(22)

25 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Friday,25th September. 2020

(22)

***************

Toh gadai su Maina a garin Kano,ko ya rayuwar zata tafi musu?

Se mun juyo sannan zamu gani..

__________________

Kauyen Burum.

Kewa ta cika Inna da Baffa,se Inna Mari da Ubale..suna nan Abubuwa sun ishe su,Sakamakon rasuwar da kakanin su sukayi,gidan ya Soma watsewa,kullun ana kan bala'i a wannan gida,kullun cikin tashin hankali ake ..

Da yake dai shi Ubale ba ruwan shi da kowa,Haka ma Sale ,kusan masifar ma faccalolin be suke yi,ya zamana yanzu jowa na kyashin yiwa wani abinci,kafin wani lokaci se suka tsiri iskanci a gun ma dahuwar,daga nan se aka daina hadaka,tunda Inna Mari taga haka,se ta fara abinci ita da Inna Salmai,suci su bai Ubale..

Kwata kwata ma suka fita daga shirgin gidan,in Ubale ya fita ,yaje bakin kasuwa,in ya dawo ya shige rumfar sa..

A hankali ya samu ke katange gun shi shima,ganin Haka yasa sauran mazan gidan kowa ya tsiri shaftar fili suna katange wa,ko kuwa a shata layi,Duk Wanda kuwa ya haura gun anyi ta tafka bala'i kenan..

Ubale ya Yi iya kokarin da na ganin cewa ya tsaida wannan badakalar,a samu ma a raba dai dai kowa kada yabi son ran sa.

Amman dake suna ganin sun girma,gasu da diyoyin su,se suka ki ji,suka ce su Basu San wannan zancen ba..

Toh shi kan shi Sale uban su sun raina shi,hakan yasa Ubalen ma yanzu basa ganin shi da kima,yanzu zasu gaya maka maganar banza wadda har zata Bata maka Rai..

Kawai se Ubale ya fidda kofar shi ma ta waje,ya zama katangar gidan sa ce a tsakar gidan wannan,Amman kofar shi tana ta wani bangare,hakan yasa ba Wanda yake ganin shigen shi da ficen shi,tunda ya fidda kan shi daga sabgar su,se ya samu lafiya..

________________

Kano

A ran da suka sauka ,suka gyara dakin su,sukai shara ,Duk da take ma dakin ba wani datti garai ba,Dan befi sati biyu ba aka fita daga dakin.dan Haka suka sauke kullin kayan su a Yar kwana sannan sakala Dan labulen su Wanda dashi suka taho abun su.

Fita sukai su samo yan kayan bukata,Kamar taburma,buta da sauran su,fitar su keda wuya aka shiga dakin nasu aka kwashe musu yan kayayyakin su, aka bar su da zallar kayan su na saka wa.wanda suma kala hudu hudu suka zo dashi.Allah yaso ma kudin su na kuturin su,da tuni suma sun Sha mamaki ,kano kenan

****

Tafi tafi se da suka siyo taburma,da butar su Dan bokiti da robar wanka,sannan suka siyo biredi da Dan kosai suka yo gida.

Suna shigowa dakin suka ga alamun an bincike su,Dan yan kunne,warwaron Mairo na karfe,Yar fitilar su day suka siya a danbatta,hatta abunda be Kai a dauka ba seda aka dauka..

A dai dai bakin kullin nasu yaci sa'a ya ga wannan sarkar ta Mairo tuni ya dauke ta sannan suka maida kayan su suka daure suna ta mamakin wannan abu..lallai Kano ta daban ce,dan duk sauran garuruwan da suka sauka ba inda aka daukar musu ko da tsinke ne,se gashi ko awa biyu Basu cika ba daga saukar su har an yashe su,wannan ne ya koyar dasu hankali ,suka gane cewa se sun daura dammara..

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now