(25)

28 1 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Sunday, 27thth September. 2020

(25)

*******************

Zeema fa yanzu Abu biyu take wa hako,ga Maina ga sirkar matar Maina..

Yau dai jira take Maina ya fice daga gidan.dan Kam yau da dubara da wayo zata karbe wannan sirkar,ko kuwa in Mairon ta zagaya bayi,ta shige dakin ta dauko ta ..

Toh da yake sirkar a gun Maina take zama tun bayan da suka gane cewa a garin Kano se kayi kaffa kaffa da kayan ka..

Kuma dai a ranar Maina ya tashi da ciwon Kai Wanda ya tilasta Masa zaman gida a ranar..

Koda Zeema taga Mairo na yunkurin daura tukunya,se tazo take ce Mata .."Yar fillo aiki ake ne,yau Ina me aikin naki yake?"

Shiru Mairon tayi bayan ta kalle ta ta gyada mata kai.ba tare da amsar inda Maina yake ba.

Zeema dai ta tabe baki sannan tace .."Niko Yar fillo ranar nan na ganki da wata yar wuya ,tai mun kyau,a ina kika siye ta,Kuma nawa kika siye ta?"

Maina da yake jin su tun farko se ya taso ya fito kofar dakin,kallo daya yawa Mairo,Wanda dole maganar da take niyyar Yi ta tsaya mata chak a baki.

Zeema da bataga sanda Maina ya kalli Mairon ba se wani kwarkwasa take yi Mai, wai ita yar bariki.

Be bi ta kan Zeema ba ya juya harshe yace da Mairo ta wuce ciki ,anan ya zauna yana karasa abunda bata karasa ba..

Bayan shigar Mairo ciki se take masa magana da yaren su take ce Masa.."ta sanya dandano a girkin kada ya dada.."

Ce Mata yayi .."ai na fiki iya girki dai yarinya.."

Nan ta fara Dariya a daki harda waka tana cewa ita ta fishi,shima dariyar yake yana ta girgiza Kai,wautar Mairo na burge shi a rayuwa ,in banda abun Mairo ma mene abun waka..hmm kawai yace ya juya ya shige cikin dakin su..

Zeema ma juya wa tayi tana jin haushin Mairo har ranta..

Ta Kuma dauri aniyar samun Maina ita ma,kyawun shi abun kallo ne,ga wani irin jiki da take da shi wanda ya same shi sanadiyar turin kura,Kuma da yake asalin kirar sa ma me kyau ce,hakan yasa ko da jikin ya tashi mummurdewa yabi lafiyayyen surar sa ta asali tayi mai kyau,ga tsaftar sa,Dan Duk da Yana bakauye be yadda da kazanta ba..

*****

A lokaci ake irin na sanyi a garin na Kano,Kuma a shekarar wani irin sanyi ne ake me ratsa jiki, dole Maina ya fita ya nufi kasuwa dan siyo musu mayafin sanyi..

Koda yaje kasuwar se yaje kwari ne,tunda Malam Ado yace mai Nan ce ta sutura,se da ya je Yana tambayar kayan sanyi ,se suka duba kalar shi suka kwatanta masa cewar yaje kasuwar Wambai.in yaje se ya tambayi gun masu kayan sanyi .

Dake me kan gado ne tuni yaje inda yake nema ya samo musu rigar sanyi da hula harda safa..

Maina baya wuce opportunity ,nan ya sari safar gwanjo da huluna ya nufo gida.

Mairo taga riga da safa da hula me kyau ta dauka tana ta tsalle abun ta.se yace mata ga safunan nan ya saro mata ta nuna wa Maman Nana ko zasu siya..

Hakan kuwa akayi,se gashi safuna da huluna suna ta tafiya ,kan sati biyu sun kare,se ake ta tambaya ,dole ta sanya ya sake komawa ya debo wasu .

Suma suka zo ana ta siyan su da yake masu arha ne,komai Naira 20 ya kara akan yadda ya siyo su. .

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now