Jasmine Baturiyya ce

By Amiratuoo

117K 8.8K 1.4K

Completed (Currently Editing and Re-uploading) JASMINE haifafiyar kasar ingila (England) ce. Ya'a ga hamshaki... More

🌷JASMINE🌷
🌷Shafi na 1🌷
🌷Shafi na 2🌷
🌷Shafi na 3🌷
🌷Shafi na 4🌷
🌷Shafi na 5🌷
🌷Shafi na 6🌷
🌷Shafi na 7🌷
🌷Shafi na 8🌷
🌷Shafi na 9🌷
🌷Shafi na 10🌷
🌷Shafi na 11🌷
🌷Shafi na 12🌷
🌷Shafi na 13🌷
🌷Shafi na 14🌷
🌷Shafi na 15🌷
🌷Shafi na 16🌷
🌷Shafi na 17🌷
🌷Shafi na 18🌷
🌷Shafi na 19🌷
🌷Shafi na 20🌷
🌷Shafi na 21🌷
🌷Shafi na 22🌷
🌷Shafi na 23🌷
🌷Shafi na 24🌷
🌷Shafi na 25🌷
🌷Shafi na 26🌷
🌷Shafi na 27🌷
🌷Shafi na 28🌷
🌷Shafi na 29🌷
🌷Shafi na 30🌷
🌷Shafi na 31 🌷
🌷Shafi na 32 🌷
🌷Shafi na 33🌷
🌷Shafi na 34 🌷
🌷Shafi na 35🌷
🌷Shafi na 36🌷
🌷Shafi na 37🌷
🌷Shafi na 38🌷
🌷Shafi na 39🌷
🌷Shafi na 40🌷
🌷Shafi na 41🌷
🌷Shafi na 42🌷
🌷Shafi na 43🌷
🌷Shafi na 44🌷
🌷Shafi na 45🌷
🌷Shafi na 46🌷
🌷Shafi na 48🌷
🌷Shafi na 49🌷
🌷Shafi na 50🌷
🌷Shafi na 51🌷
🌷Shafi na 52🌷
🌷Shafi na 53 🌷

🌷Shafi na 47🌷

1.6K 126 65
By Amiratuoo

A tsaye Alamin ya tarar da ita rike da kofi a hannunta tana waya a lounging area da ke cikin suite dinsu, karasawa wajen yayi ya zauna akan kujera yana jiran ta gama wayar. Tana kashe wayar ta juyo tana kallon fuskarsa da ke dauke da murmushi, a hankali tace "Good morning M,"

Turbune fuska Alamin yayi yace "What is good about this morning, bayan kin bar ni ni kaɗai a ciki,"

Dariya maganar tasa ta bata ganin yadda yayi maganar kamar wani karamin yaro, "Amma what was I suppose to do, na tashi daga bacci me zanyi kuma akan gado,"

Jingina Alamin yayi a jikin kujerar da ya samu ya zaune yana murmushi "I can think of a thousand things," ya faɗa hade da kashe mata ido daya.

Girgiza kanta kawai Jasmine tayi ta dauke fuskarta dan boye murmushin da ke kokarin fitowa, a hankali ta daga kofin da ke hannuta ta kurbi hot chocolate din da ke ciki sannan tace "Yanzu dai, what do you want for breakfast?" Sannan tayi nuni da wajen cin abinci da ke suite din "Though nasa an kawo mana English breakfast,"

Mikewa Alamin yayi yana kallon kofin da ke hannuta yace "I want that?"

Kofin da ke hannunta ta daga tace "Hot Chocolate?"

A takaice ya bata amsa "Eh," sannan ya kara matsowa inda take yasa hannunsa ya janyota kusa da shi.

"Is it nice?" ya tambayeta yana kallon hot chocolate din da ke hannunta.

Girgiza kai Jasmine tayi tace "Uhmm," tana mismis ta bakinta, tana kara kurba Alamin ya haɗe bakinsa da nata, a hankali ya dago kansa yana tsotsar bakinsa kafin yace "I love it, zan kara," yana kallon bakinta.

Kallonsa kawai Jasmine ta tsaya tana yi ta kasa cewa komai, "I want more," ya kara maimaitawa. Hannu a sanyaye Jasmine ta daga kofin ta mika masa.

Girgiza kai yayi yana kallon kofin yace "Nope, you are going to feed me,"

Sakin baki tayi tare ta juya kwayar idanunta tace  "You are not serious,"

Mumushin nan na gefen baki yayi yace "Trust me love, I am," Juyawa Jasmine tayi zata bar wajen yasa hannayensa biyu ya rike ta.

Murmushi tayi tace  "Let me go M, and stop acting like a baby,"

"But I am your baby," ya bata amsa yana dariya.

Dariya Jasmine tayi amma kafin ta bashi amsa ya jata suka nufin dinning area din suite din. Kujera Alamin ya janyo ya zauna sannan ya janyo ta ta zauna akan cinyarsa, kokarin mikewa tayi ya riketa.

"Come on M, ka cika ni mana I want to sit,"

"You are sitting," ya bata amsa tare da sa hannu ya cire mata rubber band din da ke rike da gashinta.

