Jasmine Baturiyya ce

By Amiratuoo

117K 8.8K 1.4K

Completed (Currently Editing and Re-uploading) JASMINE haifafiyar kasar ingila (England) ce. Ya'a ga hamshaki... More

🌷JASMINE🌷
🌷Shafi na 1🌷
🌷Shafi na 2🌷
🌷Shafi na 3🌷
🌷Shafi na 4🌷
🌷Shafi na 5🌷
🌷Shafi na 6🌷
🌷Shafi na 7🌷
🌷Shafi na 8🌷
🌷Shafi na 9🌷
🌷Shafi na 10🌷
🌷Shafi na 11🌷
🌷Shafi na 12🌷
🌷Shafi na 13🌷
🌷Shafi na 14🌷
🌷Shafi na 15🌷
🌷Shafi na 16🌷
🌷Shafi na 17🌷
🌷Shafi na 18🌷
🌷Shafi na 19🌷
🌷Shafi na 20🌷
🌷Shafi na 21🌷
🌷Shafi na 22🌷
🌷Shafi na 23🌷
🌷Shafi na 24🌷
🌷Shafi na 25🌷
🌷Shafi na 26🌷
🌷Shafi na 27🌷
🌷Shafi na 28🌷
🌷Shafi na 29🌷
🌷Shafi na 30🌷
🌷Shafi na 31 🌷
🌷Shafi na 32 🌷
🌷Shafi na 33🌷
🌷Shafi na 34 🌷
🌷Shafi na 35🌷
🌷Shafi na 36🌷
🌷Shafi na 37🌷
🌷Shafi na 38🌷
🌷Shafi na 39🌷
🌷Shafi na 40🌷
🌷Shafi na 41🌷
🌷Shafi na 43🌷
🌷Shafi na 44🌷
🌷Shafi na 45🌷
🌷Shafi na 46🌷
🌷Shafi na 47🌷
🌷Shafi na 48🌷
🌷Shafi na 49🌷
🌷Shafi na 50🌷
🌷Shafi na 51🌷
🌷Shafi na 52🌷
🌷Shafi na 53 🌷

🌷Shafi na 42🌷

951 100 21
By Amiratuoo

Cambridge, England

Tunda Jasmine ta sauko daga kafar jirgi take ji wani iri a jikinta kamar wani abu ne zai faru amma ta rasa me nene. Juyawa tayi ta kalli baby Ayeesh da ke dauke a hannun Rahma, murmushi ne ya ziyarci fuskarta dan cikin sati biyu nan da tayi da ita jinta take tamkar yar da ta haifa a cikinta.
Satin biyu Jasmine tayi tana jiran dawowar Alamin gida, amma tunda ta baro shi a office dinsa bata sake sa shi a idanunta ba, baya kasar ma kwatakwata bare taje inda yake, Visar su  Ayesha da Nanny ta na fito ta tattara kayanta baro Nigeria dan ba zata iya cigaba da zaman jiransa ba, ba waya bare sako.

Suna tafiya a cikin Airport din ta fara jin hayaniyar wajen ta fara karuwa, gani tayi gaba daya hankalin mutanen ya karkata zuwa wani bangare na Airport din, tana juyawa taga mutane suna bawa wasu mutane hanya, karkata kanta ta tayi taga waye dan tasan bazai wuce wani celebrity din ne ba ganin yadda mutane suke ta daukar hotunansa yana tafiya .

Zaro idanu Jasmine tayi ganin mutum da ke tsakiyar bodyguards din ba kowa bane face Matthews. Me yake yi a Airport din nan?  Tambayar da tayiwa kanta kenan.

Tana gani ya tunkaro inda take tayi sauri ta juya dan bata son ya ganta "Wuce muje, da sauri," ta faɗawa Rahma cikin hanzari.

"I am sorry," murya Matthews ce ta tsayar da ita. Idanunta ta rintse dan tasan yau ta kade daga ita har ganyenta. Dan duk soyayyar da suke ita da Matthews a siri suke yinta, basu taba bari paparazzi ko wasu an jaridar sun gano abunda ke tsakaninsu gudu surutun jama'a, soyayyar su iya makusanta su ne kawai suka sani, dan ko kaɗan Jasmine bata da sha'awar ganin hotunanta kullum a jaridu da blogs kawai dan tana soyayya da wani. Tana gudun kar abinda ya sameta lokacin tana tare da Karl Rodriguez ya sake faruwa, yan jarida suyi ta binta duk inda ta shiga ya zamo babu wani sirri a rayuwata.

