Jasmine Baturiyya ce

By Amiratuoo

117K 8.8K 1.4K

Completed (Currently Editing and Re-uploading) JASMINE haifafiyar kasar ingila (England) ce. Ya'a ga hamshaki... More

🌷JASMINE🌷
🌷Shafi na 1🌷
🌷Shafi na 2🌷
🌷Shafi na 3🌷
🌷Shafi na 4🌷
🌷Shafi na 5🌷
🌷Shafi na 6🌷
🌷Shafi na 7🌷
🌷Shafi na 8🌷
🌷Shafi na 9🌷
🌷Shafi na 10🌷
🌷Shafi na 11🌷
🌷Shafi na 12🌷
🌷Shafi na 13🌷
🌷Shafi na 14🌷
🌷Shafi na 15🌷
🌷Shafi na 16🌷
🌷Shafi na 17🌷
🌷Shafi na 18🌷
🌷Shafi na 19🌷
🌷Shafi na 20🌷
🌷Shafi na 21🌷
🌷Shafi na 22🌷
🌷Shafi na 23🌷
🌷Shafi na 24🌷
🌷Shafi na 25🌷
🌷Shafi na 26🌷
🌷Shafi na 27🌷
🌷Shafi na 28🌷
🌷Shafi na 29🌷
🌷Shafi na 30🌷
🌷Shafi na 31 🌷
🌷Shafi na 32 🌷
🌷Shafi na 33🌷
🌷Shafi na 34 🌷
🌷Shafi na 35🌷
🌷Shafi na 36🌷
🌷Shafi na 37🌷
🌷Shafi na 38🌷
🌷Shafi na 40🌷
🌷Shafi na 41🌷
🌷Shafi na 42🌷
🌷Shafi na 43🌷
🌷Shafi na 44🌷
🌷Shafi na 45🌷
🌷Shafi na 46🌷
🌷Shafi na 47🌷
🌷Shafi na 48🌷
🌷Shafi na 49🌷
🌷Shafi na 50🌷
🌷Shafi na 51🌷
🌷Shafi na 52🌷
🌷Shafi na 53 🌷

🌷Shafi na 39🌷

1K 109 30
By Amiratuoo

     A falon sama su Alamin suka zauna suna jiran Antinsa da suka zo wajenta, ruwa, lemuka da snacks  aka kawo masu kafin ta fito. Wata kyakyawar budurwa ce ta zo ta gaishe da su ta zauna suka fara hira, Jasmine kuma na yiwa yan biyu wasa. Ruwa Jasmine ta deba acikin glass cup ta kurba tana murmushi saboda abinda budurwar ta faɗa.

"Wato dai sai yau ka ga damar kawo min Amaryar taka na gani ko, ina yar tawa take," Muryar da Jasmine ta ji ce tasa ta juyar da kanta inda sauti ke tahowa.

"Lalala yau ɗana na ya tuna da  Mummy sa,"

Dariya Alamin yayi yace "Haba Mummy, Wallahi aiki ne kemin yawa shiyasa bana zuwa, kuma ai ba kya kasar,"

"Hakane, amma ai kwaki ka je kasar da ne amma ba nemeni ba, wata nawa yanzu amma sai yau ka ga damar kawo min Amaryar taka na gani ko, ina yar tawa take," Muryar da Jasmine ta ji ce tasa ta juyar da kanta inda sauti ke tahowa.

Murmushi Alamin yayi yace "Toh ayi min affuwa Mummy,"

Dariya Anty Kaulat tayi tace "Hakane, amma ka wanke kanka tunda ka kawo min diyata,"

Juyawa Jasmine tayi domin ta gaishe da Anty kaulat amma sai ta kame chak  tamkar wacce aka sakawa pause saboda Anty Kaulat  da ta gani a gabanta, a hankali ta mike tsaye tana kallonta itama matar tana kallonta, glass cup din da ke hannunta ne ya zame ya faɗi tas a kasa saboda dauke wuta da kwakwalwar ta tayi a lokacin. Mamanta Mahaifiyarta ce a gabanta, wasu zafafan hawaye ne ke zuba a idanunta lokacin da ta tunkari matar tana tafiya a hankali tamkar wacce aka zarewa laka. Rufe idanunta tayi ta sake bude su domin ta tabbatar ba mafarki take yi ba.