Turo baki Jasmine tayi tace "Amma, I am not comfortable,"

"Ouch, that hurts," bata rai Alamin ya dan yi na wasa "Don't tell me kin fi son kujerar nan akai na, I am softer,  cuddly and fluffy,"

Tuntsurewa da dariya tayi tace "Fluffy sai kace wani cotton candy,"

Sautin dariyar ta ce ta sa shi murmushi a hankali ya sumabaci gefen fuskarta sannan yace "Speaking of candies reminds me, ina Ayeesh?"

Karkatowa Jasmine tayi tana kallon fuskarsa tace "Lallai, father of the year, sai yanzu ka tuno da ita."

Murmushi mai sauti ya saki yace "Father of the year, come on." 

"Eh mana, yaushe rabon da ka ganta amma ko tambayarta baka yi,"

"Shikenan, I am sorry Mama bear zan rika tambayar ta. Yanzu tana ina?"

Saboda gajiya da tayi da yanayin zamanta yasa Jasmine ta gyra zamanta ta jingina ajikinsa sannan tace "Tana gidan mu, I got her a new nanny bana son ina yawo da ita, she is a baby jinkinta bai yi kwari ba,"

Murmushi Alamin yayi ya gyra mata gashinta da ya zubo gefen fuskarata yana jin dadin sakin jikinta da tayi da shi, a hankali yace "That's very thoughtful, yanzu me zamu fara ci?"

"Ka zaba, what do you want?"

"Duk abunda zaki ci,"

Murmushi kawai jasmine tayi ta dauki fork da yar wuka ta yanko sausage ta kawo masa daidai bakinsa, a haka ta rika bashi abinci yana ci itama tana ci, suna dan taba hira tare da tsokanar juna.

Kwankwasa kofar suite dinsu da aka yi ne yasa Jasmine juyawa ta kalleshi tace "Are we expecting someone?" kokarin mikewa tayi Alamin ya riketa yace "Just ignore it love,"

"Indan emergency ne fa,"

"Ba shi bane,"

Murmushi kawai tayi ta mike zata je ta bude kofar shima yayi saurin mikewa ya riko "Ki tsaya a nan, lemme open the door,"

Alamin yana bude kofar yaga Nadia a tsaye, fuskarsa cike da mamaki yace "Nadia?"

"Yaya Alamin ina kwana," ta gaishe murya a makale cike da yanga har da dan durgusawa.

Shiru Alamin yayi ya matsa mata ta shigo sannan ya rufe kofar. Tsayawa yayi yana jiran tayi magana. "Uhmm.. Yaya Alamin daman magana na zo muyi,"

Tsayuwarsa ya gyra yace "Okay, ina jin ki,"

Cikin suite din ta kalla ta bude bakinta zata yi magana ta hango Jasmine ta fito daga dinning area, a take taji kamar an chaka mata mashi a cikin zuciyarta dan gabaki daya shirinta rugujewa yayi ya narke tamkar gishirin da aka kwarawa ruwa, har sai da fuskarta ta nuna ranta ya baci duk da tayi saurin rufe bacin ran da murmushi amma sai da Alamin ya gani. Ita a zatonta Jasmine ta na dakin Marianna dan taga anan ta sauka, sam bata yi zaton zata sameta a nan ba.

A hankali Jasmine ta karaso wajen tana kallon kayan jikin Nadia. Da kyar ta iya rike dariyarta, tana juyawa kuwa suka hada ido da Alamin ta gane shima dariyar yake rikewa. Mamaki ne ya kamata ganin Nadia tayi irin shigarta, hatta irin tattarar da take yi da gashin kanta shi Nadia tayi da Brazillian wig din da ke kanta, gashi tasha makeup sosai, tayi kyau ba wai bata yi kyau ba sai dai kwaliyar tayi saffiya da yawa sannan kana kallon shigar indai ka san Jasmine to kasan ita ta kwaikwaya.
Murmushi Jasmine ta sakar mata sannan tace "Yanzu ko muke breakfast, please join us,"

Murmushin yake Nadia tayi sannan tace "Ina kwana bamu gaisa ba,"

"Lafiya, muje," Jasmine ta nuna mata hanya tare da yin gaba Alamin yana biye da ita a baya. Kujerar da ke kallon ta Alamin Nadia ta Jawo ta zauna. Jasmine ta janyo kujera zata zauna Alamin ya janyota ta fado kan cinyarsa, daidai kunnenta ya kai bakinsa ya rada mata magana cikin harshen Spanish. Murmushi kawai Jasmine tayi ta saki jikinta,  hannu Alamin yasa ya gutsuro Sausage ya kawowa Jasmine bakinta ta karba, kumatunta ya sumbata sannan shima ya kai wani bakinsa.

Zumbur Nadia tayi ta mike dan ji take kamar ta kurma ihu a wajen saboda tsabar takaici da bakin ciki, wato a gaban idanunta zasu yi wannan barikin ko kunyar babu, to kara baza su yi mata ba.

Da sauri Alamin yace "Aa ina zaki kuma baki fada min abunda ya kawo ki ba, ki zauna mana,"

Komawa Nadia tayi ta zauna tana kallo Jasmine ta dago kofin hot Chocolate dinta ta kai wa Alamin bakinsa ya sha sannan itama ta sha. Runtse idanunta tayi tana bawa zuciyarta hakuri kar tayi abunda zai sa ta barar da garinta gaba daya. "Daman, na zo ne akan maganar komawa ta gida," Nadia ta faɗa a hankali tana kokarin haɗa karyar da zata faɗa dan ba abunda ya kawota ba kenan.

