(27)

44 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sunday, 27th September. 2020

(27)

***************

Duk da Maina yana da albashi me tsoka a wata,hakan be Hana shi yin sana'ar sa ba a gida.dan dai Maina ya fara sawo agwaluma tunda lokacin ta yazo,Kuma Haka yake kukuta wa yake tallar ta ,da yake ma a tire yake yawo da ita akai,se kawai ya ruga zuwa gidan Baba Alhaji da ita bisa kan shi,yaran gidan kuwa abun so ya samu,su siya,Kuma ya Basu kyauta,in ya tashi daga gidan Baba Alhaji se ya iza ta Kai yayi Dan tiri tirin shi ya samu abunda ya samu sannan ya koma gida..

Sannu a hankali suke tafiyar da rayuwar su cikin rufin asiri,kauna da tsantsar soyayya da farin ciki..

********

Rana ce ta Alhamis wadda ta Kama ranar da yan gidan Baba Alhaji sukai tafiya Izuwa kasar waje,Kuma kafatanin su suka tafi,hakan ne yasa Maina ya samu hutu har na wata guda..

A yau da suka tafi Maina beje ko Ina ba,zaune suke a Yar karamar tsakar gidan su,inda Maina yake kwance akan wata taburma ba riga a jikin shi..

Mairo kuwa tana zaune gaban shi tana ta kwaba kullin yar sulub din ta, da za ta fara toyawa daga cikin gidan ta..

Idanun shi Maina a rufe suke,hankalin shi yayi gida ne cikin yan kwanakin nan,sedai har yanzu be tara abunda zeje dashi ba gidan,dole Haka ze zauna yin tunani da zarar ya tuno su,ba tare da samun madafar tunanin nashi ba..

A yau ma hakan take,Mairo na tai Masa Hira ma ,Amman baya ko jin ta,Dan ya Lula a duniyar tunanin iyayen sa..

Seda ta taba shi sannan ya kalle ta,Kuma sannan ne hankalin shi ya dawo gareta.

Churo baki tayi tana cewa .."Hammah,shine nike ta maka magana kaki kulani ko?"

Kallon ta ya sake Yi cikin magagin kaunar ta.ya daga hannun sa ya jawo lallausan farin  kumatun ta .

Cewa yayi.."Ai Ina jinki Mairo ta,kawai na manta me kika ce ne.."

Tuni ta fado kansa tana kukan shagwaba..

Kamo ta yayi yana cewa..."toh dan sake gaya mun, me ma kika ce.."

Kallon shi tayi tana cewa .."cewa nayi Ina son ka siyo min kayan shafa,irin Wanda su humaira suke shafawa Nima Ina shafawa.."

Dariya yayi ,yace .."shi kenan kike so?"

Cike da yarinta da rashin isashen wayo na yadda yake maidata kamar wata Yar jaririya ta daga kai tana wani abu da bakin ta..

Girgiza Kai yayi Yana cewa .."An gama Mairon maina,gobe juma'a,insha Allah zanje kasuwa na siyo miki kayan shafa.."

Murna ta dinga yi,shi kuwa Maina ya shiga ciki,ita Kuma ta fara toya wainar ta..

Washegari juma'a,da wuri ya nufi kasuwa,kasuwar da yake ya samu me kayan hoda,yace a bashi komai na shafa,me kayan yace wace kala,nan Maina ya rasa yadda zeyi.se yace "toh kaban wadda tafi kala ta haske.."

Haka me hoda ya hada wa Maina hoda ,kwalli,janbaki harda jagira..

A gefen shi kuwa wani me kayan koli ne yake wa Maina tallar turaren hammata,tuni ya siya musu guda daya abun su,da yake irin body spray din nan ne ,aiko kamshin ba laifi,haka ya Kara zagaya wa sannan ya koma gida...

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now