Mikewa Alamin yayi, yayiwa kanwar Jasmine alama itama ta tashi suka sauka kasa tare da yan biyu suka bar Jasmine da mahaifiyarta a tsaye suna kallon juna. Wasu zafafan hawaye ne ke zuba a idanun Jasmine har ta karasa gaban mahaifiyarta bata iya cewa komai ba sai hawayen. Anty Kaulat daga hannu tayi ta taɓa fuskar Jasmine a hankali tace "Bethlehem,"
Girgiza kai kawai Jasmine take yi da kyar ta iya cewa "Mami,"

Hawaye ne suka fara zubowa a idanun Anty Kaulat lokacin da Jasmine ta daga hannu ta taɓa fuskarta dan ta tabbatar da gaske mahaifiyarta take gani, a hankali ta kara cewa "Mami,"

Da sauri Anty Kaulat ta janyo Jasmine ta rungumeta tana kuka itama Jasmine na kuka. Sun fi minti uku a haka kafin Jasmine ta zare jikinta a hankali tana kallon mahaifiyarta. Wani dogo saurayi da bai wuce shekaru goma sha takwas bane ya shigo falon, tsayawa yayi yana kallon su Jasmine kafin yace "Mummy lafiya? wace wannan?"

Shiru Anty Kaulat tayi sannan tace "Kai baka iya gaisuwa ba, to matar Yayanku Alamin ce, jeka ka bamu wuri," da sauri Jasmine ta daga kai ta kalleta idanun cike da mamakin kin fadar gaskiyar da Mahaifiyarta tayi, a hankali Jasmine ta zame daga jikin mahaifiyarta tana kuka ta tsaya tana kallonta, lafiyarta kalau sannan da alamu babu wata matsala da ke damunta, to meyasa bata nemeta ba? Tambayar da ta yiwa kanta kenan. A hankali ta tace "Why?"

Shiru Anty Kaulat tayi kafin ta mayarwa Jasmine da tambaya "Which one?" Ta faɗa a hankali itama hawayen yana kwaranyo daga idanunta.

"Everything," Jasmine ta bata amsa murya a sanyaye "Why did you abandon me and Papi? Meyasa baki taɓa nemana ba? Ko a waya? Ko ba kya sona ne? Meyasa kika bar ni Mami?"

Lumshe idanunta Anty Kaulat tayi sannan ta bude su a hankali tare da share hawayen da ke kan fuskarta, "Bethlehem," a hankali ta furta sunan Jasmine sannan ta tace "I made a mistake and covered it with another mistake, I cannot undo what I did,"
Ita kanta Jasmine bata san tana matsawa baya ba dan ji tayi gabaki daya kamar ba ita ke sarrafa jikinta bah. Abunda Jasmine tafi tsoro shine ya faru wato mahaifiyarta ta san inda take amma bata nemeta ba, wato bata son ganinta kenan ko kuma bata damu da ita ba kwatakwata. Ƙasa tayi da kwayar idanunta tace "Am I the mistake?" 

Shiru Anty Kaulat tayi bata ba ta amsa ba hakan yasa Jasmine ta sake maimaita tambayarta da dan karfi. Dago idanunta Anty Kaulat tayi ta kalli Jasmine tace "Just be because I didn't raise doesn't mean zaki iya daga min murya, I am still your mother,"

Girgiza kanta Jasmine ta fara yi tana dariyar takaici tace "Really? All this while I thought you don't know where I was or worst you're dead ashe gani na ne kawai ba kya son yi," Anty Kaulat ta bude bakinta zata yi magana Jasmine ta rigata da cewa "Ba sai kince komai ba Mami, na san ba kya sona, I am a mistake right, daman bai kamata na zo ba, I will leave right away." Da sauri Jasmine ta juya ta yi hanyar sauka kasa tana ji mahaifiyarta tana kiranta taki juyawa.


Alamin yana zaune a falon kasa tare da kannenta, ya ga ta sauko da gudu ta fita daga falon. Mikewa yayi da sauri ya bita da yaga bata tsaya ba ta yi hanyar fita daga gidan, da gudu ya bita ya riko hannuta, kokarin kwacewa tayi amma yaki cikata, a hankali ya juyo da ita yaga tana kuka janyota jikinsa yayi ya rugumeta bai ce mata komai ta ringa kuka a jikinsa har kukan nata ya dan tsagaita, sannan yaja hannunta ya kaita har idan motarsu take ya bude mata kofa ta shiga sannan shima ya shiga. 

Alamin yana yin parking a cikin gida Jasmine ta bude kofar motar ta fita tun kafin ya kashe motar, da sauri ta nufi bangarensu ta shige dakinta ta rufe da mukulli, a jikin kofar dakin ta sulale a kasa tana kuka kamar ranta zai fita.

