(14)

39 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Thursday, 28th August. 2020

(14)

***************

Kawai se ta fara kwalla,cikin taushin murya ta fara magana cike da rauni,tace ...."Dan Allah Hammah ka maida ni gida,nidai na gaji da Nan din.."

Dago wa yayi ya kalle ta ,har lokacin Yana jiyo hayaniya a tsakar gidan ,se ya share yace .."Mairo bakya Sona ne har haka,kika yarda da abunda ta fada?"

Girgiza kai tayi tana cewa ..."Ah ah,ni Daman bintalon ce dasu Uwani sun dameni, bintalon fa har bina bayi take tana dunguri na tana zagi na,Kuma tace wai se ta aure ka ko Zan mutu.."

Fashe mai da kuka tayi,shi Kuma mamaki ne ya kama shi,wai kenan ma shine ake wa laifi,Amman ake maida shi me laifi,tashi yayi chak ya kama hannun ta..
A kofa suka gamu da isuhu Dan wan Kamalu na uku.nan ya shaida musu cewar Mallam sa'idu ne yake Kira..

Hannun ta cikin nashi ya raso tsakar gidan,a kasan bishiyar Maina ya tadda su.kowa ya tsugunna ,ga bintalo da har lokacin take ta sharara kuka ,Maina beyi mamaki ba Dan ya gane cewa makira ce ta karshe ..

A gefe suka tsugunna,Duk Wanda ya kalli fuskar Maina yasan ba wasa ,ya hade fuskar Nan tasa tsaf ba maganar rahama ko annuri..

Ita dai Mairo tana ta share hawaye,Dan zuciyar ta fal da tsoro,gashi Bintalo tace kar ta fada wa kowa abunda take mata Kuma ta fada.ita fatan ta daya ma Allah yasa kar Hammah Maina ya fadi bintalon taji.dan ita ta fada ne Dan ya maida ta gidan su...

Kaka sa'idu ne yayi gyaran murya ya fara magana cikin muryar tsofaffi yace .."da guda me yake faruwa ne haka?"

Maina da aka Kira da da guda Yana kallon gefe yace .."Baffa ni ban sani ba gaskiya,nadai San na shiga kewaye na iske wata Diya ciki.."

Kan ya dire se ga salatin su Uwani hadda tafa hannu irin Maina ya shararo karya dinnan..

Ba Wanda yabi ta kansu ..Mallam sa'idu ne yace.."Toh wacce magana nake ji daga bakin bintalo?"

Ran Maina Yana dada baci ta yadda ya kusa kasa iya tankwara zuciyar shi,haka ya daure yace .."Baffa ka tambaye su ,Nima naji lefi na.."

Kallon sa Baffa yayi,sannan ya kalli Bintalo,baya son yayi saurin yanke hukunci,Amman shima a ransa yasan Maina baze yi abunda suke nufi ba ..sedai shedar Dan yau Yana da wahala ,shiyasa gwamma yabi komai a hankali a samo bakin zaren..

Cikin hikima yace.."yaki nan bintalo,zo Nan kusa daina kukan haka,zoki gaya mun abunda ya faru.."

Taso wa tayi munafuka ta iso gefen Baffa ta tsugunna.maimaita mata tambayar yayi,Nan ta karkace ta hau zayyano jawabin karya ..fadi take .."Baffa ni ban San me isa ba kullun naje gewaye se ya biyoni bayi,ya ruga mun mugun wasa ba.."

Wani iri Maina yaji a ransa kamar an soke shi da mashi a zuciya..be Ankara ba yaji tana sake cewa .."Baffa nema na yake yi .."

Ai Maina beyi shawara da zuciyar shi ba ya tashi ya isa gaban bintalo ya make mata baki,take bakin yayi jini..a hankali Kuma ya koma ya tsugunna a inda ya taso,bayan yace wa bintalo .."cigaba da bayanin.."

Yo Ina bayani ze samu a naushe baki har ya hau lokaci guda?

Kuka ta fashe dashi tana auna yadda suka tsara abunsu a dai dai ita dasu Uwani,Amman tun ba'ai nisa ba har an samu matsala..

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now