Hannuta ta damke sosai tana addua kar Matthew ya aikata wani abun dan rabuwar da suka yi ta karshe ba a cikin jin dadi bace. "I Love You Jasmine," taji ya faɗa da karfi.

A hankali ta juya ta ganshi tsaye a bayanta, gabaki daya mutane da ma ma'aikatan Airport din kowa tsayawa yayi yana kallon su, masu recording nayi, masu kunnawa live a social media dinsu ma na yi.

"I am so sorry I misunderstood you," Matthew ya faɗa tare da takowa kusa da ita.

Jasmine ji take kamar ta nitse a kasa "What are you talking about Matt, stop this nonsense right now. You're making a scene," Ta faɗa a hankali tana kallonsa da bata son ya cigaba da wannan surutan banza, idan Alamin ya gani tasan shikenan kuma musamman yanzu da yake fushi da ita.

Murmushi Matthews yayi ya kamo hannuta yace "It's not nonsense darling, I know you did what you did to help a friend in need and I forgive you,"

Bude baki Jasmine tayi ta rufe dan ji tayi gabaki daya bakinta ya bushe, wato yasan aurenta da Alamin ba na gaske bane. Kara matsowa kusa da ita Matthews yayi yana kallon cikin idanunta yace "I am sorry," a hankali dan ita kadai ta ji kafin ya fara magana da karfi kowa yana jinsu "Jasmine, You're my best friend for over 13 years, The Love of my life for over 4 years, I have known you for half of my life which felt my whole life, you're everything I ever wanted and need," A hankali ya duka da kafa daya a gabanta yasa hannu a aljihu ya ciro wannan dan karamin akwatin zoben da ya so yayi mata proposing da shi ya bude zoben yana kalli ya rike a gaban ta "Jasmine the love of my life and my everything, will you grant me the honor of being your life partner, Husband and best-friend forever."

Jasmine ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi a jikinta, gaba ki daya gabobin jikinta kasa motsi suka yi, da kyar ta iya daga kanta ta kalli dinbin mutanen da suka zagaye su kowa ya daga waya yana recoding din su, duk jiran amsarta suke. Da ace shekarun baya da suka wuce ne koma watanni 8 da suka shige da ta amshi zobensa cike da farin ciki saboda a lokacin babu kowa a zuciyarta sai shi amma yanzu komai ya chanja.

Wani dogon nunfashi ta shaka ta kalli Matthews yadda yake kallonta idanunsa cike da so da kauna, ba sai an faɗa mata ba ita kanta tasan yana kaunarta tsakani da Allah, ba zata iya disga shi a gaban mutanen ba. Wani murmushin karya ta kakalo har da yar karamar dariya tamkar na gaske dan duk iya gano abunka baza ka gane yake ta ke ba, zuciyarta babu abunda take in bada tunanin yadda Alamin zai dauki wannan abunda da take kokarin aikatawa. Cikin farin cikin karya tace "Yes my love, Yes..."
Cikin jin dadi mara misaltuwa Matthews ya zira mata diamond ring din nan a hannunta, wajen ya kaure da tafi da ihu, dagowa Matthews yayi ya rungumeta yana dariya kafin ya cikata ya riko fuskarta zai sumbace ta kamar yadda kowa keyi bayan anyi accepting proposal dinsa. Hankalin Jasmine ba karamin tashi yayi ba dan bazata iya bari wani namiji ya sumbace ta ba In ba Alamin dinta ba, ga shi har yanzu da auren Alamin a kanta, kuma a gaban mutane kai bazai yiwu ba. Ja da baya tayi tana murmushi tace "Matt, take me out of here, right now," sannan ta janyo mayafin rigar jikinta ta rufe fuskarta idanunta kawai ta bari a waje.

Dam Matt ya danyi yana kallonta dan ya fara ganowa dariyar yake take amma bai ce komai ba, hannunta kawai ya kamo suka yi hanyar fita. A kofar shiga Airport din kuwa Paparazzi ne cike jim kim dan har sun samu labarin engagement din. Su Jasmine na fitowa Hasken Camera ya fara dalle masu idanu, idanunta ne kawai a waje amma haka bai hana Paparazzi daukar hotunan su ba, sai da bodyguards din Matthew suke dunga ture mutane sannan su ka samu suka shiga cikin mota. Ayeesh da Nanny ta suma aka saka su a cikin wata motar.

