GAMON JINI

Galing kay Oum_Tasneeem

7.6K 421 23

Labarine da ya qunshi soyayya cikin xumunci,sadaukarwar soyayyah,da kuma qarfin zumunci. Higit pa

GAMON JINI 1
GAMIN JINI 2
GAMON JINI 3
GAMON JINI 4&5
GAMON JINI 5 to 10
GAMON JINI 10 to 15
GAMON JINI 15 to 20
GAMON JINI 25 to 30
GAMON JINI 30 to 35
GAMON JINI 35 to 40
GAMON JINI 40 to 45
GAMON JINI 45 to 50
50 to 55
GAMON JINI 55 to 60
GAMON JINI 60 to 65
GAMON JINI 65 to 70
GAMON JINI 70 to 75
GAMON JINI 75 to 80
GAMON JINI 80 to 85
GAMON JINI 85 to 90
GAMON JINI 90 to 95
GAMON JINI 96
GAMON JINI 97
GAMON JINI 98
GAMON JINI 99
GAMON JINI 100
GAMON JINI 101
GAMON JINI 102
GAMON JINI 103
GAMON JINI 104
GAMON JINI 🔚🔚🔚

GAMON JINI 20 to 25

213 11 1
Galing kay Oum_Tasneeem

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

2⃣0⃣ to 2⃣5⃣

Da uniform dinta ta pito ta gangara qasan layinsu kasancewar basu da nisa da gidan kawun nata,tana isa ta tarar dashi a qopar gida yana jiranta,tsugunnawa tayi

" INA kwana"

"Lapiya,har an shirya tapiya makarantar kenan"

"Uhmm"

"Toh dama abinda yasa na kiraki nasan kin shirya saboda haka daga yau na hana zuwa makarantar nan,don banga ampanin da zatai miki ba,ke da zan miki aure"

Da Sauri ta dago kai ta dubeshi

"Ban isa bane?? Ko kuma kina da magana ne ??
Girgiza kai tayi.  

yace" shikenan,tashi ki tapi" miqewa tayi ta kama hanyar komawa gida.

Tana Shiga gida ta rushe da kuka,umma ta samu a tsakar gidan zaune akan tabarma.

"Lapiya fadee,me ya paru"

Cikin kuka take magana"umma yace wai kar in qara zuwa makaranta,ya hana saboda aure zaimin,umma ya zanyi?? Me yasa basa sona??
rarrashinta ta para yi,har tayi shiru sannan tace taje ta cire uniform dinta,daki ta tashi ta shiga ta cire uniform din ta dawo ta kwanta akan tabarmar da ummanta take zaune ta Dora kanta akan qafafunta.

A haka umman tai ta yi mata nasiha har ta warware suka para hira,har wajen 12 sannan fadeelan ta tashi ta Dora musu abincin rana tunda yau bata je mkaranta ba.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Salima CE da khadija a parlon mummy suna hira

"Khadija wannan Wanda na gani da yaya Abdul ranar nan pa?? Naga yana kama daku kuma yapi yaya Abdul fara'a"

"Ohk,yaya mubarakh,qanin dad ne,a gidan nan yake amma baya zama sosai,yapi zaman Libya,ko dai kanshi kika koma kuma??"

"Haba dai ai ina nan akan baka na,don Abdul sai ya soni,kuma sai na aureshi ko ta wane hali"

Tabe baki khadija tayi ta miqe tabar wajen don tasan halin salima da mummy na bin malamai kuma  ita har yanxu bata ga nasarar da mummyn ta samu ba.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Yau da wuri suka dawo daga office,mubarakh ne ya dauko wayar da ya siyo ya sa a chaji,bayan ta cika ya bude ya sa sim da recharge card din daya siyo sannan ya sa number shi a cikin wayar yai saving,shima yai saving din sabuwar number a cikin wayarshi.
Tashi yai yayi wanka ya shirya sannan ya kira abdul a waya yazo yashirya don shi tunda suka shigo gidan ya tapi wajen mommah.

Shima shigowa yayi yai wankan sannan ya shirya,sukai sallar la'asar sannan suka pito don tapiya gidansu fadeelah.

Tapiya sukeyi mubarakh yana bin waqar da suka saka a motar,abdul kam gabanshi ne yake ta faduwa,ya rasa dalili,a haka har suka isa bakin titin gidan gidansu fadeelah suka pito suka shiga.

