(26)

39 3 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sunday, 27th September. 2020

(26)

***************

Washegari Maina ya tafi gun su Malam Ado.daga nan suka je unguwa uku ganin gida,nan Maina yaga gida,gidan Kuma ya kwanta mishi sosai duk da dan mitsitsi ne ,Nan aka fada masa kudin hayan,Amman na shekara ake biya ko na rabin shekara .

Nan yace yaji ya gani ze biya,amman yace bashida shi a halin yanzu .kudin hayan gidan naira dubu talatin ne a shekara.

Koda Malam Ado yaji haka se yace wa Maina ko su je yaga gidan da yake gaya Masa yanzu?

Nan Maina yace ba damuwa. suka kuwa hau babur se gidan.gidan ma Yana nan ne a hotoro ..

Suna sauka a kofar gidan cikin sa'a Sega motar me gidan nan tazo zata fita..

Yana ganin Malam Ado ya saki fara'a yana me nuna jin dadin ganin shi.a mutunce suka gaisa ,Maina ma ya gaida shi .

A nan Alhaji ya sake bawa Ado hakuri kan barin sa aiki ba tare da laifin fari ba,bare ba baki.

Malam Ado yace "Ah ai Alhaji ba komai,ba gashi ba har yanzu Ina kasuwar kwari,Kuma ba Kai ka kaini ba.ai an gode sosai madallah,dama WATA KADDARAR ita ke kawo wata ai.."

Nan Malam Ado yace .."uhm Alhaji dama nazo ne da dana gashi Maina,ko ze samu aikin Yi anan din.."

Cewa Alhaji yayi.."Eh toh,nako ji hajiya na neman sabon me wanki,wai shi me musu zeje gida ya dawo,Amman shi me musun yace ze kawo wani ya ruke Masa kan dawowar sa din.Amman abunda ban sani ba shine ya kawo din ko be kawo ba .."

Kallon Maina Alhajin yayi yaga yadda ya matsa nesa dasu tun bayan da yaji sun fara magana..

Haka Nan yaji Mainan ya kwanta Masa,se ya dauki wayar sa ya Kira matar da,yace .."Ni an samu me wankin ne ko ba'a samu ba.."

Shiru yayi Yana sauraren ta,Chan Kuma se yace .."toh ba damuwa,Ni na samu wani yaro se ya ruga mana,mu gwada muga ni ..yawwa toh .Allah yasa."

Kashe wayar yayi Yana cewa.."Toh Malam Ado.yaron ka na dauke shi ze nayin wanki ,sedai yanzu kaga a hanya nake,in ze iya gobe ya sameni misalin goma na safiya se muyi magana..

Baki har keya Malam Ado yake ta godiya,dan a dan zaman da sukai da Maina ya fahimci mutum ne me amana da mutumci.ko bayan sun tashi yasha zuwa gun shi ko a gida ko a kasuwa,Kuma be taba zuwa hannu rabbana ba,se ya Kai masa dan Abu yace akai wa Aisha ..

Nan Alhaji ya damko akalla naira dubu biyar ya baiwa Malam Ado yace su hau mota, sannan yace Maina yazo gun goma ya same shi..

Da Haka suka juyo Makam Ado ya raba kudin gida biyu ya bawa Maina rabi.shiko Maina yace wallahi baze karbi haka ba.saurin rantsuwar da yayi ce tasa Malam Ado ya cire 500 daga kudin ya baiwa Maina 2000.nan ma Maina yaki ansa .a karshe dubu guda ya karba yana godiya .Hakan da akai ya Kara wa Maina kima a idon Malam Ado.daga Haka suka rabu,kowa yayi hanyar gidan sa.

Washegari tun Tara na safe Maina ya iso kofar gidan.

A nan waje ya zauna yana ta kalle kallen sa abunsa.

Cikin Haka motar Alhaji ta danno zata shiga,ganin Maina a waje gun Tara ne yasa ya dubi agogo Dan yana tunanin ya Saba alkawari.ashe Maina dai be ya iso da wuri yake zaune .

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now