(21)

26 1 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Wednesday,9th September,2020.

(21)

***************

A cikin wannan shekara Abubuwa da dama sun faru.
wasu na dadi wasu na rashin dadi.
kamar yadda tun asali Maina ba rago bane, hakan ne yasa ya Kama wata sana'ar tunda ya dade da Saida kurar ruwan sa,Sakamakon ganin da yayi cewa in ya biye wa zaman da ya tsira na tuanani ,Dan shagon nasu ze durkushe.

Dan a cikin Abubuwa da suka faru ,harda balle shagon Mairo da akayi aka yashe Mata yan kayayyakin saidawar ta,

gashi Kuma Mainan da ya zauna ya dogara da wannan shagon ,ganin hakan ba ze yiyu ba,ya karbi Dan kudi a gun Mairon ya saro Rake,

tuni ya fara yawo Yana Saida raken shi Wanda yake bi hayi hayi Yana tallar sa,bashi da baaro,hakan ne yasa a kafada yake Saba raken yayi ta yawo dasu Yana Saida wa..

**********

Ubale nata Shirin shi a gefe,kuma so yake bikin kada ya dauki lokaci ayi shi ..

Diyar da ya samu kanwar Maina ce,Yar wajen Wan Kamalu,sedai da akai rishin sa'a yarinyar tana da saurayin ta me suna Haladu,Kuma soyayya suke sosai abunsu.

Kwatsam Ubale yake nemawa Maina ita,Nan ta dire tace Bata yadda ba ,Dan soyayyar Haladu ta rufe Mata ido.

Haka iyayen ta suka so tirsasata ,sadda ta fice kwanan su biyu suna neman ta,dan ta tafi ,Amman ta bada sallahu cewar a gaya musu indai suka mata dole zata gudu tabar gidan gaba daya.dole haka aka hakura da batun aura mata Maina..

To ita ta saukaka wa Maina ma ,dan ko zeyi aure baze auri Yar cikin gidan su ba,shi bega mata a gidan ba ma,Duk kuwa da suma fulanin ne Kuma Basu da lefinsu..

Dan haka da ta ki shi ma, ta ta taimake shi,yarinyar ma me suna Suwaiba ake ce Mata suwai,wata ballagazar yarinyace,gashi ita ba kyau ba ,bare ya damu ,Dan haka shi a dadin shi ,Dan ba karamin sauki ta sama Mai ba,sannan ta shafa Mai lafiya..

Ko da ma har yanzu Ubale be hakura ba,yace Daman Dan kar na gida be koshi bane ba a bai na waje,Amman tunda anyi Haka,a cewar Ubale ze samo mace ta kere wa sa'a ya aura wa Maina...ita kuma Suwai se ta je ta karata !

*********

Haka rayuwa take ta tafiya da dadi ba dadi,sedai a bangaren Maina da Mairo abun ba Haka bane,dan wata tsaftataciyar kauna ce ta gaske a tsakanin su,Kai da ganin su ma kasan asalin masoya ne,sosai suke barjar soyayyar su San ransu,tare suke girkin su ,suci su Kuma Kora da soyayya ,babu abunda yake wa Maina dadi a zaman su da Mairo irin yarintar ta,dan sak halayen ta na yan fari ne,Bata cika wayo ba sam,shi Kuma wannan rashin wayon nata ya basa damar juya ta yadda yake so,gata da kafirin tsoro ,gata bata da musu,Dan haka da Sanin ta dai Bata Saba wa Maina,sedai bisa kuskure,Wanda Daman shi Dan Adam ajizi ne.

ko dan ma yadda yanayin hukuncin shi yake ai dole ta kama kanta a guri guda...Dan shi a gado yake nashi hukuncin ,Maina kenan,Namiji me jini a jika..

_____________

Rana ce ta laraba,Maina be je ya saro sabon rake ba,Sakamakon dan ciwon Kai da Mairon take ta fama da shi.dan haka yaje da kan shi Yar kasuwar hayin su,wake ya auno gwamgwami guda,Naira asirin,se shinkafa gwamgwami daya Naira arba'in,se salak da tumatir da albasa ,Naira talatin,Manja Naira talatin ya nufo gida..A shagon su Mairo ya dauki sufa dif ya hada musu..

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now