"Ina jinki," Alamin ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, gabaki daya hankalinsa yana kan Jasmine da ta dauko yankan pancake ta kawo masa daidai bakinsa. Ajiyar zuciya Nadia ta saki tare da sunkuyar da Kanta  kasa dan sam bazata iya cigaba da kallonsu a haka ba. "Daman so nake na biku Germany idan zaku tafi ni ma na dubo jikin Abba,"

Sai a lokacin Alamin ya juyo ya kalleta yace "That's fine, gobe zamu tafi sai ki shirya around 3pm zamu tashi."

Kakalo murmushi tayi tace "Alright, nagode," sannan ta mike da sauri tace "Na tafi," cikin hanzari ta fita daga suite din saboda kar kukan da take dannewa ya subuce mata a gaban Jasmine.

Tana fita Jasmine ta kalli Alamin suka hada ido sai suka tuntsure da dariya a tare, sunfi minti daya suna dariya da sun kalli juna sai dariyar ta sake kubuce masu, da kyar Jasmine ta tsayar da da dariya ta tace "She really loves you M,"

"What makes you say that?" Alamin ya tambayeta yana kokarin tsayar da tasa dariyar.

Murmushi kawai Jasmine tayi tace "Nothing," sannan ta mike daga kan cinyarasa.

"Ina zaki?" Yayi saurin tambayar ta.

"To get ready for the day," ta bashi amsa tare da yin hanyar kafar benen da ke cikin suite din su. Murmushi kawai ya bita da shi har ta bace masa da gani.

Jasmine tana fitowa daga bandaki ta tarar da Alamin a zaune akan kujera sanye da sababin kaya da alama bayan ta shiga Wanka shima wankan yayi a daya dakin. Ganin bai dago kasa daga kan wayar da ke hannunsa ba yasa Jasmine ta bata rai, takowa ta tayi har inda yake ta leka cikin wayar tasa taga hotunanta yake kalla, wayanda ma bata san sanda ya dauke su ba dan, har da wanda tana bacci ya dauke shi "Oh My God, yaushe ka dauki wannan hoton?" ta tambayeshi tana kokarin karbar wayar da ke hannunsa, amma kafin ta kai ga karba ya kasha wayarsa ya dago yana kallonta "Yesterday, lokacin da kikai bacci?"

Turbune fuska Jasmine tayi tace "Gaskiya ni dai ka bani na goge hoton nan banyi kyau ba, ka rasa sanda zaka yi min hoto sai ina bacci."

Mikewa Alamin yayi yana dariya yace "I don't think so love, beside ni hoton yayi min kyau, you look cute when you sleep."

Bata rai Jasmine tayi ta buga kafar ta a kasa kamar wata karamar yarinya ta chuno baki tace "To bani na sake ganin hoton,"

Dariya Alamin ya fara yi ya daga hannunsa sama tare da wayar a ciki yace "No matter how cute you look Love, bazan baki ba, ina son hoton."
Daga gira daya Jasmine tayi "Really?" ta tambaya tana kallon idanunsa, murmushi tayi ganin ya zuba mata idanu yana kallonta irin ko me za ta yi ba zai bata ba. A hankali tace "That sounds like a challenge," 

Shiru yayi bai bata amsa ba, hakan yasa tayi murmushin ta masa kusa da shi. Dan yatsanta daya tasa akan fuskarsa tana ja a hankali kamar mai tafiyar tsusa har izuwa wuyansa, sannan ta saki sauran yatsunta ta janyo shi a hankali yadda zai yi daidai da tsayinta. Bakinta takai dai dai kunnensa ta sumbata a hankali sannan ta fara magana muryarta a sanyaye tamkar mai rairai waka cike da yanga ta fara cewa "I...I.... Lo...vee...Love.."  tare da daukan lokaci kafin ta karasa da "PIZZA," cikin sauri ta janye jikinta daga nasa tana dariya.

Wani irin kallo Alamin yayi mata yana murmushi, hannunsa ya kalla yaga babu wayar a ciki, bai san lokacin da ta karba ba dan gabaki daya hankalinsa baya jikinsa lokacin da take masa magana.

"Mema kake cewa dazu?" Jasmine ta tambaye shi tare da daga wayarsa da take hannunta tana girgizata.

Bude baki yayi zai yi magana sai kuma dariya ta kubuce masa ya sunkuyar da kansa, yana dagowa yayo kanta da gudu. Dan karamin ihu Jasmine tayi kafin ta taka a guje.

Biyota yayi da gudu, suka ringa gujeguje kamar kananun yara a cikin suite din da kyar ya iya kamota. Yana rikota ta ya hade hannayenta biyu a waje daya ya riketa gam. "Why did you do that?" ya tambayeta tare da gyra rikon da yayi mata.

Jingina kanta tayi a jikin bangon da take jiki, tana haki tace "You started it,"

"Wato challenge ne?"

Wani kyatacen murmushi tayi tace "Definitely,"

"Amma, ai that was cheating, kuma ma ni bansan ya zama challenge ba,"

Girgiza kanta tayi tana kallon cikin idanunsa tace "Oh dear, no one smarts plays fair musamman a fanin soyyaya,"

Dariya Alamin yayi sosai har sai da dimple dinsa ya lotsa "You are you using my words against me," ya faɗa tare da cika mata hannayenta.