Tunda suka shiga motar Jasmine ta daina murmushi sannan ba ta kara cewa kala bah koh da Matthew yayi mata magana har suka isa unguwarsu. Makeken gate din gidan da kansa ya bude motocin suka shiga ciki, Rahma da take cikin daya motar tare da baby Ayeesh , bude glass din motar tayi ta ziro kanta waje tana karewa gidan kallo dan gani take tint din motar ba zai barta ta kalli gidan sosai bah, tsabar haduwa gidan har miyau sai da ya diga daga bakin Rahma da tana kallon gidan.

Motocin na tsayawa Jasmine ta fito daga ciki ta bar Matthew, a daidai bakin kofar shiga cikin gidan ta tarar da Butler su Mr. Staline. Cikin fara'a ya tarbi Jasmine "Welcome back Home Miss Jasmine,"

Dan karamin murmushi Jasmine tayi masa tace "Thank you Mr Staline," sannan ta cigaba da cewa "Uhm, Can you please get my Daughter and her Nanny in, take them to my room and prepare the guest-room for the Nanny,"

Dan Jim Mr. Staline yayi yana mamakin yaushe Jasmine ta haihu bai sani ba, ba tare da yayi tambayar da yake so yayi akan Jaririyar ba yace "Sure," sannan ya wuce ya nufi inda Rahma take tsaye da Jaririyar a hannunta.

Jasmine wucewa tayi ciki ta nufi Living room dinsu ta tsaya har Matthew ya karaso inda take sannan ta daga kai ta kalleshi, ranta a bace tace "What the hell was that stunts for? Matthew do you know the implications of what you did? God!!" Idanunta ta rufe tana girgiza kai.

"I did what I did for love, to have you back," ya bata amsa muryarsa babu nadama ko kaɗan a ciki.

A hankali Jasmine ta bude idanunta ta watsa masa wata harara "By jeopardizing my sanity and reputation? You know, I strongly dislike being the center of attention especially when it comes to social media and your Royal stuff, that was the whole point of keeping our relationship off the media,"

Shiru Matthews ya danyi yana kallonta, "I apologize, it's not my intent to offend you. I wanted to do it in a more secluded manner, that was the whole point of going to Nigeria to meet you but then things happen and here we are," Shiru ya danyi sannan ya cigaba da cewa"And if we're to get married the media will know about you sooner or later,"

Gabaki daya jikin Jasmine sanyi yayi da jin kalamansa a sanyaye ta matso kusa da shi ta riko hannunsa tace "I am so sorry I yelled." Numfasawa tayi tana kallonsa tace "I need to be alone, go home Matt. We can continue this later, Okay,"

Murmushi Matthew yayi yace "It's okay, I understand," sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta sannan ya juya ya fita.

Binsa da kallo Jasmine tayi har ya fita daga dakin tana jin tausayinsa a cikin ranta. Ta shafe wasu yan mintinan a tsaye a wajen tana tunanin yadda Alamin zai dauki lamarin idan yaga labarin baikon ta da Prince Matthews. A hankali ta fara takawa tayi hanyar dakinta, tana shiga ta tarar da Rahma zaune akan kujera da Ayeesh a hannunta. Telephone din dakin ta dauka ta kira Butler su, ko minti biyu ba'a yi ba ya zo dakinta, karbar Baby Ayeesh tayi daga hannun Rahm sannan tasa Butler ya raka Rahma dakin da zata zauna.

Gabaki daya ji tayi gidan baya mata daɗi ba kamar da ba, da ba ta damu da rayuwa ita kaɗai ba, wayarta ta dauko ta fara kiran Yar uwarta Marianna.

Cikin jin daɗi Anna ta amsa wayar "Hi,"

Murmushin jin dadi Jasmine tayi da jin muryar yar uwarta, a hankali tace "I can't think straight, I think I am depressed,"

Yar karamar dariya Marianna tayi tace "Where are you Jas? London?"
"Back home Cambridge, sitting in my room," Jasmine ta bata amsa sannan ta dan karya muryarta, a marairaice tace "Can you please come over I don't want to be alone,"

Sautin murmushin Anna ne ya cika wayar kafin tace "Fine, lemme text Col,"

Murmushin mai sauti Jasmine tayi tace "Okay, I will be waiting," sannan ta kashe wayarta.

*********
London, England

Cikin sauri Jamal ya kwace basketball daga hannun Alamin sai dai bai jefa ta cikin ragar da ke gabansa ba, tsayawa yayi yana kallon abokinsa wanda shima kallonsa yake yana mamakin dalilin tsayawar abokin nasa. "Why did you stop?" Alamin ya tambayi Jamal tare da cire rigar jikinsa da ta jike da gumi.

