(29)

29 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Saturday, 17th October. 2020

(29)

***************

Maina na ta jin dadi,dan makocin shi Zakari mutum ne me mutumci.

A asibitin bayan sun yanki kati,suka hau bin wani dogon layin ganin likita.Maina da Zakari dai Yar Hira suke,mafi yawan hirar tasu ma akan rashin lafiya suke yin ta,kamar daga sama se ga Haidar,cikin shigar shi ta likitoci wadda ta bala'in kawata halittar shi da kamannin shi..

Kan ya karaso se Maina take gaya wa Zakari cewa,"wanchan mutumin ne ya buge nin fa"..

Kallon shi Zakari ya sake Yi,sannan yace wa Maina .."wannan fa likita ne"

Daga kai Maina yayi,sannan yace .."shine,ni kayana ma suka dameni ,kasan a motar shi na baro su.."

Daf da ze wuce se Zakari ya tashi tsaye ya Masa sallama,Amsawa Haidar yayi cikin girmama marasa lafiyan su,tunda yasan baya wuce hakan..

Gaisawa sukai,se Zakari yake cewa.."Dama Dan uwana na rako zega likita,se ya ganka yace wai ya manta kayan sana'ar sa a motar ka .."

Tabbas Haidar ya tuno da Haka,se sannan Kuma Maina ya taso Yana gaida Haidar din,tuni Haidar ya gane shi,yace .."Subhanallah,har yanzu be fara warkewa ba,gashi har ya kumbura ma.."

Tsaddaden Agogon hannun shi ya kalla,ganin cewa Yana da sauran time kafin su shiga tiyata,se yace dasu.."Ina karamin katin take?"

Mika Mai Maina yayi,dakin ganin likitan ya shiga,ba dadewa ya karbi file din Maina ya fito ya shiga wani office din,yace su biyo shi.

Ba bata lokaci ya hau duba Maina,nan ya fara zargin ko dutse ne a goshin,yasa yake ta kumburin,ciwon Kai Kuma da Maina yake Daman dole yadan ruga yin ciwon Kai.

Ya rubuta musu magani,Kuma take ya zaro kudi ya bayar yace su siya a Lamco ,suna fitowa suka tsaya suka siya,Daman yace da Maina ya same shi a asibitin sa bayan kwana biyu,a Nan ze ruga duba shi..

A gida Maina yayi kokarin Shan magungunan shi,tare da kiyaye sharuddan da Haidar ya kafa masa.

A kwana na biyun Maina ya nufi asibitin ,misalin Sha biyu na rana,sedai Yana doso gate din wata mota ta sake hankade shi,ko da Maina ya samu ya tashi be ko tsaya ba yayi gaba a hannun sa.sedai ji da yayi Dan yatsan shi na Masa wani itin azabar zugi.

Matukiyar motar Kuma mace ce,me suna Ummi,wato kanwar Haidar,wadda take aiki a banki,Kuma cikin sauri take Dan komawa wajen aikin ta, dalilin ta na zuwa asibitin Kuma Daman Dan Haidar ya sa tazo ta kawo Masa kayan ne tun jiya,Amman Bata zo ba,se a yau ta samu tazo,gashi tsautsayi yasa tayi ciki da wani..

Cikin sauri tayi ribas ta koma cikin asibitin ,a reception ta same shi Yana zaune,ya dafa Kai,kusa da shi taje tayi Mai sallama..

Yana dago kansa ,tayi arba da wani kyakkyawan bafillatanin matashi,baasar wa tayi tace .."Malam da fatan baka ji ciwo ba?"

Girgiza Kai kawai yayi.

Daman Yana shigowa ya fadi yadda Haidar ya sanar Masa ,tuni har an kai Masa iso,se wata nurse tazo,tana ganin Ummi ta sake gaisheta cikin girmamawa sannan tace wa Maina .."wai yace ka shigo office"

Bin ta Maina yayi,Ummi ma kuwa tabi bayan su ,a office din Maina ya zauna Yana gaida Haidar,cikin fara'a Haidar yake amsa Maina,tare da tambayar ba'asin lafiyar shi.shi dai Maina ya amsa da da sauki..

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now