsaye, hannunta ta dora kirjinshi ta dan tura shi baya, ya jingina a jikin bango. Dagowa Alamin yayi da sauri yana kallonta mamaki fal idanunsa amma kafin yace wani abu  tasa yatsanta akan bakinshi tana murmushi tace "Shhh." A hankali ta matsar da fuskarta kusa da tashi, duk da akwai heels a kafarta sai da ta danyi dage sannan ta kai daidai kunnensa. A nutse cikin siririyar muryarta tamkar mai raira waka tace masa "Il tuo fidanzato ci sta perseguitando, so I thought why don't we give her a show," (Fiancée dinka na mana labe, so I thought why don't we give her a show) Ta karashe maganarta da yar karamar dariya.

Murmushi yayi sannan ya dora hannunsa a kan kugun Jasmine, a hankali ya kara janyota jikinsa. Gefen fuskarsa Jasmine ta shafa a kasale sannan ta kai bakinta daidai nasa sai ta dan matsar da shi ta yi masa karamin kiss a gefen bakinsa, idanunta ta dago tasa a cikin nasa tace "Sai ka dawo."

Cika shi tayi za bar wajen Alamin ya riko ta ya dawo da ita jikinsa "You have no idea how control you have iver me Yasmine! Ko dai bakya son na fita ne?" Ya tambayeta yana lumshe ido.

Murmushi Jasmine tayi ta kai bakinta daidai kunnensa tace "Nice acting, you deserve an Oscar,"

Kwalla ce ta ciciko sosai a danun Nadia tamkar tayi kuka. Tabbas tasan ita ta jawa kanta domin da ta ruke mutuncinta da yanzu ita ce a amatsayin Jasmine. Wasu zaffafan hawayen fushi da kishi ne suka zubo mata, Idanunta a rufe ta juya da gudu ta tafi tana kuka har ta buga kofar da ta buya a bayanta bata sani ba, tana kuka ta koma bagarensu, zuciyarta fal cike da dana sani.

Jasmine na ganin ta tafi tayi saurin ta ja da baya daga jikin Alamin tana dariya, shi kuwa Alamin murmushi kawai ya dan yi jikinsa duk a sanyaye.

Cikin dariya Jasmine tace "Yau Allah neh kadai zai kwace ni idan na hadu da Nadia, Allah neh kadai yasan abunda zata yi min."

"Babu abunda ta isa tayi miki," Alamin ya faɗa yana kallonta "But, please let's not play this dangerous game again I am not sure I have this much control next time."

Tsagaitawa da dariyar tayi tace "Why? We were just acting?"

Wani irin kallo yayi mata yace "You were but I wasn't, every word I meant it."

Juyawa yayi ya fita ya bar a tsaye da baki a bude tana bisa da kallo.



Assalam Alaikum

Happy New Month Guys

Dafatan kunji dadin wannan shafin ku fada min ra'ayoyinku
Alamin zai tafi Germany, gashi Nadia mah tana chan kuma gari daya asibiti daya to ya kenan??
Jasmine kuma zata cigaba da neman mahaifiyarta.

Continue Reading

You'll Also Like

123K 12K 31
Tana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu...
355K 27.7K 56
Kaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar...
125K 17.4K 30
ရိုးရိုးအချစ်ဇာတ်လမ်းလေးတစ်ပုဒ်ပါပဲ
393K 24.5K 73
Labarin Zaid da Zahrah...."Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mai zaka amfana dashi acikin rayuwarka ? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci ? Na...