Shiru Jamal ya danyi kafin ya ce "Saboda ka ki ka faɗa min gaskiya,"
Murmushin kawai Alamin yayi ya ta ho da guda ya kwace basketball din da ke hannun Jamal, daga inda yake ya jefa ta har cikin raga. Jamal ne ya dauko ball din suka cigaba da wasan. Sannan Alamin yace "Na faɗa maka babu abunda yake damu na,"

Kwace ball din daga hannun Alamin Jamal yayi shima ya gefa ta cikin raga sannan yace "I had known you since we were three, tare muka yi HighSchool, sannan ka tafi Aviation daga baya muka yi MBA tare. Alamin I can write a fucking book about you, stop pretending and tell me the truth,"

Ball din da ke hannunsa Alamin ya jefar da karfi ta daki kasa tayi sama sosai ta diro sannan Jamal ya kamo ta. A hankali Alamin yace "I know you're my best friend and you care about me. Amma ta yaya zan fara faɗa maka munyi fada da kanwarka,"

Bata rai Jamal ya danyi, sannan ya jefowa Alamin ball din hannusa Alamin ya chafe suka cigaba da wasan kafin yace "Me ya haɗa ku?"

"Matthews," Alamin ya bashi amsa yana kokarin kaucewa kar Jamal ya kwace ball din daga hannunsa.

Yar karamar dariya Jamal yayi yace "What did he do?"

Tsayawa Alamin yayi yana kallon abokinsa yace "He came to Nigeria and proposed to her,"

Duk wani wasa da dariya bacewa yayi daga kan fuskar Jamal, cikin kakkausar murya yace "And she accepted?"

Girgiza kai Alamin yayi yace "No, I walked in before she could," nunfasawa Alamin yayi sannan ya kara da "Do you think she still love him?"

Shiru Jamal ya danyi ya fara tafiya, adaidai wani bench suka zauna sannan Jamal yace "Duk wayannan Ex boyfriends dinta are just a distraction, and whenever she loves someone it's hard to not notice."

"Like Kyle Rodriguez," Alamin ya faɗa kansa a sama yana kallon taurarin da da ke ta kyali a sararin samaniya.

Murmushin Jamal yayi yace "Yes like Kyle, that footballer she dated because she wanted to learn Italian which is completely ridiculous," Shiru Jamal ya danyi sannan ya cigaba da cewa "But she was just lonely I guess. We grew up together Alamin kasani a America muka yi karatu, and Papa baya yin kwana biyu a gida kullum yana cikin business trip, idan an bada hutun makaranta I hardly go home gidan mahaifiyata na ke zuwa hutu ni kaɗai saboda bata son Jasmine. She practically grew up alone daga ita sai Nannies sai Maids,"

Gabaki daya jikin Alamin sanyi yayi da jin yadda matarsa ta taso, kasa cewa komai yayi har Jamal ya cigaba da cewa "I wasn't always there for her ko da muka girma ban cika zama a gida ba kullum nima Ina cikin tafiye tafiye, something I deeply regret. That's how Matthews came in, at first abokinta ne amma daga baya shakuwarsu tayi matuka har suka fara soyayya. He was always there for her and I am pretty sure he was her first love. Rabasu ko kuma cire mata sonsa daga zuciyarta ba abu bane na lokaci guda ba ko wasu yan watanni, mussamman ba faɗa suka yi ba babu abunda ya shiga tsakaninsu, rushe abotar fiye da shekara goma ba abu ne mai sauki bah."

Dafa kafadar abokinsa Jamal yayi yace "Amma tunda kaga har ta zauna da kai na tsawon wannan lokacin she have feelings for you, I know my sister idan bata sonka baza ta zauna da kai ba. Just give her some time to end things with Matthew and keep an open mind idan ba haka ba za ku cigaba da fada because she can stubborn at times,"

Murmushi Alamin yayi yana jin dadin kwarin gwiwar da abokinsa ya kara masa, a hankali yace "Thank you Bro,"

Continue Reading

You'll Also Like

352K 27.6K 29
Mini Story Uni Life Style Sweet Romance
219K 13.6K 44
Yanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resem...
2.1K 321 16
Ba Ni Da Laifi! Kaddara tana zuwa maka a yadda baka tunani, Kuma a matsayin mutum na musulmi Dole ne ya karba wannan kaddarar. Ko kunsan meye tawa...
455K 48.7K 41
It's all about destiny...