Jasmine Baturiyya ce

By Amiratuoo

117K 8.8K 1.4K

Completed (Currently Editing and Re-uploading) JASMINE haifafiyar kasar ingila (England) ce. Ya'a ga hamshaki... More

🌷JASMINE🌷
🌷Shafi na 1🌷
🌷Shafi na 2🌷
🌷Shafi na 3🌷
🌷Shafi na 4🌷
🌷Shafi na 5🌷
🌷Shafi na 6🌷
🌷Shafi na 7🌷
🌷Shafi na 8🌷
🌷Shafi na 9🌷
🌷Shafi na 10🌷
🌷Shafi na 11🌷
🌷Shafi na 12🌷
🌷Shafi na 13🌷
🌷Shafi na 14🌷
🌷Shafi na 15🌷
🌷Shafi na 16🌷
🌷Shafi na 17🌷
🌷Shafi na 18🌷
🌷Shafi na 19🌷
🌷Shafi na 20🌷
🌷Shafi na 21🌷
🌷Shafi na 22🌷
🌷Shafi na 23🌷
🌷Shafi na 24🌷
🌷Shafi na 25🌷
🌷Shafi na 26🌷
🌷Shafi na 27🌷
🌷Shafi na 28🌷
🌷Shafi na 29🌷
🌷Shafi na 30🌷
🌷Shafi na 31 🌷
🌷Shafi na 32 🌷
🌷Shafi na 33🌷
🌷Shafi na 34 🌷
🌷Shafi na 35🌷
🌷Shafi na 36🌷
🌷Shafi na 37🌷
🌷Shafi na 38🌷
🌷Shafi na 39🌷
🌷Shafi na 40🌷
🌷Shafi na 41🌷
🌷Shafi na 42🌷
🌷Shafi na 43🌷
🌷Shafi na 44🌷
🌷Shafi na 46🌷
🌷Shafi na 47🌷
🌷Shafi na 48🌷
🌷Shafi na 49🌷
🌷Shafi na 50🌷
🌷Shafi na 51🌷
🌷Shafi na 52🌷
🌷Shafi na 53 🌷

🌷Shafi na 45🌷

1K 78 18
By Amiratuoo

Wani irin kayataccen murmushi  ya saki ganin kayan da ya aika mata ne a jikinta. Ba karamin kyau kayan suka yi mata ba fiye da yadda yayi tsammani, ji yake kamar ya tafi da gudu ya rungumeta dan ba karamar kewarta yake ba, mussaman yanzu da yake kallonta a kusa da shi bai fi taku goma ne a tsakaninsu ba.

Ya daga kafa kenan zai fara takawa inda take ya hango wani bature ya riga shi zuwa wajenta, murmushi ya ga tayi wa baturen shi kuma ya karbi hannunta ya sumbata sai kuma suka bige da hira, tsayawa yayi yana kallonsu yana kokwanton ya je ko kar yaje wajenta.

Abunda James ya faɗa ne ya bawa Jasmine dariya tace “Goodness I missed a lot when I was in Nigeria,”
Murmushi James yayi ya mikawa Jasmine hannu yace “May I have a dance,”

Hannunta Jasmine ta sa a cikin nasa tace “Sure,” sannan suka nufi filin rawa inda mutane ke rawa tare da patners dinsu, suma suka fara rawar a hankali.

Suna cikin rawar James yace “I need your help Jas,”

“Okay,” Daga nan James ya fara faɗawa Jasmine kudirinsa na son yayi proposing ga kawarta Charlotte dan sun dade suna soyyaya, Jasmine shawarwari ta ringa bashi suna rawar suna tsara yadda zai yi abun ya zamo bazata a wajen charlotte.

Alamin yana tsaye yana kallonsu babu abunda yake in banda mugun kallon da yake aikawa James duk kishi ya bi ya lullube shi, ji yake kamar yaje ya  fincike James daga wajen mussaman da yaga ya faɗawa Jasmine wani abu ta daga kai tana dariya cike da nishadi. Abu daya ne ya hanasa karasawa wajen baya son yayi abun kunya a wajen tunda su awajensu turawa hakan ba wani abu bane amma shi duk abun yabi ya dame shi. Hannu Alamin ya ji an dora masa a kafadarsa ya juya yaga Jamal ne yake kallonsa, “Har ka gama yaudararta ta?” Alamin ya tambaye shi tare da juyawa gaba ki daya daga inda zai dunga hango Jasmine.
Murmushi Jamal yayi yace “Ba yaudararta nake ba, we were just catching up,”

Irin Murmushin nan na gefen baki Alamin yayi yace “If you say so,”

Girgiza kai kawai Jamal yayi bai ce komai ba sai kuma ya kalli bayan Alamin ya hango kanwarsa tana rawa da saurayin Charlotte James, muryar a dan kasa Jamal yace “You know you can get her away from him rather than standing here sending him daggers with your eyes,”

Juyawa Alamin yayi ya kalli Jasmine yaga har yanzu murmushi take, sannan ya juyo ya kalli Jamal yace “How?"