Gwalo Jasmine tayi masa tace "Ai bani na sa ka faɗa ba," sannan tayi gaba zata bar wajen, hannunta ya riko yace "Not so fast, wannan wasan bai kare ba,"

Girgiza kai tayi tana murmushi tace "Kai ma kasan ba zaka kai labari ba, you are going to fail,"

Murmushin nan na gefen baki yayi yace "Haka kika ce, uhm all this confidence ina ya tafi jiya da daddare?" 

Jasmine ta bude baki zata bashi amsa karar bugun kofa ya katseta. Tsaki Alamin ya yi hade da bata rai, ita kuwa Jasmine dariya abun ya bata "Why can't they let us be,"  Alamin ya faɗa hade da sakin wani tsakin.

Cikata Alamin yayi ya je ya bude kofar suite din, Personal Assitant dinsa ce Jalila ta shigo "Good morning Sir," ta gaishe shi tare da rufe kofar da ke bayanta. Jasmine ta kalla da ke tsaye a chan gefe ta aika mata da dan Ƙaramin Murmushi sannan tace mata "Hi,"

Da kyar Jasmine ta mayar mata da murmushi ita ma tace mata "Hi," sannan ta wuce ta hau stairs din da zai kaita Bedroom din da suka kwana, dan har yanzu bata son Jalila. 

Ciki Alamin ya wuce ya samu waje ya zauna akan kujera itama Jalila ta zauna akan wacce take kallon tasa sannan ta fara yi masa  bayani akan abunda ya kawo ta wajen sa. Sun fi minti ashirin suna tattaunawa kafin Jalila ta tafi. 

Jalila na fita Alamin ya bi Jasmine bedroom din, akan kujera ya sameta a zaune tana daddanna wayarta. Wadrobe ya bude ya dauko suit dinsa ya ajiye a kan gadon, dago kanta Jasmine tayi ta kalleshi ganin ya fara cire kayansa, suna hada ido ya kasha mata ido guda ya cigaba da abunda yake. Girgiza kanta kawai Jasmine tayi dan har ta fara sabawa da irin wannan halin na Alamin, kanta kawai ta sunkuyar ta cigaba da daddanna wayarta. Yana gama saka kayan ya karaso in take ya zauna a kusa da ita. Hannunta ya kamo a hankali yana dan daridari dan shi kansa yasan bazata so abunda zai faɗa mata ba. Iska ya fusar daga bakinsa kafi yace "Love," kashe wayarta Jasmine tayi ta juyo dan ta saurare sa.

"Na manta gabaki da da schedule dina, kinsa I came here for business and ina da meeting yau da wasu potential investors, ga kuma media conference akan sabon company da muka bude tare da Jamal."

"Shiyasa ka chanja kaya, wato tafiya zaka yi ka bar ni ni kadai bayan kace we are going on a date today," 

"Da ina da zabi babu inda zani I do rather stay here with you but amma, I have to make money for us love,"

Zumbura baki Jasmine tayi ta juya masa baya. Dan kalaman nasa basu gamsar da ita ba "But you promised me,"

Rungumeta ta baya yayi sannan ya sumbaci gefen kanta yace " you know I love you right, gabaki daya na manta da schedule dina and I thought baza ki zo ba da ba haka zan tsara abubuwa ba,"  

"Amma......" fasa karasa maganar da ta fara tayi sai kawai tace "You know what, it's actually fine ka tafi meeting dinka," sunkuyar da kanta tayi bata kara cewa komai ba.

Ganin ranta abace yasa ya sa hannunsa a kafadarta ya juyo ta ita tana kallonsa sannan ya kamo hannayenta yace "Ina kike so mu fara zuwa?"

Cike da farin ciki ta dago kanta tana kallon kwayar idanunsa tace "Ka fasa fita?"

Murmushin yayi har cikin ransa yana jin dadin faranta mata da yayi "Eh, na fasa." Ya furta a hankali "We can go wherever you want and do whatever you want, I am all yours, but you have to convince Jamal yaje meeting dinnan a maimako na, dan nasan ba ji maganata zai yi ba bayan tafiya da nayi na barsa da mutane jiya, amma nasan zai ji taki."

Yar karamar dariya Jasmine tayi tace "Fine, zanyi masa magana na san zai yarda. Media conference din fa?"
"It is just a one hour thing, zaki raka ko?"

Murmushi Jasmine tayi masa tace "Eh, lemme go and get dress,"

Jasmine tana fitowa Alamin ya mikewa tsaye murmushi kan fuskarsa ya kara fadada, "You look beautiful Wife," ya faɗa a hankali yana takowa inda take.

***
A kofar suite din Jamal suka tsaya suna jiran ya bude musu kofa. Marianna ce ta bude masu kofar suka shiga ciki.

"Jamal are you seeing what I am seeing," Marianna ta tambayi Jamal ta masa nuni ga Jasmine da kwayar idanunta.

Mikewa tsaye Jamal yayi ya karaso inda suke suka gaisa da Alamin sannan ya kalli Marianna yace mata "Cous, do you know who she is?"

