WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Saturday, 6th june. 2020

(6)

___________________

Kamar yadda al'ada ta tanadar ,ana hidimar tarar sallah ana ibadah ..

Ita ma inna duduwa tana murnar zuwan Sallah,a gefe guda kuwa tana fargabar wuce war azumi.

Dan da azumi basa rasa abinci,kama daga na buda baki da sahur,sannan kuma na dumamen safe saboda su Hansai ..

To abinci ne ake ta sadaqar sa lokacin azumi,Amman Azumi na wuce wa shekenan se su koma yar gidan jiya..

Dan ma suna yin yan dabarun su na ganin an rufa wa kai asiri..

Salame kam daman ita tana zama a gurin Ladi me kosai wanda daman ko ba da azumi ba Nan take zama,tana Taya ta tuya da irgen kosan..Kuma da kudi take biyan ta ,hallau duk Randa akai ragowar kosan takan sammata ..

Hasi da Mairo ne mara tsayayyen aiki,dan su komai yazo yi suke abun su..

Wankau kuwa inna keyin shi,su sai dai su mata shanya ko su taya ta dauraya..

Ko abincin siyar wa ma Inna keyi daga zaure kuma mafi yawancin lokuta da Hasi suke yi..

Ita Mairo tafi yin komi daga cikin gida abun ta..

Toh ko da inna take wannan tunanin ma tasan cewa dai bakin da Allah ya tsaga baya hana shi abun sa wa cikin sa..

Kwanci tashi ba wuya se ga Sallah ta zo..

Yau take Sallah,inda kowa mutane manya da yaran su suka shirya suka nufi sallar Eidi..

Kowa ka gani fuskar shi cikin fara'a ana ta gaigaisa wa da jama'a

Haka akaje aka dawo daga sallah ,yaran layi kowa yaci kwalliyar sa ,chan na gano su Mairo sunyi ankon su,su hudu sunyi kyau kuwa..

Daman innar su tayi musu Jan lallen su tun dare,hallau ta sa su gaba sukai tsifa,nan ta wanke musu kai ,sannan tayi musu kitson su gwanin sha'awa

Daman gasu da yalwar gashi Masha Allah..

Yawo ne yaran suka hadu suna yi ,daga nan gidan zuwa wanchan gidan ana ta gaisuwar sallah ana ta karakaina da kwanuka,ga wani gilashi da ake yayi lokacin irin me kalolin nan

Se ganin yaran kake ana ta kwambo ana juyi,gashi anci wannan gilashin na roba Malam.

Kwalliya kuwa ba'a magana ,duk da ma kwalliyar irin ta da ce tun asali,hoda ce se kwalli da kan ta kile akr ta digo digo dashi

Haka suke ta hidimar sallar su,ana ta Rabon abinci,daga nan gidan zuwa chan,daga chan zuwa nan..

A dai dai wannan lokacin kuma Maina na chan,shi dai burin sa kawai yaga Mairo..

Ita kuwa Mairo gurin sha biyun rana ma ta dawo gida tayi kwanciyar ta,ga cikin ta da yake dan mata ciwo

Su Hasi da Talan kuwa ! Ai sun yi cikin gari ma ,ana ta yawo Malam,dan daman kusan tare suke kawanchen su gaba daya.

A gun yawon nasu suka gamu da Maina ,aiko su hudu seda ya bisu da Murtala Murtala,haba wa se murna,dan ita al'adar kauye har yau suna bada barka da sallah wa diyan su,me yar Biyar,me yar goma ,haka dai

WATA KADDARAROù les histoires vivent. Découvrez maintenant