Yar dariyar mugunta Jamal ya danyi sannan yayi gyran murya cikin tsokana kafin ya fara magana “Well, first zaka samo dancing partner ku fara rawa awajen idan kunzo kusa dasu sai ka nemi kuyi swapping partners. Simple”

Wani rin kallo Alamin yayiwa Jamal kafi yace “Kafi kowa sanin bana rawa da matan da ba muharramai na bane,”

“I know,” kawai Jamal yace kafin ya kara da “That’s your first and polite option, da other one is a bit rude which is ka tafi kai tsaye and ask to dance with her….” Kafin Jamal ya gama rufe bakinshi Alamin yayi gaba. Yana isa inda Jasmine da James ke rawa ya taba kafadar James yace “May I dance with the beautiful Lady please?" 

Murmushi kawai James yayi ya cika Jasmine sannan yace mata “It’s a great pleasure dancing with you,” sannan ya bar filin rawar.

Dan karamin murmushi Jasmine tayi sannan ta juya ta kalli Alamin, tafin hannunsa ya bude ya miko mata yana kallon fuskarta, dan jim kaɗan tayi kafin ta saka hannunta a cikin nasa. Kusa dashi ta matso kadan sannan ta dora hannunta akan kafadarsa. Hannunta da ke kan kafadarsa ya kalla sannan ya juyo a hankali yana kallon fuskarta, shima yasa hannunsa a bayanta dayan hannunsa kuma rike da nata. A hankali suka fara takawa suna bin sauti instruments din da ake playing a wajen, juya ta Alamin yayi ta jingina da bayansa, a hankali ta daga kanta ta kalle shi sai kuma ta dauke kanta. Kamshin turaren gashinta da ya shaka ne ya sashi lumshe idanu tare da sakin ajiyar zuciyar, a hankali ya daga hannunta ya juya ta, ta maida hannunta kan kafadarsa suka cigaba da rawar. Babu wanda yace kala a cikinsu har masu playing instruments din suka tsaya. Ganin kidan ya kare amma Alamin bai cikata ba yasa Jasmine cewa “Kidan ya tsaya fa,” juyawa tayi ta kali gefe da gefen su taga mutane sun fara barin filin rawar amma bai cikata ta ba, kawai ya tsaya yana kallonta. Bata rai tayi, sai kuma taji sabon kida ya fara tashi har wasu mutanen sun fara tunkaro filin rawar suna haduwa da wayanda suka rage a ciki.

Matso da ita kusa yayi sosai tana jin saukar nunfashinsa akan fuskarta, a hankali ya dago hannunta da ke cikin nasa ya dora akan kirjinsa daidai saitin zuciyarsa har tana iya jin bugunta a karkashin tafin hannunta sannan ya dora hannunsa akan nata ya rike shi waje daya. Baya Jasmine tayi kokarin yi ganin fuskokinsu sun yi kusa da yawa amma ta kasa sabo irin rikon da yayi mata, a sanyeye ta dan daga kanta sai kuwa suka hada ido dan ya dade yana kallonta, kasa dauke idanunta daga cikin nasa tayi haka suka cigaba da rawar.

Ko da baka san su ba irin kallon da suke wa juna kawai ya isa ya tabbatar maka cewa tabbas su masoya biyu ne da suke dade da nutsewa a cikin kogin kaunar juna, dan ji suke tamkar su kadai ne a filin wajen. A hankali Jasmine ta kawar da kwarya idanunta daga cikin na Alamin sai dai bai daina kallonta ba.

Nadia da bata dade da shigowa ba kuwa kasa motsawa daga inda ta ke tayi saboda takaici da bakin ciki da ya mamaye mata zuciya, kyalin diamonds din da ke jikin rigar Jasmine ne yasa ta kasa daina kallon rigar, tasan kwaliyar da tayi ko kamo kafar ta Jasmine bata yi ba. Sai kuma ta lura da irin kallon da Alamin yake wa Jasmine tamkar ita kaɗai ce mace a wajen. Wato tayi kwaliya a banza kenan, ganin kwalla ta ciko a idanunta ne yasa ta daga kafafunta da kyar tana tafiya bata tsaya ba sai da ta isa inda babu mutane sosai ta juya tana kallon ruwan da ke gabanta hawaye yana zubowa a kan kuncinta. Sunanta da taji an kira ne yasa tayi saurin bude yar purse din da ke hannunta ta dauko handkichef ta dan daddana akan fuskarta sannan ta juyo. Mamaki ne yasa ta saki baki tana kallon mutumin da yake gabanta “Me kake yi anan Sabeer?” tayi saurin tambayarsa.

Murmushi Sabeer yayi yace “Gayyata ta aka yi, kuma naji labarin kin zo, gashi ina son na ganki that’s why I came,”

Bata rai Nadia tayi tace “I don’t understand kana son ka ganni, ko ka manta na fada maka whatever is between us ya riga da yakare,”

Tuntsurewa da dariya Sabeer yayi yace “Ya kare fa kika ce?”