Tunda tasan mahaifiyarta na raye bata da burin da ya wuce ta ganta a zahiri sai dai bata taba yin tunanin dalilin da yasa ta tafi ta barta ba ko dalilin da yasa bata taɓa nemanta ba. Bata taba kokwanton soyayyar da ke tsakanin Uwa da Ɗa ba sai yau, dan ta gani da idonta mahaifiyarta bata sonta.

Alamin yana shigowa ya zo bakin kofar dakin Jasmine yana bugawa yafi minti goma ya magana a bakin kofar nan taki bude masa haka ya hakura ya koma dakinsa ya zauna dan kasa fita ko ina yayi. Laptop dinsa ya dauko ya bude ya fara dube mails din da aka turo masa. Shi kansa yasan yana sake da aikinsa yanzu ba kamar da ba, gashi ya tarawa kansa bashin aiki mai yawa dan yafi kwana biyu bai je office dinsa ba. Yana duba emails dinne yaga ashe yana da Appointment gobe a Abuja ga tafiyar da zai yi Japan duk a goben, gaba daya sati nan ma bai kamata yayi shi a Nigeria ba dan ranar Wednesday shi da Jamal zasu hadu a dubai akan wani sabon kasuwanci da zasu bude a a chan UAE din. Dafa kasan yayi ya lumshe idanunsa, ga kuma matsalar Jasmine, abubuwa na kokarin dagule masa. Da sauri yake typing a cikin laptop din ya turawa PA dinsa email akan ta daga masa appointments dinsa na abuja sai bayan ya dawo daga Dubai. Emails dinsa ya cigaba da replying amma hankalinsa yana kan Jasmine, tunanin tafiya yake da ita business trip din nasa idan ta yarda, dan yasan bazai iya tafiya ya barta a cikin wannan hali ba. Gashi daman zai je Germany wajen Mahaifinsa sai su tafi tare tunda daman yayiwa mahaifin na sa alkawarin zai kai masa ita. Rufe laptop dinsa yayi bayan ya turawa PA sa wani email din akan ta yi masa replying din sauran Emails din da basu da mahimmaci sosai ta bar masa masu mahimmaci.

Yana duba lokaci yaga har 8:30pm na dare yayi, mikewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya shiyar cikin kananan kaya jeans da simple shirt ya fito yana ta tashin kamshi. Dakin Jasmine yaje yana bugawa taki budewa haka yasa ya koma dakinsa ya dauko extra key din dakinta ya bude, a kan gado ya ganta zaune ta cusa kanta a tsakanin cinyarta da alama bata daina kukan ba, a hankali ya karasa inda take ya zauna a kusa da ita "Jasmine," ya kira sunanta a hankali. Kin dagowa tayi har sai da ya dora hannunsa a kanta yace "Kin san dai kuka baya magani ko, but a problem shared is problem solved," a hankali ta dago kanta ta kalleshi tace "Alamin bata so na she doesn't want me,"


Hannusa yasa ya goge mata hawayen da ke kwararowa akan fuskarta ya janyota ta kwantar da kanta akan kafadarsa sannan yace "Shh sweetheart, babu uwar da bata son ɗan ta duk lalacewarsa bare ke Jasmine, babu wanda bazai yi alfahari ba idan har ya sameki a matsayin Ya'a,"

Wasu hawayen ne suka sake zubowa fuskar Jasmine tace "Yet she called me a mistake," dagowa Jasmine tayi daga kan kafadarsa ta kalleshi tace "Does that means I am a bastard?" Da sauri Alamin ya dora hannunsa akan lebenta yace "Shh, stop saying that Love, you're not and even if you are that doesn't make you any less of who you're, and neither will my love for you lessen or your mother's love for you," shiru Alamin ya danyi sannan ya cigaba da cewa "Tana sonki Jasmine, she was suprised just like you idan kika bata lokacin a hankali zaki fahimci komai."

Lumshe idanunta Jasmine tayi ta budesu akan fuskar Alamin a hankali tace "Thank you," komawa tayi zata kwanta Alamin ya janyota "Ina baza ki kwanta ki cigaba da wannan kukan ba?"