Girgiza kanta Marianna tayi itama tana Kara karewa kayan jikin Jasmine kallo tace "Nope, but she looks familiar,"

A tare suka juya suka kalli Alamin, Jamal yace "Who is this?"

Murmushi Alamin yayi shima ya biye masu yace "My bad I forgot to introduce her, This is Yasmine, I met her on my way here."

Wani mugun kallo Jasmine ta watsa masu "Seriously guys, this is not the first time I wear clothes like this,"

Marianna ce tayi saurin cewa "No, but this is my first time seeing you fully clothed like this with your hair fully covered,"

Juya kwayar idanunta Jasmine tayi ta wuce ta je ta sami wuri ta zauna ta barsu a tsaye. Jamal ne ya biyota yana cewa "I think you look really pretty when you dress decent Little Sis,"

Turo baki Jasmine tayi ba tace komai ba kawai ta matsa masa ya zauna a kusa da ita.

"It's true you look beautiful," Marianna ta faɗa tare da samun waje ta zauna a kusa da Jasmine. Tureta Jasmine tayi tace mata "Todavía estoy enojada contigo, déjame en paz," (Ni fa haushin ki nake ji, gwanda ma ki kyale ni)

Tuntsurewa da dariya Marianna tayi tace "Se por que está enojada, no tengo  que preguntar," (Na ma san dalilin fushin na ki ba sai na tambaya ba)

Girgiza kanta Jasmine tayi tanan kallon Marianna wato dai bazata taba chanja hali ba, "Where is your husband?" Jasmine ta tambaye ta.

"Ah, he  travelled today, work and stuff,"

"Oh," kawai Jasmine tace sannan ta juyawa wajen dan uwanta Jamal, lankwasar da kanta tayi a shagwabe tace "Hermano mayor,"

cikin sauri Jamal ya mike tsaye yana cewa "We  are definitely not doing this," Dariyar da Alamin yaga Marianna na yi ne ya sa shi tambayar Jamal "What are you not doing?"

Juyawa Jamal yayi ya kalleshi yace "Tunda kaga ta fara haka abu zata tambaye ni, and I know I won't like it,"

Bata rai Jasmine tayi ta dauke kanta tace "Shikenan, tunda baza ka iya taimakawa yar uwarka ba," mismis tayi da idanu kamar zata yi kuka nan da nan Jamal ya koma ya zaune a kusa da ita, hannunta ya kamo yace "Tell me, what do you want cupcake,"

Yatsina fuska Jasmine tayi tana kallonsa tace "Cupcake, kasan bana son petname dinnan but I will let it slide," sai ta dan yi murmushi sannan ta cigaba da cewa "Daman so nake, kaje meeting dinnan in place of Alamin, please,"

"What? Why?" Jamal ya tambayi ta sannan ya juya ya kalli Alamin da ke zaune akan kujera yana kallonsu cikin nishadin kamar mai kallon film. Wani irin mugun kallo Jamal ya watsa masa, Alamin ya mayar masa da murmushi mai hade da dariya.
Jasmine ce tasa hannu ta juyo da fuskar Jamal gareta tace "Please Jamal we are going on a date today, kai fa kayi alkawari komai nake so za rika yi min,"

Nunfasawa Jamal yayi ya sakar mata murmushi yace "Fine, have fun," sannan ya juya ya kalli Alamin yace "Zan rama ni ma,"

Murmushin nan na gefen baki kawai Alamin yayi bai tanka masa ba duk da yasan tabbas sai Jamal ya rama, tunda ba yau suka saba yar haka ba.

*****
ATLANTIS HOTEL, DUBAI

Juyowa Alamin yayi yacewa Jasmine "How do I look?"

Murmushi Jasmine tayi ta tako inda yake tasa hannunta ta gyra masa necktie dinsa sannan tace "You look Handsome, Husband,"

Murmushi yayi ya sumbaci goshinta sannan yace "Are you sure ba zaki bini interview dinnan ba,"

Girgiza kai Jasmine tayi ta bude wayarta ta mika masa, Heading din articles har guda hudu na Gidan Jaridu daban daban ya gani akanta. Na farkon ya fara karantawa. 

Prince Matthew's Fiancée Jasmine Alejandro spotted with Billionaire Businessman Alamin Attah at an event in Dubai.

Cheating or Friendship : Prince Matthew's betrothed Jasmine Alejandro spotted with a billionaire socialite. 

Mika mata wayar kawai Alamin yayi ba tare da ya karasa karanta sauran headings din ba. Karbar wayar Jasmine tayi tace "We should thank God har yanzu tabloids and paparazzi's dinnan basu gano ni matarka ba ce,"

Bata rai Alamin yayi yace "Is being my wife a bad thing?"

Girgiza kai Jasmine tayi tace "No, bah aka nake nufi ba, idan suka gano abun zai zame mana scandal it will be very bad musamman da Matt yayi proposing a airport few days a ago, we have been trending a internet har yanzu maganar bata mutu ba achan Europe, it's a big deal a wajen su kasan royal stuff. And idan aka gano ina da aure abun zai zama Kaman I am cheating with him, so it's better mu bi a hankali, I don't want to taint our reputation."

