WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sunday, 19th July. 2020

(9)

***************

Abu ce tace.. "Toh kuzo muje mu ida charafken na mu mana.."

Hasi ce tace.."Ah ah ,an kira sallah sedai kuma gobe..kin san Innar mu zane kafa take in bamu yi Sallah ba"

Katse su inna ta yi da " Kuje maza kuyi Alwala kun tsaya zaku dasa sabon tadi .."

Tuni suka nufi wani bahon ruwa dukka suna rige rigen yin Alwala ..

Kyale su inna ta yi ta tada sallar ta a nan dan tsakar gidan nasu..

Suka zo suka jona tasu daga gefen innar ..seda suka idar sannan Inna ta sasu sukayi Addu'a suka shafa.bayan nan se inna ta sa suka mika wa Baffa 
Ledar tsiren nan ..cewa yayi yara suci abunsu ,Dan ita ma innar baci zata yi ba .

Haka ta bude ledar ta bawa Hasi ,nan Hasi ta ajje musu tsakar gida suka zura hannu suna ci dukkan su suna santi..daman ita inna a al'adar ta bata raba kwanon yaran ta ,komai tare suke ci,ko kadan ne ko me yawa a tare suke cin koman su.

Watakila wannan ma ya taimaka wajen hadin kan su da shakuwar su ...

Bayan sun cinye tsiren ne su Abu suka tashi tafiya ,nan kowa ta ruga gidan su tana murnar taci tsire..

*************************

Kamalu ne a hanyar zuwa gida,ba hirar da yake se ta Hasi ,shi dai yace yau ze aiko a nema masa shi ma .Dan gaskiya ya ga yarinyar kuma yaji ta shiga ran shi..

Kallon shi Maina yayi yana fadin..."Yo kuma kayi yaya da Sauden ?"
(Saude itace budurwar kamalu)

Kallon Maina yayi yace .."Yo saude, hana ni za tayi ko mi?,ince dai zan iya auren dukkan su har ma na dado wasu biyun?"

Dariya Maina ya fara yana tafa hannu cikin yanayi na mamaki ..cewa Maina yayi ...."kai mutume na ,daga ganin sarkin fawa se miya tayi zaki?"

Dariyar shi ma Kamalu yayi yana fadin "Ah toh ,kasan ance zama waje daya tsautsayi inji kifi .."

Dariya sukai dukkan su sannan suka nufi gida,Dan su ba cika yawon Daren nan sukai ba ..

Kai tsaye sukai gun Innaji ,nan suka zauna suna hira .a nan ne Kamalu ya fadin wa kakar tasu cewa .."Shi ma ya samu wata matar .."

Kallon shi tayi tana fadin.."kai wannan da ,yo wannan zilamar duk ta miye haka?,ina diyar wajen Musa Kwantin kayi ya ya da ita shin?"

Kallon Juna sukai su biyun..se kamalu ya hau shafa fuska yana tunanin indai innaji ta tsaya mai to magana ta kare ,Amman tana nuna rashin amincewar ta zancen yasha ruwa ...

Nan take kuwa ta sallami wannan maganar hallau suka jawo wani paipan suka fara dashi...Wanda suke maganar kayan da Maina zeyi na auren Mairo ..

Ita dai innaji tace .."Kayi ta Addu'a "Da guda" Allah ze hore .

"Da guda" suna ne Wanda iyayen Maina da kakanin sa suke kiran shi da shi,sakamakon zaman shi da yayi "Da" daya jal a gun Ubanshi wato Malam Ubale ...

***********

Tafi tafi dai har watan Babbar sallah ya kama wannan ya nuna cewa saura wata biyu kan bikin Maina da Mairo..

A gefe guda kuma Kamalu ya matsa da maganar Hasi,cikin hikimar Allah se gashi Saude ta fara kula wani me dinkin takalmi me suna Yakubu,tunda dama ba'ai masu baiko ba .Hakan ne yasa Innaji tayi wa Ubale magana tun bayan da Kamalu ya same ta da maganar saude tayi sabon daurayi ,nan da nan ake je tambaya ,nan ma ba gardama Malam iro ya bayar,tunda su da Kansu suka je da batun ita ma Hasi zatayi karatun ta a dakin ta ..

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now