WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Tuesday, 16th june. 2020

(8)

***************

Tsaya wa sukai suna kallon kasa,ita kuwa Hasi  da ta ga shirun ba me karewa bane se tace ..

"Ni kuwa bari na shiga gidan su Sabuwa ..."

Tana gama fadar haka ta fara tafiya ,kan kace me har ta fada soron gidan su Sabuwa tunda makota suke. .

Su kuwa mutanen naku da ido suka bi Hasi har sai da suka ga ta shige soron sannan suka dawo da kallon su daga gareta...

Shi Maina a kan Mairo ya sauke idon shi ,ita kuwa Mairo a kasa ta sauke nata idon..

Kallon ta yake, yayin da yake sake tabbatar wa kansa cewa ita ta dace dashi..

Ita kuma Haushin hasi ne duk ya cika ta ,Dan a ganin ta ya za'ai hasi ta mata haka ,cikin wannan tunanin taji yace ..

"Mairon Maina"...

Saurin tsugunnawa tayi tare da saka fuskar ta a kan gwiwowin ta ,se kuma ta hau wasan kasa ,cikin sa'a ta hango tsinke,daga tsugunnen ta muskuta ta janyo tsinken se ta fara Zane Zane a kasa..

Shi dai yana tsaye yana kallon ta,a lokaci lokaci kuma ya kan kalli masu wuce wa ,wasu suyi mai sallama wasu kuma suyi wucewar su ba tare da sun ko kula dasu ba..

Sake cewa yayi..." ta Maina bata magana ne ?"

Tsaya wa yayi yana kallon ta ,Dan Chak tayi ta daina zanen da da take yi..wannan ya nuna mai alamun tana jin me yake cewa ..maganar ce kawai baza tayi ba

Tsugunnawa yayi Dan nesa da ita,daman chan asali ma haka zancen yan karkara yake ,a tsugunne ake yin sa,kamar yadda kuma ake yin sa Saurayi ya kalli kudu,hallau budurwa ta kalli arewa ..😂

Toh Amman shi dai Maina ko da jikin sa yake kallon gabas ,fuskar shi kuwa bangaren Mairo take kallo,Dan ya zuba mata ido kallon ta kawai yake yi bako kaukauta wa ..

Jin son ta yake yi har cikin bargon sa da jinin jikin sa,shi kan shi yana mamakin yadda akai cikin lokaci kankani ya kamu da soyayyar yarinyar ...

Murmushi yayi shi kadai,yayin da duk motsin shi kuma akan iya jiyo kamshin turaren shi me karfi ga arha..

Ce mata yayi ..."Mairo,Mairon maina ko kallona baza kiyi ba ?..toh bari na tafi tunda ba'a maraba da zuwa na .."

Dan motsi tayi kadan ta kalli saitin shi,Amman idon ta a takalmin shi ya tsaya ..se kuma ta dauke idon ta,ta sunkuyar da fuskar ta tana kallon yawan zanen da tayi a gaban ta ..ita a nata tunanin dai ai ta kalle shi

Hasi ce ta dawo ta tsugunna daga gefe ita ma ..Kallon Hasinan yayi yace mata "Addar ki bata magana ne ?"

Dan kallon Mairo tayi kadan se tace.. "Yo tana magana mana,amman ba sosai take wa mutane ba.."

Ta fada tana cilla dutsen da ta dauka gefenta..

Dan kallon Mairo yayi ,wadda yanayin ta ya nuna ma kamar bata wajen,Amman a zahiri tana sauraran su..
Ok
Hasinan ya sake kallo se yace .."Hasi tashi Ku shiga gida ,ni zan koma .."

Tashi Hasin tayi tana cewa .."Adda to taso mu shiga.. "

Tashi Mairon tayi tana satar kallon sa.ce musu yayi .."se da safe,Ku shige ina kallon Ku.."

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now