Murmushi kawai Alamin yayi ya sumbaci kanta sannan yace "Alright, na gane,"

P.A din Alamin, Jalila ce ta shigo cikin dakin da Alamin ya kama saboda taron tace "Sir, komai ya shiryu, yan jaridan na jiranka a hall din," 

Gyda kai yayi kawai bai ce mata komi ba ta fita, tana fita yacewa Jasmine "Alright love, wish me luck,"

"Good luck, Allah ya taimaka," Jasmine ta faɗa tana murmushi.

Janyota jikinsa Alamin yayi yace "I want a goodluck kiss,"

Girar daya ta daga tace "Goodluck kiss, uhhh?"

Girgiza kai yayi "Eh, I want one,"
Murmushi kawai tayi ta lumshe idanunta ya hade bakinsa da nata.

*******

"How was the media conference?"
Idanunsa Alamin ya dauke daga kan titi ya kalleta yace "It was okay, amma kinsan sai da suka yi min tambaya akanki,"

Juyowa Jasmine tayi tana kallonsa tace "Daman na sani, what did they ask about?"

"Kamar dai yadda suka saba, wai suna son su san alakar da ke tsakaninmu, at first nayi masu shiru sai wani ya sake tambayata akan rawar da mukayi tare jiya a gala," Shiru Alamin ya danyi yana tuki sannan ya cigaba da cewa 'I told them wannan ba taro bane akan alakata da mutane ba, it's about our new company, hence all questions should be related to it,"

Gyada kai Jasmine tayi "That's a smart repond amma kasan it will only make them more curious sai mun yi taka tsantsan because I don't want them following me duk inda naje,"

Murmushi Alamin yayi yace "Well, ni dai I can't lie that ke ba matata bace but zamu iya ce masu ke cousin dina ce,"

Hade girarta Jasmine tayi tace "Amma ai we are not,"

Murmushi mai sauti Alamin ya saki yace "Ofcourse we are, maternal cousins, Aunty Kaulat is my Aunt,"

Bude bakinta Jasmine tayi tana kallonsa tace "Ta yaya aka yi bansan da hakan ba, baka taba gaya min ba,"

Juyowa Alamin yayi ya kalleta yace "Well, maganar ce bata taba tasowa ba,"

Lumshe idanunta Jasmine tayi ta jingina a jikin kujerar motar tace "Ya Allah, I was so oblivious to things happening around me, I never really ask you tayaya  ka gano inda mahaifiyata take because ban taba baka wasu details akanta ba,"

Parking Alamin yayi yace "We have a lot to talk about love, amma ki bari in munje gida mayi maganar. Yanzu dai lets enjoy our date," Shiru kawai Jasmine tayi tana kallonsa ya fita daga motar ya zagayo inda take ya bude mata kofa ta fito.  Hannunta ya rike suka fara tafiya.  

Juyawa Jasmine tayi ta kalli stable din da ke gabanta sannan ta sake kallon Alamin tace "Wai kamanta cewa bana hawa horses,"

Murmushin gefen baki Alamin yayi "Ko dai kina tsoronsu ba," ya faɗa cikin tsokana.

"Na ji, ai gwanda ni ba doll nake tsoro ba,"

Sunkuyar da kai yayi yana dariya yace "Fair enough," Jan hannun ta yayi ya zaunar da ita akan wani bench ya tsuguna a gabanta,takalmin kafarta ya cire mata ya samata boot din da aka basu sannan shima ya saka nasa.

Fito masu da dokin wani maikacin Musshrif park ya yi ya bawa Alamin lizamin dokin ya tafi ya barsu a wajen, rike dokin Alamin yayi yana shafa gashinsa, a hankali ya dago idanunsa ya kalli Jasmine da ke gefe guda tana kallonsa. Murmushi yayi mata yace "You know, it won't hurt you babu abunda zai miki,"

Kasa Jasmine tayi da kanta tana wasa da yanyatsunta tace "I hate to admit it but I'm scared not a phobia kinda thing kawai ina dai jin tsoronsa,"

"I understand shiyasa na kawoki nan, because I believe our greatest achievements are overcoming our fears, and it is one of the best feelings knowing that you no longer fear it," hannu daya ya mika mata yace "Come love, give it a try,"

Dogon nunfashi ta shaka sannan ta tako a hankali ta sa hannunta a cikin nasa. Murmushi Alamin yayi mata ya matso da ita kusa da shi. A hankali ya daga hannuta ya dora a saman dokin, hannunta Jasmine ta kalla sai ta kalleshi ta fara murmushi "I touch it," ta faɗa tana yar dariya.

Murmushi yayi yace "Yes you did, yanzu pet him,"

"How?" ta tambaye shi.

Dawo da ita gabansa yayi sannan ya sa hannunsa daya a kugunta ya riketa daya hannun kuma ya dora akan nata da ke kan dokin yana nuna mata yadda zata yi. Ta fi minti biyu tana petting din dokin kafin yace mata "Are you ready, zaki iya hawa dokin yanzu?"