Fadeelan da tunda ta gama girki ko abincin bata ci ba tai wanka ta shirya cikin wata jar atampa mai ratsin baqi acikinta sannan ta dauko gogaggen hijabin ta baqi ta ajiye domin zuwan mubarakh,ta gama ta koma daki ta zauna tana tunanin rayuwarta tajiyo sallamar yaro.

Fitowa tayi don tasan mubarakh ne ta dauki pray mat guda biyu ta pita.

Sallama tayi acikin soron gidan ta shimfida pray mat din,ganin su biyu ne yasa ta shimpida musu a kusa domin su zauna a tare,ta juya ta koma gida ta dauko wata a gida ta shimpida dan nesa dasu.tunda ta shigo wajen idon mubarakh yake kanta don ba qaramin kyau tayi mishi ba,shiko abdul bai ma san abinda suke ba.

"Bismillah" tace tana nuna musu wajen zama,dai dai lokacin da abdul ya kalleta take yaji bugun zuciyarshi ya qaru,
"ba dai ita ce budurwar mubarak ba" ya fada a zuciyarshi,lallai akwai matsala.

Maganar da mubarakh yake mai ne yasa ya dawo daga tunanin da yake shima ya zauna kusa da mubarakh.

Suna gama gaisawa abdul ya miqe yacewa mubarakh zai jirashi a mota ya gama.

Kasancewar ita fadeelahn bata ganeshi ba ma yasa bata nuna wani abun ba.

Basu dade ba mubarakh yace zai tapi saboda abdul dayake mota yana jiranshi,bayan ya sanar da ita ranar juma'a manyanshi zasuzo maganar aurenta,miqewa yayi suka pito tare ta rakoshi qopar gida,wata takarda ya miqa mata sannan sukai sallama ya tapi.
Komawata soron taga leda a inda ya zauna,da sauri ta dauki ledar ta pito bata ganshi ba ta koma ta shiga gida,
Sai da ta shiga daki ta bude takardar

_Ga waya nan ki kunnata pls,zan kiraki_
  _mubarakh_

Ledar ta bude taga waya ce acikin kwali,wajen ummanta ta tapi

"Umma,kinga yaya mubarakh ya ajiye,kuma ya bani wannan takardar" karbar takardar tayi ta karanta sannan ta ce

"Toh fadeelah,nidai ina tsoron yaran nan  masu kudi,kar ya aureki ya wulaqanta ki fadeelah,ya ganki er talakawa"

"Hakane umma,amma ni wlh kawai ganin girmanshi nake sosai"

"Toh,Allah yasa alkhairi"

"Umma kuma yace ranar juma'a zasuxo a fadawa su kawu"

"Toh nasan kawun naki zaizo ma ai kapin juma'ar"

Bude wayar tayi a kwalin ta kunna ta,duk da bata san kan waya ba amma tunda ta iya turanci bata ji wahalar operating wayar ba.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Abdul tunda ya pito daga gidan tapiya kawai yake har ya qaraso bakin titi ya bude motar ya shiga,kanshi kawai ya kipa,wani irin sarawa kan nashi yake mishi ga tunani da ya mai yawa,saboda yasan ko giyar wake yasha ba zai iya cewa mubarakh itace wacce yakeso ba.

A haka mubarakh ya zo ya sameshi ya bude motar ya zauna.

"Abdul ya dai??"

Dago kanshi yai jin maganar mubarakh,mubarakh da yaga idonshi yayi jaajur ne duk hankalinshi ya tashi.

"Me ya paru??"

"Kaina ne yake ciwo" ya fada da qyar

"Toh,muje asibiti" ya pada tare da kunna motar

"A'ah muje gida kawai,in na dan huta zai tapi"

"A'ah muje dai a karbo mka magani"

"ko dai akan maganar jiya ne??"

"Noo, ba ita bace,muje gida kawai"

Marriam mayshanu👌🏻

Ipagpatuloy ang Pagbabasa

Magugustuhan mo rin

12.7K 852 9
✧𝒁𝒂𝒏𝒊𝒚𝒂𝒉 - Forever, Always ∞ Jeon Jeongukk, The most prestigious and respected Commissioner. For whom every thief and murderers are...
517K 33K 41
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
647K 29.4K 42
Needs editing [ the destiny series #1] 𝑻𝒉𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆 𝒑𝒖𝒔𝒉𝒆𝒅 𝒕𝒉𝒆𝒎 𝒂𝒑𝒂𝒓𝒕 𝒃𝒖𝒕 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒂𝒈𝒂𝒊𝒏 𝒑𝒖𝒍𝒍𝒆𝒅 𝒕𝒉𝒆𝒎 𝒕𝒐𝒈...
1.7M 142K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...