Shiru Jasmine tayi bata ce masa komai ba sannan bata ma yi kokarin kwace hannuta daga cikin nasa ba kamar yadda ta saba ko mosti bata yi ba kawai idanu ta zubawa masa. Girgiza kansa Alamin yayi yace "Inaah, I cannot let you wallow in this self pity party Sweetheart, ki tashi ki shirya zamu fita,"

Zame hannuta Jasmine tayi ta jingina a jikin gadonta sannan tace "Ni babu inda zani, kawai ka kyale ni."

"I have already done that, na baki yafi 2hours kinyi kukan yanzu ki tashi ki shirya ko ni na shirya ki da kaine," Matsowa Alamin yayi kusa da ita kamar zai daga ta, da sauri Jasmine ta kauce tana harararsa, tsakiyar gadon ta koma tace "Ni babu idan zani ka kyale ni,"

Murmushi Alamin yayi ya mike kamar zai fita, sakin jikinta Jasmine tayi ta zauna dan a zatonta Alamin fita zai yi, bata yi aune ba sai ji tayi ya kamota, kokarin kwacewa ta fara tana fusge fusge amma yaki cikata "Alamin dan Allah ka kyale," Jasmine ta faɗa a marairaice. Shiru yayi mata ya daga ta chak sai bathroom din dakinta. Ajiyeta yayi ya kunna ruwa a bath sannan ya juya yace "Na taya ki cire kayan ne ko zaki yi da kanki,"

Harararsa tayi tace "Naji zan yi da kaina," fitowa daga bandakin Alamin yayi ya shiga cikin closet dinta ya dauko mata kayan da zata saka. Leko kanta Jasmine ta farayi bayan ta gama wankan tace "Can you get out Please, zan fito."

Yar karamar dariya Alamin yayi yace "You're quite funny love, Wai meye difference din towel din da ke jikinki da wayannan short skirts din da kike sakawa,"

Tabe baki Jasmine tayi tace "The difference is you here, ni dai ka fita,"
Girgiza kansa kawai Alamin yayi ya tashi ya fita. Kayan da ya dauko mata ta kalla ta tabe baki sannan ta shige cikin closet dinta ta dauko wanda take son ta saka. Silky white button up shirt da coffee color wando ta dauko sai wani dan karamin mayafi da zata yafa. Takalmi kuwa yau bata dauko heels din da ta saba sakawa ba, farin canvas na kamfanin Nike ta dauko.
Turare kawai ta fashe jikinta sannan ta fito. Alamin na zaune akan kujera a falo ta fito har inda yake ta tako tace "Na shirya, Wai ina zamu?"

Dagowa Alamin yayi ya kalleta yace "A haka zamu?"

Kayan jikinta ta kalla tace "Rigar nan ta kusa kaiwa gwiwata fa and na rufe gashina, ni bazan chanja kaya ba sai dai na fasa zuwa,"

Murmushi kawai Alamin yayi yace "It's fine, muje a hakan." Dan ya fuskanci rigima take ji.

Kasa suka sauka suka fita waje, wata bakar G-Wagon ce ta tsaya gabansu Alamin ya budewa Jasmine gidan baya ta shiga sannan shima ya shigo ya zauna a kusa da ita. Juyawa Jasmine tayi ta kalleshi dan duk sanda zasu fita da kansa yake tuka su. Murmushi kawai Alamin yayi mata bai ce komai ba har suka isa idan zasu. Alamin ne ya fara fita sannan Jasmine ta biyo banyansa tana karewa wajen kallo. Cikin Gusto Restaurant suka shiga suka zauna aka kawo masu menu suka zabi irin abincin da suke so, sannan suka zauna jira. Dagowa Jasmine tayi ta ga Alamin yana kallonta, "What?" Ta tambayeshi fuskarta babu fara'a.
Dariya Alamin yayi ganin har yanzu bata sauko ba, "You look Beautiful without makeup," ya bata amsa. 

Juya kwayar idanunta Jasmine tayi tace "That line is not gonna work on me M,"

Alamin ya bude bakinsa zai bata amsa yaji an kira sunansa, yana Juyawa yaga Abokinsa Abdul tare da Matarsa Hajara, cikin fara'a suka gaisa sannan suka zauna a table din su Jasmine suma suka bada tasu order. Hira suka fara yi, tun Jasmine bata cewa komai sai yake har ta saki jikin da su itama aka ringa hirar da ita. Bayan sun gama cin abinci kuwa har musayar number Jasmine da Hajara sukayi, Hajara tayi alkawarin zata kawowa Jasmine ziyara sannan zasu dinga chatting ta social media. Tare suka fito daga cikin Gusto Restaurant, su Abdul suka shiga motar su suka tafi. Juyawa Jasmine tayi zata nufi idan motarsu take Alamin ya riketa yace "Muje da kafa zamu koma tunda kinga ai babu nisa zuwa gida,"

Hannunsu a makale da juna suke tafiya cikin daren, wata daddadar iska na kadawa gashin babu abun hawa sosai akan titin, garin ya danyi shiru sai karar mota idan tazo shigewa, driversu na biye dasu cikin mota a baya yana tafiya a hankali. "Advice," Alamin ya faɗa yana kallon Jasmine.