Nunfasawa tayi tace "Yeah, I think so,"


Murmushi yayi ganin haryanzu tana jin tsoron sai dai ba kamar da ba, "Ki rufe idonki," ya rada mata a kunneta tare da sumbatar fatar kunnenata. Hannunta ya janye daga jikin dokin ganin ta rufe idanunta, a hankali ya dagata  ya dorata akan dokin sannan shima ya hau. Hannayensa yasa ya riko linzamin dokin sannan yace mata "Open your eyes,"

Dariya Jasmine ta fara yi ganinta a kan dokin amma ba tace komai ba suka fara tafiya akan dokin a hankali suna zagaye park din. Sunfi minti talatin akan dokin suna zagaye park din kafin Alamin ya sauka daga kan dokin ya rike linzamin dokin yana yawo da ita. Sai bayan wasu lokuta suka koma bakin stable, wani daga cikin maikatan wajen ne ya zo Alamin ya mika masa linzamin dokin sannan ya sauko da Jasmine daga kan dokin.

Tana saukowa kuwa ta rungume shi tana dariya, "Thank you so much M," Rungumeta shima Alamin yayi yana murmushi.   

"Yanzu ina zamu je?" Jasmine ta tambayi shi tana saka seatbelt.

Murmushi yayi yace "I can't tell you love, idan munje zaki gani,"

"I thought this was a date ba surprise spree ba,"

"You will love it, amma it's quite adventurous,"

Murmushi Jasmine tayi tana jinin jina maganar "Adventure," juyawa tayi ta kalli Alamin tace "I already love it."

Suna isa wajen Jasmine ta kalli Alamin tace "Sky dive?" Hannunsa ta rike tana nuna farin cikinta a filin "OMG, wannan date din is going to be the best date ever,"

Murmushin jin dadi yayi ganin irin farin cikin da ya sata "Yeah but first," Dinner in the Sky ya nuna mata yace "lets have brunch a chan,"

Murmushin fuskarta ne ya kara fadada tace "Perfect,"

Bayan sun shiga ciki aka basu waiver suka yi signing sannan suka zabi abinda zasu ci, Fingers Sandwish, Sacher torte with orange blossom da Scones sai Tea suka yi order. Ba'a jima ba staff din wajen suka zo suka sa su suka saka seat belts dinsu. Suna fara yin sama Jasmine ta kunna wayarta ta fara daukan video wajen, murmushi kawai Alamin yake yana kallonta yana jin dadin farin cikin da ya saka ta a ciki, sai da suka kai 50 meters sannan suka tsaya chak a saman. Staff din wajen ne ya yayi serving dinsu, hana Alamin cin abincin Jasmine tayi har sai da ta gama daukan pictures din abincin tukun, "Wai me zaki da videos and pictures dinnan haka,"

"Posting zanyi a snap and my Instagram," ta bashi amsa tana cigaba da daukan video sannan tace "Gyra zaman ka na daukeka hoto,"

Yar karamar dariya ce ta kubuce daga bakin Alamin amma bai ce komai ba ya gyra zaman nasa ta dauke shi hoton bayan ta gama masa hoton, shima wayarsa ya dauko ya mikawa Staff din da ke serving din su ya yi masu hotuna tare da Jasmine sannan suka fara cin abinci. 

Suna cin abincin Jasmine tace "Ya akai ka sama mana wajen nan, I thought last minute decision ne and you have to book ahead of time,"

Fork din da ke hannunsa Alamin ya ajiye yace "Yeah, I pulled a few strings and booked the whole place for privacy,"

"That's cool, shiyasa naga mu kadai ne," girgiza kansa Alamin yayi suka cigaba da cin abincin kafin Jasmine tace "This is my first time here, but I read about wajen nan a magazine, it's one of the ten most unsual restaurants a duniya, cin abinci a sararin samaniya not in a plane, I have always wanted to come."

Hannunta ta dora akan nasa tace "Thank you M,"

Murmushi yayi ya dago hannunta ya sumbata yace "It's my pleasure, and I am glad you like it, dan da farko na danyi kokanton ko bazaki so wajen nan ba, da Ossiano Restaurant zan kaiki naga it more of a luxurious girly kinda thing but changed my mind, a little adventure won't hurt,"

Wani irin kallon so tayi masa tace "Aww, that's so cute but indai adventure ne always sign me in,"

Dariya Alamin yayi yace "Sure," Shiru suka yi suka cigaba da cin abincinsu, Jasmine ce ta kara magana ganin shirun yayi yawa "Kana social media, I know kana da twitter account ka taba nuna min wannan trend din akaina, amma are you active like akan sauran social media platforms because ban taba cin karo da page din ka ba duk da muna da mutual friends,"

Tea din da ke hannunsa Alamin ya kurba sannan yace "Yeah, kawo wayar ki kiga," hannu ya mika Jasmine ta bashi wayarta ya shiga Instagram yayi typing username dinsa yana shiga page dinsa ya mika mata wayar. Da sauri Jasmine ta dago tana kallonsa tace "You have 16milllion followers," scrolling ta rika yi akan page dinsa tana ganin abubuwan da yake posting, yauwanci akan yawon shakatawa da suke zuwa da abokansa ne, irin su camping and adventures sai abubawa ga me da business dinsa, sama ta yo scrolling taga mutane ashirin kawai yake following, shiga tayi taga har da ita a cikin mutanen da yake following sai yan uwansa da wasu celebrities guda hudu, dago kanta tayi daga kan wayar tace "Yaushe kayi following din ban sani ba,"

"Sanda kika koma Uk," ya bata amsa.
Murmushi tayi tana kallon wani hotonsa da yayi posting tace "Ah dole ka samu followers irin wannan kyau haka, I bet rabinsu mata ne,"

Dariya Alamin yayi har sai da dimple dinsa ya lotsa, cikin tsokana shima yace "I can't help it, I mean take a look at this," nuni yayi da jikinsa tare da gyara jacket din jikinsa.