Wata irin muguwar harara Nadia ta wurga masa tace “Eh, ya kare.”

Girgiza kai Sabeer ya fara yi yana zagaye Nadia kafin ya tsaya a gabanta “Har diyata da kike boye min?”

Wani irin gumi ne ya ketowa Nadia amma ta dake tace “Ba yarka bace!”

Murmushi Sabeer yayi yace “Na farko kin yaudare ni, sannan kin gujeni da kika sami wanda ya fini kudi, yanzu kuma ya’a ta zaki hanani?”

Nan da nan Nadia ta murtuke fuska tace “Ayesha ba yarka bace,”

Daga gira guda Sabeer yayi yace “Oh really, shikenan zanyi wa Yaya Alamin magana sai muje ayi DNA sai na tabbatar da ba ya'a ta ce ba.” Juyawa Sabeer yayi zai bar wajen Nadia tayi saurin riko hannunsa “Sabeer Please kar kayi min haka, naji yarka ce amma ka bari nayi maka bayani, lets go somewhere else,”

Basma na tsaye fuskarta dauke da murmushi tana kallon Alamin da Jasmine suna rawa ta hango Jamal, murmushinta kara fadada yayi saboda har yanzu bata daina crushing a kansa ba,  kallonsa ta cigaba da yi tana adduar Allah ya sa ya ganta yayi mata magana, sai kuwa ya juyo karaf suka hada ido, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa. Ta na kallo ya baro inda yake ya fara tunkaro ta amma kafin ya karaso wata baturiya ta tsayar da shi, bata rai Basma tayi ganin ya tsaya awajen baturiyyar suna hira, har tayi fushi ta juya zata bar wajen sai kuma taji ya kira sunanta. Wani irin farin ciki taji ya ratsa zuciyarta, da sauri ta juyo tana murmushi, har ya karaso inda take “Ina zaki je?” Ya tambaye ta.

Rasa me zata ce Basma tayi ta fara wasa da yanyatsunta, sai kuma tace “Uhhm… Dama ciki zan koma naji,”

Murmushi Jamal yayi yace “Da wuri haka, duk kwaliyar nan da kika yi ko baki san kin fi kowa kyau a wajen nan ba,”

Sunkuyar da kanta Basma tayi tana murmushi sannan Jamal ya cigaba da cewa “Yanzu dai we can’t let wannan kwaliyar go to waste, idan bakya son zama anan we can go and see dubai daman kinsa yawo da daddare yafi dadi a dubai,”

Dago kanta Basma tayi da sauri tace “Really?"

Girgiza kai Jamal yayi yace “ Yeah, I’ll let your brother know sai mu tafi ko,”

Murmushi Basma tayi tace “Okay, lemme go get a flat shoe sai na zo mu tafi,” cikin sauri Basma ta fara tafiya zata je restroom ta gyra kwaliyarta sannan ta dauko flat shoe. Tana shan kwana kenan ta hango Sabeer da Nadia suna magana, a hankali ta fara tafiya saboda wajen babu haske sosai irin dim light dinnan ne a wajen, so take tayi masu ba zata, dan bata san Sabeer ya zo taron ba, ita ko Nadia tun zuwansu basu sake haduwa ba. Maganar da taji suna yi ce ta tsayar da ita a inda take bata san sanda ta dauki hannu ta dora akan bakinta ba saboda mamaki.


Finally Baby Daddy Nadia ya bayyana!!!!!
Me Kuke tunanin zai faru ? Labari ya zo karshe sauran kiris

Ps: Sabeer Cousin din Khadija da Nadia ne ta bangaren mahaifiya, shi ne wanda suka taba haduwa da Jasmine lokacin da taje Breast Cancer awareness Abuja.

Continue Reading

You'll Also Like

ZUMA By Ta masu gari

Teen Fiction

52.2K 7.3K 44
A story of love ❤️ A heart deforming story💔😫 Ban taba sanin kuka yana saka ciwon ido ba se a kaina, na kasance Inada cika baki ko a cikin kawaye a...
1M 53K 46
အမိန္႔စည္း+သခြပ္႐ိုး ( ႐ွင္မႈန္းနံ႔သာ) အမိန့်စည်း+သခွပ်ရိုး ( ရှင်မှုန်းနံ့သာ) ခြင့္ျပဳခ်က္မရပဲ ငါ့အနားကထြက္ခြာခြင့္မျပဳနိင္ဘူး အသက္နဲ႔ခႏၶာတည္ျမဲေနသ...
280K 17.4K 73
" ရှင်က ၀န်ကြီးချုပ် ဖြစ်တယ် ဆိုတိုင်း ကျွန်မက ကြောက်ရမှာလား " " ဟင့်အင်း မကြောက်ရပါဘူး။လုံးဝကို ကြောက်စရာမလိုတာ။ထက်သာ ကသာ မကြီးကို သက်ဆုံးတိုင် ချစ...
52.8K 5.7K 30
GIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta y...