"Ina jinka," ta bashi amsa ba tare da ta kalleshi bah.

Shiru Alamin yayi tamakar mai kokwanto akan abunda zai fada kafin yace "Venting out your anger on others bashi ne mafita ba Jasmine, ki koma ku sake magana zata yi miki bayanin komai,"

Girgiza kanta Jasmine tayi tace "Bata sona Alamin, bata so na zo ba kuma da tana son yi min wani bayanin ai da ta yi min tun dazun,"

"Ke fa kika gudu, baki tsaya tayi miki bayani ba Sweetheart,"

"Wai meyasa kake so na kara komawa wajenta?" Jasmine ta faɗa a dan fusace.

Tsayawa Alamin yayi ya daina tafiya yace "Saboda Mahaifiyar ki ce ita, sannan ta kira ni dazu."

Da sauri Jasmine ta juya ta kalleshi tace "Ta kira ka?"

Gyda mata kai yayi alamar eh ba tare da yace komai ba. Shiru Jasmine ta danyi Kafin tace "Fine, zan sake zuwa amma ba yanzu,"

Murmushi mai sauti Alamin yayi yasa hannusa ya janyo Jasmine jikin yace "Ma'asha Allah, ko ke fa,"

Dariya kawai Jasmine tayi tace "Thank you M, you're the best husband and friend a girl can ask for and I actually feel better now gwanda da ban zauna a gida ba,"

Murmushi kawai Alamin yayi kafin Jasmine ta kara cewa "Abokinka Abdul shi da matarsa suna da kirki, I like her,"

"Yeah, Abdul yana da kirki sosai, da zaki iya tunawa ya zo bikinmu tare da shi aka yi komai zaki ganshi a wedding pictures din mu,"

"Oh, you're guys are really close,"
"Yeah, tare muka yi aviation da shi, idan kin tuna na faɗa miki nayi makarantar koyan jirgi Aviation,"

Haka suka yita hira suna tafiya acikin daren har suka je tarauni da kafa suka shiga Flakes suka siyo Ice Cream, daga nan kuma mota suka shiga driver ya maida su gida Nassarawa GRA.

Assalam alaikum

Dafatan dai kunji dadin wannan shafin, Yau dai Na cika Alkawarin update bayan one week 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Finally Jasmine ta hadu da Mahaifiyarta!!!😃

Waye yayi tunanin haka me zai faru tsakanin Jasmine da Mahaifiyarta 🤔🤔🤔 ???

Shin menene dalilin da yasa Mahaifiyar Jasmine bata taba nemanta ba ???? Any guesses????? 😉

Ya kuka ga Alamin a wannan shafin????

Supportive Husband 🥰🥰

Ku rubuto min ra'ayoyinku kar ku manta da Vote ⭐️

Don't forget to follow me and bombard me with questions or comments, I don't bite and I love your comments sune energizers dina.

Instagram: @amiratuoo
Twitter: @amiratuoo
TikTok: @amiratuoo
Facebook: Amina Umzak
Inkitt: @amiratuoo

Continue Reading

You'll Also Like

219K 13.6K 44
Yanka mata wani wawan mari tayi though ba yau suka saba gwabzawa ba, cikin masifa ta nuna mata ɗan yatsa "karki kuskura ki kara faɗin haka, any resem...
110K 16.7K 30
ရိုးရိုးအချစ်ဇာတ်လမ်းလေးတစ်ပုဒ်ပါပဲ
274K 20.2K 28
Love between a muslimah and christian✍
836K 8.9K 100
ထိုနေ့ည က မှားသွားတယ့် အမှားတစ်ခုက ကျွန်မဘဝ တစ်ခုလုံးနဲ့ ပတ်သက်မိသွားလိမ့်မယ်လို့ မထင်ခဲ့မိဘူး....... ပြီးတော့ ပတ်သတ်မိသွားတယ့်သူက ဘာလို့ သူဖြစ်န...