Tuntsurewa da dariya Jasmine tayi tace "Lallai I can see your head growing bigger kar dai ya fashe," dariya gabaki dayansu suka yi sannan Jasmine tace "You are not really that private na dauka baka posting komai a socials dinka,"

Murmushi Alamin yayi yace "I do, ina posting abunda nake ra'ayin mutane su gani mana not everything and not everytime, ni social media a wajena is a place of entertainment and networking,"

Girgiza kan ta Jasmine tayi tace "Well said, nima dai ina yi ne to have fun,"

Bayan sun gama cin abincin da hutawa SkyDive suka wuce domin karasa date dinsu. Suna isa kuwa wani daga cikin ma'aikan wajen yazo yayi maso iso dan sun san da zuwanasu, Bayan sun gama cike takardu, jumpsuit, helmet da parachute aka basu sukaje suka yi changing sannan suka fito, aka fara yi masu bayani akan yadda zasu yi skydiving, daga nan aka masu jagora zuwa airplane din za su hau, suka shiga ciki. Hannun Jasmine Alamin ya kamo ya rike "Are you ready for this?" ya tambayeta yana kallon kwayar idanunta.

Murmushi tayi ta girgiza Kanta "Amma, ina dan jin tsoro kadan,"

Hannunsa ya sakalo a kafadar ta yace mata "Kinsan I have always dream about doing crazy stuffs with my wife, I'm glad we are doing this together. You gonna be okay, ai kin iya remember that feeling lokacin da kika taba yi, flying is one of the most beautiful feelings in the world,  only a few are fortunate to experience it, just close your eyes and take a deep breath,"

Murmushi Jasmine tayi tace "Thank you," goshinta ya sumbata sannan yace "And it's a competition za mu ga wanda zai riga landing, and duk wanda ya riga zai fadawa wanda ya fadi wani abu da yake so yayi masa and dole sai yayi,"

Tsuke baki Jasmine tayi tana kallonsa ya kasha mata ido hade da sakin murmushi nan na gefen baki. Juyawa kwayar idanunta tayi ta girgiza kanta tace "The game is on," sannan ta dauki helmet dinta ta sa.

Bayan wasu yan mintuna Instructor su ne ya sanar masu lokaci yayi bayan jirginsu ya tsaya a 18,000 feet a sararin samaniya, daidai kofar jigin suka matso suka tsaya, juyawa Jasmine tayi ta kalli Alamin tace "I haven't done this for quite a while, I can't wait to jump,"

Murmushi kawai yayi mata ya mika mata hannunsa tasa nata a ciki, dogon nunfashi suka shaka a tare suna kallon juna sannan suka yi tsalle suka fito daga cikin jirgin, ihu Jasmine ta fara yi Alamin ya riko dayan hannun nata yana dariya, "Close your eyes and take in the freash air," ya fada mata da karfi dan ta ji shi. Hakan ko tayi sannan ta bude idanunta a hankali tana kallonsa, "Enjoy yourself, they are recording it and don't forget the game is still on," ya faɗa mata da karfi sannan ya cika mata hannayenta.

Kamar yadda ya faɗa tayi, sakin jikinta tayi ta na jin dadin yawo da take a iska, Bayan wasu yan mintuna ta saki parachute dinta. A hankali tayi landing. Tsabar farin ciki kuwa kasa rufe bakinta tayi, cikin sauri ta cire parachute dinta da ta hango Alamin, da gudu ta tafi wajensa shima ya taho suka hade akan hanya ta dafe shi, juyi ya fara yi da ita suna dariya sannan ya sauketa kasa suka kara rungume juna cikin farin ciki, "We did it Jasmine ta faɗa cike da farin ciki,"

"Yeah," Alamin ya bata amsa yana kallonta.

Suna zaune suna hutawa Jasmine ta kallesa ta ce "What's next?"

Murmushi yayi yace mata "Lets go shopping,"

"Dubai mall?"

"Aa,  Souks,"

Daga nan kasuwar gargarjiyata dubai suka je suka yi siyayya, Alamin ya siya mata Awarwaro na farin gold da dadogayen riguna da takalma, da kyar ya bari Jasmine ta siya masa zoben azurfa da agogon azurfa da kudinta. Daga kasuwar nan, dinner Alamin ya siyo masu a wani Chinese restaurant. Suna komawa gida. Wanka suka fara yi sannan suka ci abinci, sai bacci dan gabaki dayan su sun gaji saboda irin yawon da suka rika yi a ciki garin.


Don't forget to follow me and bombard me with questions or comments.

Instagram: @amiratuoo
Twitter: @amiratuoo
Facebook: Amina Umzak
Inkitt: @amiratuoo
Tiktok: @amiratuoo

Continue Reading

You'll Also Like

37.7K 3.6K 94
An Interesting Love story
274K 20.2K 28
Love between a muslimah and christian✍
219K 13.6K 44
Yanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resem...
37K 1.3K 32
Karki kashe! Tsura ma screen din wayar tayi tana kallo, ta rasa me Rayhan yake nufi da ita sam a rayuwarta. Send me you pic I wanna see that beautifu...